KAI TSAYE, Yaƙin Iran da abubuwan da ke faruwa a sassan duniya
Wannan shafi na kawo muku abubuwan da ke faruwa a yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi da Iran da kuma sauran muhimman labarai a sassan duniya na 16/04/2026.
Firaministan Lebanon ya yi maraba da sanarwar tsagaita wuta
Asalin hoton, EPA
Firaministan Lebanon Nawaf Salam ya ce yana maraba da yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta na wucin gadi da Isra'ila, wadda ya ce dama abin da Lebanon ke buƙata tun bayan ɓarkewar yaƙin.
Ya ce yana fatan yarjejeniyar za ta baiwa waɗanda rikicin ya shafa damar komawa gidajensu.
Salam ya kuma yaba da ƙoƙarin ƙasashen duniya na cimma yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta.
Trump ya gayyaci Netanyahu da shugaban Lebanon Fadar White House
Asalin hoton, EPA
Shugaban Amurka Trump ya ce ya gayyaci firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da shugaban Lebanon Joseph Aoun zuwa fadar White House domin ci gaba da tattaunawa.
Hakan na zuwa ne bayan da Trump ya sanar da tsagaita buɗe wuta na kwanaki 10 tsakanin kasashen biyu, inda ya ce za ta fara aiki da karfe 5 na yamma agogon ƙasar.
"Dukan ɓangarorin biyu suna son ganin an samu zaman lafiya, kuma na yi imanin hakan zai faru, da sauri!" Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Truth Social
Sai dai ba a bayyana ko sun amsa gayyatar ba.
Shugaban Lebanon ya gode wa Trump bisa 'ƙoƙarin' ganin an tsagaita wuta
Asalin hoton, Reuters
Ofishin shugaban ƙasar Lebanon Joseph Aoun ya tabbatar da cewa ya tattauna ta wayar tarho da shugaban Amurka Donald Trump a yau Alhamis.
A cikin wani saƙo da aka wallafa a shafin X, ofishin ya ce Aoun ya gode wa Trump saboda ƙoƙarin da ya yi na cimma yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta a Lebanon da kuma "wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali".
Aoun ya jaddada cewa yana son ganin an tsagaita buɗe wuta tsakanin Isra'ila da Hezbollah "nan kusa".
Bayanin ya ƙara da cewa Trump zai ba shugaba Aoun da Lebanon goyon bayan da ya dace
Firaministan Pakistan ya isa Doha domin ci gaba da ziyarar diflomasiyya kan yaƙin Iran
Asalin hoton, EPA/Shutterstock
Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif, wanda ke taka rawa a matsayin mai shiga tsakani a tattaunawar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran, ya isa Doha a ranar Alhamis bayan ziyararsa Saudiyya, inda ya gana da Sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani.
Fadar Firaministan Pakistan ta ce Sarkin Qatar ya yaba da rawar da Pakistan ke takawa, inda suka nuna goyon baya ga ƙoƙarin rage tashin hankali da ƙarfafa haɗin kai na ƙasa da ƙasa domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a yankin, musamman wajen tabbatar da hanyoyin samar da makamashi ba tare da tangarda ba.
Ziyarar Sharif zuwa Saudiyya da Qatar ta zo ne kwanaki huɗu bayan tattaunawa tsakanin manyan jami’an Amurka da Iran a Islamabad.
Ana sa ran Sharif zai wuce Turkiyya a gaba.
Tattaunawar da aka yi a Pakistan ba ta kai ga cimma yarjejeniya ta dindindin ba don kawo ƙarshen yaƙin Gabas ta Tsakiya, duk da cewa an samu tsagaita wuta na kusan kwanaki goma tsakanin Iran, Amurka da Isra’ila.
Trump ya ce Isra'ila da Lebanon sun amince da tsagaita buɗe wuta na kwanaki 10
Asalin hoton, Reuters
Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa Lebanon da Isra'ila sun amince da tsagaita wuta na kwanaki 10 da zai fara aiki da karfe 5:00 agogon ƙasar.
A cikin wani sakon da ya wallafa na bayyana yarjejeniyar tsagaita bude wuta, Trump ya ce ya tattauna da shugaban Lebanon Joseph Aoun da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.
Sai dai babu dai wani ƙarin bayani a cikin bayanin nasa game da ƙungiyar Hizbullah da ke samun goyon bayan Iran a Labanon, wadda Isra'ila ke ta musayar wuta da ita.
Trump ya ce: “Na tattauna da Shugaban Kasar Lebanon Joseph Aoun cikin girmamawa, da Firaminista Bibi Netanyahu na Isra’ila.
“Shugabannin biyu sun amince cewa domin a samu zaman lafiya a tsakanin kasashensu, za su fara tsagaita wuta na kwanaki 10 a hukumance da karfe 5 na yamma," in ji Trump.
Kotu ta ba EFCC izinin kama tsohuwar ministar jin ƙan Najeriya Sadiya Faruoq
Asalin hoton, Sadiya Umar Farouq/FB
Kotu a birnin tarayyar Najeriya Abuja, ta ba hukumar yaƙi da masu yi tattalin arzikin ƙasar ta'annuti EFCC, izinin kama tsohuwar ministar jin ƙai ta ƙasar Sadiya Umar Faruoq.
EFCC na binciken tsohuwar ministar ne da badaƙalar dala miliyan $1.3m da kuma Naira miliyan N746.6m na ma'aikatar da ake zargin an wawure.
A wani saƙo da EFCC ta wallafa a shafinta na X, ta ce mai shari'a Jude Onwuegbuzie, ya kuma ba da izinin kama sakataren ma'aikatar Bashir Nura Alkali.
Ta ce matakin ya biyo bayan ƙin bayyana a gaban kotu da waɗanda ake zargin suka yi a ranar Alhamis.
Lauyan waɗanda ake ƙarar sun buƙaci a ba su uzuri sakamakon rashin lafiya da hana Sadiya halartar kotun, amma kuma ba a amince da buƙatar tasu ba.
EFCC ta ce ta shigar da ƙarar ce tun a ranar 15 ga watan Disambar 2025, amma ba a samu damar yin ido biyu da waɗanda ake zargin domin miƙa musu takaradar kotun ba.
Sadiya ta riƙe muƙamin ministar ne a mulkin marigayi tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, inda daga baya ta auri tsohon babban hafsan sojin saman Najeriya AVM Sadiq Abubakar.
Isra'ila ta kai munanan hare-hare a kudancin Lebanon
An saki wasu sabbin hotuna da ke nuna yadda Isra'ila ta kai munanan hare-hare a kudancin Lebanon.
Hotunan farko guda biyu da aka ɗauka sun nuna bayan wani hari da aka kai a birnin Nabatieh, wani birni mai mutane kusan 40,000 a arewacin kogin Litani, kuma ya nuna hayaki na tashi sama.
Hoto na uku ya nuna yadda mutane a Qasimieh da ke kusa da gaɓar tekun Mediterrenean na duba irin ɓarnar da harin ya haifar, wanda wani babban jami'in tsaron kasar ya ce ya lalata gadar ƙarshe da ta haɗa kudancin Lebanon da sauran sassan ƙasar.
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Reuters
Tsagaita wuta a Lebanon na da muhimmanci kamar na ƙasarmu - Iran
Shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Baqer Qalibaf, ya jaddada cewa a wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Lebanon, Nabih Berri tsagaita wuta a Lebanon na da muhimmanci iri ɗaya da na Iran.
Qalibaf, wanda ya jagoranci tawagar Iran a tattaunawar kai tsaye da Amurka a Islamabad, ya ce Iran na ƙoƙarin ganin an tilasta wa ɓangarorin da ke rikici su amince da tsagaita wuta na dindindin.
Ya kuma ce Iran ba ta manta da ‘yan uwanta na Lebanon ba, kuma tana sa ido a kai a kai kan halin da ake ciki a ƙasar da kuma ƙoƙarin samar da tsagaita wuta, wanda ya ce yana da matuƙar muhimmanci a gare su.
Nabih Berri, wanda ake ganin na kusa da ƙungiyar Hezbollah ne, ya yaba da ƙoƙarin Iran, yana mai cewa bai ga wata hulɗa kai tsaye da Isra’ila a matsayin abin da ya dace da muradun al’ummar Lebanon ba.
Isra'ila ta yi barazanar kai wa Iran hare-hare masu zafi
Asalin hoton, Reuters
Ministan tsaron Isra'ila, Isra'ila Katz, ya yi gargaɗin cewa kasarsa za ta ƙaddamar da hare-hare masu zafi a kan Iran matuƙar ba ta amince da yarjejeniya da Amurka ba.
"Iran na tsaka mai wuya. Wannan ne lokacin da ya kamata su ɗauki matsaya - tsakanin makomarsu ko kuma keɓewa cikin halaka," in ji shi.
Ya ce idan Iran ba ta yi abin da ya kamata ba, Isra'ila za ta ƙaddamar da munanan hare-hare a inda ta yi niyya tun da farko fiye da waɗanda suka gani a baya.
Ya ƙara da cewa: "Zaɓi ya rage nasu, kuma su za su ji a jikinsu."
Abubuwan da taron manema labaran sojojin Amurka kan yaƙin Iran ya ƙunsa
Asalin hoton, Getty Images
Sakataren tsaron Amurka, Pete Hegseth, tare da shugaban hafsoshin soji Janar Dan Keene da kwamandan CENTCOM, Admiral Brad Cooper, sun yi taron manema labarai a Pentagon kan yaƙin Iran.
Ba a bayyana sabbin muhimman bayanai ba, amma sun mayar da hankali kan gargadi da nuna shirye-shiryen soja. amma ga wasu abubuwa da suka tattauna a taron
Hegseth ya ce Iran na da “ƙwarin gwiwa mai yawa” na amincewa da tsagaita wuta
Rundunar CENTCOM ta ce sojojin Amurka na sabunta dabarunsu da hanyoyin aikinsu
Hegseth ya sake kira ga gwamnatin Iran da ta zaɓi hanya ta gaba cikin hikima
Janar Keene ya ce duk wani jirgi da ya yi ƙoƙarin kauce wa toshewar mashigar Hormuz da aka yi, za a ɗauki mataki a kansa yadda ya dace
Janar Keene ya kuma ce Amurka a shirye take ta koma yaƙi a kowane lokaci
Hegseth ya kara da cewa kasa da kashi 10 cikin 100 na ƙarfin rundunar ruwan Amurka aka yi amfani da shi wajen toshe mashigar Hormuz
Hegseth ya ce Iran ba za ta iya maye gurbin ƙarfin sojinta da ta rasa ba
Fafaroma Leo ya soki "azzaluman" da ke kashe biliyoyin kuɗi a yaƙe-yaƙe
Asalin hoton, Getty Images
Fafaroma Leo ya soki shugabannin da suke kashe biliyoyin kuɗi a yaƙe-yaƙe a wani kalami na rashin tsoro a Kamaru. Wannan dai na zuwa ne bayan da shugaban Amurka, Donald Trump ya yi masa kakkausan suka a karo na biyu a shafinsa na soshiyal midiya.
Da yake magana a Bamenda Kamaru, Fafaroman na farko ɗan Amurka ya yi alawadai da "masu amfani da addinin da sunan ubangiji a harkokin soji da tattalin arziƙi da kuma neman cin nasara a siyasa," inda ya yi gargaɗin amfani da addini wajen samun hujjar haifar da rikici.
"...duniya na fama da wasu tsirarun azzalumai,"
Fafaroma Leo ya kuma bayyana irin kuɗaɗen da ake kashewa a fannin yaƙi inda ya soki abin da ya bayyana da rashin daidaito a duniya a fannin abin da ya dace.
Ƴan daba sun addabi jihar Diffa a jamhuriyar Nijar
Asalin hoton, Getty Images
A jihar Diffa a jamhuriyar Nijar, al'ummomi na kokawa kan yawaitar ayyukan faɗan daba da ƙwacen waya ta hanyar amfani da miyagun makamai.
Hukumomi sun ɗora laifukan a kan mutanen da suka bayyana da baƙi duk da dai wasu ƴan ƙasar su ma na da hannu a cikin miyagun lafiukan.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ƙungiyoyin da ke ɗauke da makamai da suka haɗa da Boko Haram da sauransu ke zafafa hare-hare da ke haddasa salwantar rayukan jami’an tsaro da na fararen hula.
China ta ce tattalin arziƙinta ya samu bunƙasa a 2026
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Firaiministan China, Xi Jiangping
Alkaluman hukuma daga China na nun acewa tattalin arzikin ƙasar ya karu a shekara da kashi biyar cikin ɗari a rubu'in farko na wannan shekara.
Fitar da kaya waje da ƙirar kayayyaki na fasaha da kuma tallafin gwamnati ne suka janyo hakan.
To amma kuma burunƙasar cinikin ɗaiɗaikuwa na jama, ba ta kasance ba yadda aka yi tsammani.
Ana sa ran tattalin arziƙin na China zai gamu da dan tazgaro a sakamakon tsadar farashin makamashi da yaƙin Gabas ta Tsakiya ya haddasa
Burkina Faso ta haramta wa kungiyoyi fararen hula fiye da 100 aiki a ƙasar
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Shugaban Burkina Faso, Ibrahim Traore
Gwamnatin soji ta Burkina Faso ta rushe kungiyoyin sa-kai fiye da guda 100 waɗanda da dama daga cikin su ke da alaƙa da fafutukar neman ƴancin dan adam.
Ana dai yi wa al'amarin kallon wani yunƙuri na daƙile ƴancin al'umma a ƙasar.
Ma'aikatar kula da iyakokin ƙasar wadda ta sanar da matakin ta ce an rufe ƙungiyoyin ne sakamakon gazawarsu wajen bin dokokin ƙungiya da ƙasar ta tsara, inda aiwatar da hanin nan take ga duk wata ƙungiya a ko'ina afaɗin ƙasar.
Gwamnatin ta kuma ta ce hakan zai ba wa kasar damar daƙile safarar haramtattun kuɗi da tallafawa ƴan ta'adda da kuɗade.
Ƙungiyar ɗaliban FGC Kano sun koka kan ƙoƙarin mamaye filayen makaranta
Ƙungiyar tsofaffin ɗaliban kwalejin tarayya da ke Kano ta yi kakkausar suka kan abin da ta kira haramtaccen cin iyakar fili mallakar kwalejin tarayya da ke Kano.
Al'amarin dai ya janyo damuwa a tsakanin tsaffin ɗaliban game da tsaron kadarorin ilimi na ƙasa.
Kungiyar ta bayyana cewa ta ɗauki matakai cikin gaggawa domin shawo kan lamarin, ciki har da matakan shari’a, amma a cewarsu ana ci gaba da aikin yanka filayen da gine-gine.
Ukraine ta ce harin Rasha ya kashe mata mutum 12
Asalin hoton, Getty Images
Hukumomi a Ukraine sun ce wasu hare-haren makamai masu linzami da Rasha ta kai cikin dare a yankun da dama na ƙasar sun kashe aƙalla mutum 12.
Mutum shida sun mutu a yankin tashar jirgin ruwa ta Odesa da ke kudanci kamar yadda hukumomin soji na birnin suka ce.
Mutum huɗu sun rasu a hare-haren makamai masu linzami a babban birnin ƙasar Kyiv, ciki har da yaro mai shekara 12. An kuma kashe uku a Dnipro da ke tsakiyar Ukraine ɗin.
Su ma dai dakarun Ukraine na kai hari Rasha, inda Gwamnan yankin Krasnodar da ke kudancin Rasha ya ce hare-haren jiragen sama marassa matuka na Ukraine sun kashe yara biyu, 'yan shekara 5 da kuma 14, da lalata harkokin kasuwanci a kusa da tashar jirgin ruwa ta Tuapse da ke Bahar Aswad.
Gagarumar gobara ta tashi a matatar mai a Australia
Masu aikin agajin gaggawa a Australia sun ce an yi nasarar kashe wata gagarumar gobara da ta tashi a daya daga cikin matutun man ƙasar biyu.
Gobarar ta tashi ne a matatar Geelong da ke jihar Victoria, inda fashewa ta rika cilla wuta sama har tsawon sama da kafa 190.
Yanzu abin da ake ƙoƙarin sani shi ne irin illar da gobarar ta yi da kuma yadda tasirinta zai kasance wajen samar da mai a Australia.
Tuni dai farashin ya yi tashin gwauron zabi saboda yaƙin Gabas ta Tsakiya.
Matatar man ƙasar na samar da wajen kashi 10 cikin dari na man da ƙasar ta Australia ke buƙata, duk da cewa an kashe wutar, lamarin zai iya shafar yawan fetur ɗin da ake samarwa.
Har yanzu matatar na ƙwarya-ƙwaryar aiki, inda za a ci gaba da samar da man gas da dizil da man jirgin sama - cikin takatsantsan. An samu dukkanin ma'aikatan matatar.
Yaƙin Iran zai shafi yara 40,000 - Save The Children
Asalin hoton, Getty Images
Wani sabon bincike da ƙungiyar agaji ta duniya ta Save the Children ta fitar, ya nuna cewa a duk ƙarin dala biyar a kan kowace gangar ɗanyen mai, na iya raba kusan yara 40,000 da samun tallafin abinci da magunguna don kare rayukansu.
Rahoton ya fito ne a dai-dai lokacin da rikicin Gabas ta Tsakiya ke ƙara haddasa tashin farashin man fetur a duniya.
Wannan matsi na zuwa ne duk da yarjejeniyar tsagaita wuta a tsakanin Amurka da Iran.
Hakan dai na nuna yadda rayuwar ƙananan yara ta dogara kacokan kan yanayin farashin makamashi na Duniya.
An yanke wa Malema hukuncin zaman gidan kaso na shekaru biyar
Asalin hoton, Getty Images
An yanke wa fitaccen ɗan siyasar nan na ƙasar Afirka ta Kudu, Julius Malema mai shekaru 45 ɗaurin shekara biyar a gidan yari.
Twanet Olivier wadda ta yanke hukuncin a wata kotun Majistare ta samu Malema da laifin mallakar harsasai da harba bindiga ba bisa ƙa'ida ba a wurin taruwar jama'a da jefa rayuwar mutane haɗari.
Malema wanda ya saka baƙaƙen kaya da jan lakatai sannan yana tsaye yana kallo a lokacin da alƙaliyar ta yanke masa hukunci.
Tawagar lauyoyin Malema sun fara shirin neman ɗaukaka ƙara.
Ana fargabar ƴan'ta'adda na shirin kai hare-hare a Abuja - AFP
Asalin hoton, Getty Images
Jami'an tsaron Najeriya na cikin shirin ko-ta-kwana sakamakon bayanan sirri da ke nuna cewa ƙungiyoyin ƴan'adda na shirin kaihare-hare kan gine-gine gwamnati a Abuja, babban birnin Najeriya da jihar Neja mai maƙwabtaka.
Wata wasikar sirri ta cikin gida a hukumar hana fasa ƙwauri ta Najeriya da kamfanin dillancin labarai na AFP ya samu, ta nuna cewa ƴan bindigar na shirin kai wa filin jirgin sama na Abuja da gidan yari da cibiyar tsare mutane ta sojoji duka a Abuja.
Bayanin na sirri ya yi kama da harin da ƴan bindiga suka kai wa sansanin sojin sama a birnin Niamey na jamhuriyar Nijar abin da ya janyo fargabar yiwuwar hare-haren bai ɗaya a yankin.