An soke tashin jiragen sama a Riyad Babban birnin Saudiyya
Kamfanin jiragen sama na Kuwait Airways ya sanar da soke tashin jiragensa biyu da za su sauka a Riyadh, babban birnin Saudiyya, “saboda rufe filin jirgin sama da kuma halin tsaro.”
Haka kuma, Etihad Airways ya soke jirage da dama tsakanin Abu Dhabi da Riyadh har zuwa ranar 12 ga Oktoba, saboda rufe filin jirgin sama na King Khalid da ke Riyadh.
Kamfanin Air India ma ya tsawaita dakatar da zirga-zirgarsa zuwa Riyadh har zuwa ranar 15 ga Oktoba.
A irin wannan mataki, kamfanonin Flydubai, Turkish Airways, Lufthansa, da Pakistan International Airlines su ma sun dakatar da jiragensu zuwa Riyadh na ‘yan kwanaki masu zuwa.
A halin da ake ciki, Hukumar kula da harkopkin jiragen sama ta Nahiyar Turai ta faɗaɗa shawarwarinta game da sararin samaniyar Saudiyya, tana mai nuni da “ikon mayakan Houthi na kai hare-hare zuwa wurare masu nisa a cikin Saudiyya da kuma mayar da hankali ga kayayyakin more rayuwa na harkar sufurin jiragen sama na ƙasar.”
Kasashen Jamus da Canada, da Sifaniya su ma sun gargadi ‘yan ƙasarsu da su guji tafiya zuwa Riyadh, musamman zuwa King Khalid Airport.
Ya zuwa lokacin rubuta wannan rahoto, shafin Flight Radar, wanda ke sa ido kan zirga-zirgar jiragen sama a yankin, ya ruwaito cewa an soke jirage 297.






























