Wane ciniki ne zai faɗa cikin waɗannan?

Asalin hoton, Getty Images
Duk da cewa tun ranar 15 ga watan Yuni aka buɗe kasuwar musayar ƴanwasa amma har yanzu wasu ƙungiyoyin Premier na nan suna faɗi-tashin ganin sun kammala cinikin ƴanwasa kafin lokacin da kasuwa za ta rufe, ƙarfe 12 na daren ranar Talata.
Kama daga Julian Alvarez zuwa Enzo Fernandez, Cody Gakpo da Ismaila Sarr, ana sa ran wataƙila a ji wani babban labari.
To amma dole ne fa sai an hanzarta kafin kulle ƙofar kasuwa.
Julian Alvarez zuwa Barca ko Arsenal
Da alama tafiyar Julian Alvarez zuwa Arsenal za ta iya zama labarin da aka fi kasa kunne ana jira yayin da har yanzu babu tabbas kan makomar ɗanwasan gaban na Atletico Madrid.
Ɗanwasan mai shekara 26 na tsakiyar dabarwar zaɓi biyu: ko dai ya bi zuciyarsa zuwa Barcelona, inda ƙungiyarsa ta ce atafau, ko kuma abu mafi sauƙi shi ne tafiya Arsenal.
Arsenal ta daɗe tana sha’awar ɗaukar Alvarez kuma ƙungiyar na bibiya sau da ƙafa halin da yake ciki a Atletico, inda ƙungiyarsa ke neman kuɗin da bai gaza fam miliyan 128 ba.
Enzo zuwa Manchester City
Enzo bai buga wasan da Chelsea ta yi nasara ba a ƙarshen mako kan Brighton, kuma makomarsa a ƙungiyar na ci gaba da rawa ganin cewa ana alaƙanta shi da wani ciniki mai tsoka zuwa Manchester City.
Koci Enzo Maresca ya yi aiki da Enzo a lokacin da yake horas da Chelsea, yanzu kuma yana neman yadda zai ƙara ƙarfin ƙungiyarsa bayan tafiyar Rodri, Bernando Silva, Nico Gonzalez da kuma Tijjani Reinders.
Gakpo zuwa City ko Spurs
Mancester City ta fara tattaunawa da Liverpool kan sayen ɗanwasan gaba na Liverpool Cody Gakpo, kuma da alama ɗan asalin ƙasar ta Netherlands na son tafiya.
Kuma akwai yiwuwar Liverpool ta ƙyale shi ya tafi bayan sayen ɗanwasa Bradley Barcola.
Haka nan Tottenham ma na neman ɗanwasan sai dai rahotanni sun ce City ta miƙa tayin kuɗin da ya kai fam miliyan 85, kuma ana tunanin cewa Gakpo zai fi son tafiya Cityn.





