Tawagar wakilan Amurka ta nufi Pakistan don tattaunawa da Iran
Rahoto kai-tsaye
Daga Abdullahi Bello Diginza
Gobara ta kashe mutum 20 a Indiya
Ƴansandan a jihar Tamil Nadu da ke kudancin Indiya sun ce wata mummunar gobara - da ta tashi a wani kamfanin ƙera abubuwan tartsatsin wuta da ake amfani da su a wuraren bukukuwa- ta kashe aƙalla mutum 20.
Bayanai sun ce gobarar ta raunata mutum shida.
Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ce an riƙa jin ƙarar abubuwan fashewa daga tazara mai nisa.
Kawo yanzu ba a san abin da ya haddasa gobarar ba.
Gobarar masana'antu ba sabon abu ba ne a Indiya, wanda ake alaƙantawa da rashin bin dokokin kariya ko rashin amfani da su.
An gano wani bom da aka dasa tun yaƙin duniya na biyu a Faransa
Kimanin jami'an ƴansanda 800 ne suka killace wani wuri a arewa maso yammacin birnin Paris yayin da ƙwararru ke ƙoƙarin kunce wani bom da aka gano an dasa shi a wurin tun lokacin yaƙin duniya na biyu.
Dubban mazauna yankin aka kwashe daga wurin daga tazarar mita 450.
An gano bom ɗin ne a yankin Colombes kwana tara da suka gabata, amma ƙwararru suka kasa cire shi a yunƙurinsu na farko saboda makunnarsa ta lalace.
Shirin da ake yi yanzu shi ne tayar da shi a zurfin mita biyu.
Labarai da dumi-dumi, Tawagar wakilan Amurka ta nufi Pakistan don tattaunawa da Iran
Asalin hoton, EPA
Mun samu sabbin bayanai daga Shugaban Amurka, Donald Trump game da batun tattaunawar tsagaita wuta da Iran.
"Wakilaina za su tafi birnin Islamabad na Pakistan - Za su isa can gobe da maraice, domin tattauanawa'', kamar yadda ya rubuta a shafinsa na sada zumunta.
''Muna son cimma yarjejeniya mai kyau kuma mai inganci, kuma ina fata Iran za ta amince da hakan, domin idan ba ta amince ba, Amurka za ta kai hari kan kowace cibiyar lantarkin da duka gadojin Iran,'' kamar yadda ya wallafa.
Ya yi gargaɗin cewa ''babu wata lallaɓa da za a yi mana'', idan aka gaza cimma matsaya.
Shugaban na Amurka ya ce zai ruguza duka gadoji da tasoshin lantarki cikin ''hanzari, kuma cikin sauƙi''.
Mun duƙufa wajen ƙera makamai cikin hanzari a lokacin tagaita wuta- Iran
Asalin hoton, EPA
Kamfanonin dillancin labaran Iran masu alaƙa rundunonin soji da hukumomin tsaron ƙasar sun wallafa wani bidiyo da ke nuna yadda ake ci gaba da ƙera makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa a ƙasar da abubuwan harba makaman.
A cikin bidiyon an ga kwamadan IRGC mai kula da dakarun saman ƙasar, Majid Mousavi na ziyartar ɗaya daga cikin cibiyoyin - wanda ke ƙarƙashin ƙasa.
Baya ga bidiyon kamfanonin labaran sun kuma wallafa wani saƙo daga Majid Mousavi da ke cewa ''saɓanin Iran maƙiya ba su iya sake ƙera makamai a lokacin tsagaita wuta''
''A lokacin tsagaita wuta yawan ƙera makamanmu masu linzami da jirage marasa matuƙa ya ma fi sauri a kan yadda muke ƙerawa kafin fara yaƙin. Mun sani maƙiya ba za su iya ƙera wa kansu makamai ba...''.
''Sun yi asarar wannan lokaci, sun kuma yi rashin nasara a yaƙin, sun gaza a Hormuz, sun gaza a Lebanon sannan kuma a duka yankin ma gaba ɗaya'', in ji shi.
'Islamabad na shirin karɓar baƙuncin tattaunawar Amurka da Iran karo na biyu'
Asalin hoton, Reuters
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayar da rahoton tsaurara matakan tsaro a Islamabad, babban birnin Pakistan.
Yayin da jami'an Amurka da na Iran ke shirin ci gaba da tattauna batutuwan da suka sha bamban don kawo ƙarshen yaƙin Iran.
Kawo yanzu dai ba a bayyana wuri da lokacin da za a gudanarwa da tattaunawar ba.
Mashigar Hormuz - wadda ke cikin batutuwan da ɓangarorin biyu suka yi saɓani - ta kasance a rufe, saboda ci gaba da datse tasoshin ruwan Iran da Amurka ke yi.
Iran ta ce jiragen ruwa za su wuce ta mashigar ne kawai bisa amincewar dakarun IRGC.
Duka ɓangarorin biyu dai sun ɗauki tsauraran matsayi game da batun.
Shugaba Trump ya jaddada cewa Amurka za ta bari jiragen Iran su shiga ko fita daga tasoshin ruwanta ne kawai idan aka cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin, yayin da Iran ta zargi Amurka da rashin mutunta yarjejeniyar wucin gadi da aka cimma.
Fafaroma Leo ya gudanar da ibada tare da dubban mabiya a Angola
Asalin hoton, Getty Images
Fafaroma Leo na gudanar da taron Ibada tare da dubban Kiristoci da suka taru a wani wuri a Kilamba da ke wajen Luanda, babban birnin Angola.
Masu ibadar - waɗanda ke sanye da farar riga da hula mai launin ruwan ɗorawa, manne da hotonsa - sun cika wurin ibadar.
Jagoran ɗariƙar Katolikan zai kuma ziyarci Muxima, wani babban wurin ziyarar ibada a ƙasar da ke kudancin Afirka.
A ranar Asabar ne Fafaroman ya ziyarci ƙasar - a wata ziyara da yake yi a ƙasashen Afirka huɗu - inda ya gana da shugaban ƙasar.
Fafaroman ya buƙaci shugabannin siyasa kada su ji tsoron bayyana aƙidar addininsu, yana mai cewa Angola za ta ci gaba idan ta yi amfani da hanyoyi daban-daban na dukiyar da Ubangiji ya huwace mata.
Alamu sun nuna cewa babu jirgin da ya wuce ta mashigar Hormuz
Asalin hoton, MarineTraffic
Yayin da Iran ta sanar da sake rufe mashigar Hormuz, a matsayin martani ga matakin Amurka na ci gaba da rufe tasoshin ruwanta.
Shafin da ke bibiyar ziraga-zirgar jiragen ruwa na Marine Traffic ya nuna cewa babu jirgin da ya tsallaka mashigar, duk da cewa akwai jiragen da dama a gaɓar mashigar, musamman gaɓar tekun Oman da na UAE.
Shafin kula da sufurin jiragen ya nuna cewa jirage da dama ne suka matsa kusa a mashigar a jiya, to amma suka dakata bayan da Iran ta sanar da sake rufe ta.
Jiragen ruwa da dama ne ciki har da na dakon kaya aka bayar da rahoton dakarun Iran sun kai musu hari a ranar Asabar.
'Tump na amfani da yaƙin Iran don karkatar da hankalin jama’a daga bankaɗar Epstein'
Asalin hoton, Getty Images
Tsohuwar mataimakiyar shugaban Amurka, Kamala Harris, ta ce Shugaban Amurka, Donald Tump na amfani da yaƙin Iran ne domin karkatar da hankalin jama’a daga sakin bayanan bankadar mashahurin mai lalata da ƙananan yaran nan Jeffrey Epstein.
Yayin da take jawabi a wani taron mata na jam'iyyar Democrat a jihar Michigan, tsohuwar ƴan takarar shugaban Amurka a jam'iyyar Democrats ɗin ta ce firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ne ya yi wa shugaba Trump ingiza mai kantu ruwa wajen sanya shi shiga yaƙin.
Sai dai ba ta bayar da hujjar iƙirarin nata ba, amma ta ce Amurkawa ba sa son yaƙin.
Kawo yanzu dai babu wani martani daga Shugaba Trump kai-tsaye ga zarge-zargen na Mrs Harris, amma ya ce Isra'ila ''babbar ƙawa'' ce a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.
"Ko mutane su so Isra'ila ko su ƙi ta, ta tabbatar da cewa ita babbar ƙawa ce ga Amurka. Suna da ƙwazo da ƙarfi da biyayya da kuma fikira, kuma ba kamar saura ba, da suka nuna mana halinsu na ainihi a lokacin yaƙi da na matsi, Isra'ila na yaƙi da himma, kuma sun san yadda za su yi nasara!"
A makon da ya gabata ne Mrs Harris ta ce tana nazarin yiwuwar sake tsayawa takara, bayan da ta sha kaye a yunƙurin da ta yi a baya a hannun Mista Trump.
Iran ta yi gargaɗin taƙaita zirga-zirga a Hormuz
Asalin hoton, ...
Shugaban Majalisar Dokokin Iran, Mohammad Baqer Qalibaf, ya ce dakarun Iran ne ke da cikakken iko da mashigar Hormuz.
Mista Qalibaf ya yi gargaɗin ci gaba da takaita zirga-zirgar jiragen ruwa ta mashigar matsawar Amurka ba ta janye shingen da ta yi wa jiragen ruwan Iran ba.
A baya-bayan rundunar sojin Iran ɗin ta riƙa mayar da jiragen da suka yu yunƙurin wucewa ta mashigar.
Shugaba Donald Trump ya ce Amurka za ta ci gaba da hana jiragen ruwa zuwa ko fitowa daga Iran har sai an cimma yarjejeniya da Tehran.
Assalamu alaikum
Masu bibiyarmu barkanmu da hutun ƙarshen ako.
Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci, domin kawo muku irin wainar da ake toyawa.
Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.