Real Madrid na son ta dawo da Mourinho, Onyeka zai koma Conventry a matsayin dan wasa na dindindin

Asalin hoton, Getty Images
Bayern Munich na zawarcin dan wasan Aston Villa Morgan Rogers mai shekara 23. Kungiyar ta bi sahun Chelsea da Manchester United wadanda ke son dan wasan Ingila. (Football Insider), external
Dan wasan tsakiyar Ingila Curtis Jones, mai shekara 25 na shirin barin Liverpool a wannan bazara inda Aston Villa ta kara kaimi wajan zawarcinsa (Teamtalk), external
Manchester City na son ta dauko dan wasan Newcastle United da Ingila Tino Livramento, mai shekara 23, ko da yake suna neman wasu 'yan wasa. (Teamtalk), external
Real Madrid na tunanin nada tsohon kocinta Jose Mourinho wanda ke jagorantar Benfica.(Record - in Portuguese), external
Real Madrid za ta yanke shawara kan makomar kocinta Alvaro Arbeloa a karshen kakar wasani. (Marca - in Spanish), external
Real Madrid na shirin yin garambawul ga 'yan wasanta a bazara, inda dan wasan Faransa Eduardo Camavinga, mai shekara 23, zai iya barin kungiyar. (Sport - in Spanish), external
Daukakar da Coventry City ta samu zuwa gasar wasani Firimiya yana nufin cewa dan wasan Najeriya Frank Onyeka mai shekara 28 da aka bada shi aro daga Brentford zai koma na dindindin . (Talksport), external
Lorient na tunanin daukar tsohon kocin Lens da Southampton Will Still a matsayin kocinta (L'Equipe - in French), external
Shugaban Napoli Aurelio de Laurentiis ya shirya wata ganawa da kocin kungiyar Antonio Conte domin su tattauna kan makomarsa a kungiyar . (Corriere dello Sport - in Italian)












