Hungary ta kori jami'an diflomasiyyar Rasha 10 yayin da dangantaka ke ƙara yin tsami

Asalin hoton, Getty Images
Ministar harkokin wajen Hungary, Anita Orbán, ta bayyana cewa an umurci jami'an diflomasiyyar Rasha guda 10 su bar Budapest saboda abin da aka bayyana a matsayin 'shiga cikin ayyukan da ba za a amince da su ba.'
'Wannan mataki yana tabbatar da tsaro da ƴancin ƙasar Hungary," in ji ta a shafukan sada zumunta, ba tare da bayar da cikakkun bayanai ba.
Tsawon shekaru, ana kallon Hungary a matsayin babbar ƙawar Rasha a Tarayyar Turai a lokacin mulkin Viktor Orbán, amma tun bayan da ya sha kaye a zaɓen watan Afrilu, sabuwar gwamnatin ta sauya akalarta daga goyon bayan Kremlin da ya saba yi a baya.
Firaministan Hungary, Péter Magyar, ya yi alƙawarin ƙulla dangantaka mai amfani da kuma dacewa da yanayi (mai ma'ana ta zahiri) tare da Moscow tun lokacin da aka zaɓi jam'iyyarsa ta Tisza a watan Afrilu.
Shi da ministan harkokin wajen ƙasar sun yi kira ga Rasha da ta kawo ƙarshen yaƙin da ake yi a Ukraine.
A watan Mayu, Anita Orbán ta kira jakadan Rasha domin nuna rashin amincewa da wani babban harin jiragen sama marasa matuƙa da aka kai yankin Transcarpathia na Ukraine, yankin da ke da yawan al'ummar tsirarun ƴan asalin Hungary.





































