Maiduguri: An kai harin kunar bakin wake

An wallafa

Rahotanni daga jihar Borno dake arewacin Najeriya sun ce wasu 'yan kurnar bakin wake da ake zargin 'yan Boko haram ne, sun kai hari a kauyen Mule dake wajen garin Maiduguri.

Lamarin dai ya auku ne a wurin binciken ababan hawa na jami'an tsaro.

Wasu mazauna garin sun ce, an samu asarar rayuka.

Kungiyar Boko Haram dai tana ci gaba da kai hare-hare a jihar Borno.

Koda cikin wannan makon kungiyar kare hakkin dan adam Amnesty ta ce, nuna takaici akan kisan da ake yi a rikicin na Boko Haram.