Wane ne Khalid Mohammed, mutumin da 'ya tsara' hari mafi muni kan Amurka?

    • Marubuci, Lisa Lambert
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Mutumin da ake zargi da kitsa harin ranar 11 ga watan Satumban 2001 a Amurka, Khalid Sheikh Mohammed zai gurfana a gaban ƙuliya a watan Yunin 2028, fiye da shekara 25 bayan abin da gwamnatin Amurka ta kira ''harin ta'addanci mafi muni da aka kai cikin ƙasar a tarihi''.

Alƙalin kotun sojin ya yanke hukuncin cewa za a fara shari'ar ne nan da shekara biyu domin buƙatar masu gabatar da ƙara ta neman a fara shari'ar a 2027 ya yi kusa sosai.

Khalid Mohammed ya nemi a cimma yarjejeniyar da za ta bashi damar amsa laifin da ake zargin shi da aikatawa yayin da shi kuma za a bashi tabbacin samun hukuncin da ba zai haɗa da kisa ba, amma wata kotun ɗaukaka ƙara ta tarayya ta yi watsi da wannan buƙatar. A 2003 aka kama shi, yayin da aka tsare shi a sansanin Guantanamo Bay tun daga watan Satumban 2006.

A baya, Khalid Sheikh Mohammed ya taɓa amsa cewa shi ne ya kitsa harin ranar 11 ga watan Satumban 2001 tun daga farko har ƙarshe.

Alƙalin kotun sojin Amurkan, Laftanar-Kanar Michael A Schrama a hukuncin da ya yanke a ranar Laraba ya ce za a gurfanar da Mohammed da wasu mutane uku da ake zargi da hannu a harin, a ranar 5 ga watan Yiunin 2028.

Saauran mutanen da za a gurfanar tare da Mohammed sun haɗa da Walid bin Attash da Ali Abdul Aziz Ali da kuma Mustafa al-Hawsawi.

Ranar fara shari'ar za ta bayar da dama domin warware wasu batutuwan masu alaƙa da shaidun da za a gabatar.

A wata mai zuwa za a cika shekara 25 da faruwa harin, inda aka ƙwace wasu jiragen sama, aka kuma kai hare-hare da su kan cibiyar klasuwanci ta duniya da ke birniun New York da kuma hedikwatar tsaron Amurka ta Pentagon da ke Virginia, yayin da wani jirgin da aka ƙwace ya fado a Pennsylvania. Mutane aƙalla 3,000 aka kashe a hare-haren.

Ana zargin cewa Khalid Mohammed ne ya tsara da kuma horas da mutanen da suka tuƙa jiragen har suka kai hare-haren, bayan ƙwace jiragen, kuma ya gabatar da tsarin nasa ga Bin Laden, jagoran ƙungiyar al-Qaeda, wanda ya aiwatar da shi.

Khalid Mohammed, wanda ya yi karatun injiniya a Amurka, an kama shi ne tare da al-Hawsawi a Pakistan, a watan Maris ɗin 2003.

Bayan shafe shekara biyu ana tattaunawa, an yi watsi da tayin da ɓangaren wanda ake zargi ya gabatar na neman a ba shi damar amsa laifin amma da sharaɗin ba za a yanke mashi hukuncin kisa ba.

Wata shida bayan harin ne aka buɗe sansanin tsare masu laifi na Guantanamo Bay.

Har yanzu akwai fursunoni aƙalla 15 da ake tsare da su a sansanin.

Wane ne Khalid Mohammed?

Khalid Sheikh Mohammed shi ne mutumin da Amurka ke zargi da kitsa mummunan harin da aka kai wa Amurka a ranar 11 ga watan Satumban 2001, kuma ana masa kallon ɗaya daga cikin manyan jagororin ƙungiyar al-Qaeda a lokacin da Osama Bin Laden ke jagorantar ta.

Cibiyar tsaron Amurka ta Pentagon ta ce shi da kansa ya amsa cewa ya yi uwa da makarɓiya a kitsa harin "daga farko har ƙarshe".

An yi amannar cewa an haifi Mohammed ne ko dai a shekarar 1964 ko kuma 1965 a ƙasar Kuwait, said ai iyayensa ƴan asalin lardin Baluchistan ne na ƙasar Pakistan, yankin da ke iyaka da Afghanistan.

Yana ji da kuma Magana da harsunan Larabci, Ingilishi, Urdu da kuma Baluch.

Ya kammala karatunsa na digiri ne a shekarar 1986 a Jami'ar Aikin noma da Ƙere-ƙere ta Jihar Carolina da ke Amurka.

A ƙarshe-ƙarshen shekarun 1980 ya koma birnin Peshawar na ƙasar Pakistan da zama, inda a nan ne ya hadu da Osama Bin Laden.

Mohammed ya fara yin ƙaurin suna ne bayan bankaɗo wani shirin tarwatsa wani jirgin saman Amurka a shekarar 1995.

An daƙile yunƙurin ne bayan ƴansanda sun gano bayanai a wata kwamfuta sa'ilin da suke yin bincike game da zargin da ake yi kan cewa ana shirin kashe Fafaroma.

A shekarar 1999 ne Mohammed ya shawo kan Osama Bin Laden kan ya goyi bayan shirin kai hare-haren ranar 11 ga watan Satumba a Amurka.

Bayan harin, wanda ya kashe sama da mutum 3,000, Amurka ta ayyana ladar kudi kan duk wanda ya taimaka aka kama ko kashe shi.

Amurka ta yi amannar cewa Mohammed ne ya tsara komai sannan ya tura kuɗaden da aka biya waɗanda suka aiwatar da garkuwa da jiragen da kuma kai harin.

Kama Mohammed na daga cikin manyan nasarorin da aka samu a yaƙin da ƙasashen yamma ke yi da ƙungiyar al-Qaeda.

Wani masanin ayyukan ta'addanci a duniya da kuma ƙungiyar al-Qaeda, Rohan Gunaratna ya bayyana shi a matsayin "ƙwararre wajen kitsa hare-haren ta'addanci a ƙasashen duniya, kuma ɗaya ne daga cikin mutane ƙalilan da suka ƙware a wannan fanni".

Ba Amurka da Pakistan kaɗai ke neman shi ruwa a jallo ba, wata kotu a Farans ata bayar da sammacin kama shi bisa zargin sa da hannu a harin ƙunar baƙin wake da aka kai a wani wurin ibadar Yahudawa a tsibirin shaƙatawa na Djerba da ke Tunisia a shekarar 2002.

Haka nan ƙasar Australia ta yi ta son neman bayanai daga gare shi a binciken da ake yi kan harin bam da aka kai a Bali a shekarar 2002 wanda ya kashe mutum 202.