Premier League: Leicester City ta samu makinta uku

Asalin hoton, Getty Images
An wallafa
Jamie Vardy da Soyuncu ne suka taimaka wa Leicester City yayin da ta casa Cerystal Palace har gida da ci 0-2.
Jamie Vardy ya zira kwallonsa ta 10 ne a kakar bana ana saura minti biyu a tashi daga wasa bayan sun yi musayar fasin da Garay a cikin yadi na 18 din Palace.
Kafin haka, Caglar Soyuncu ne ya fara jefa kwallo a ragar Palace a minti na 57, inda ya saka wa kwallo kai daga wani bugun kwana da james Maddison ya bugo.
Wannan nasarar ta daga Leicester zuwa mataki na uku a teburi, inda ita kuma Crystal Palace ta gangaro zuwa mataki na tara.







