Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Yaƙin Iran da muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya 10/04/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai kan yaƙin Iran da kuma muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na ranar Juma'a 10 ga watan Afrilun 2026.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello, Haruna Kakangi, Usman Minjibir

  1. Tinubu ya jajanta kan kisan sojoji a Borno

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya jajanta wa al'ummar ƙasar kisan da aka yi wa sojoji a wani hari da mayaƙa suka kai kan wani sansanin soji a jihar Borno, arewa maso gabashin ƙasar.

    "Ina miƙa saƙon ta'aziyyata ga iyalan jajirtattun sojojinmu ƙarƙashin jagorancin Birgediya Janar Oseni Omoh Braimah, waɗanda suka rasa rayukansu wajen kare ƙasarmu a jihar Borno," kamar yadda shugaban ya bayyana a wani bayani da ya fitar a jiya Alhamis.

    A ɗaya ɓangare, cikin wata sanarwa, rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun daƙile harin da aka kai kan sansanin soji a garin Benisheik ranar Alhamis, sai dai rundunar ba ta tabbatar ko ƙaryata kashe sojoji ba.

    Wasu mazauna yankin da abin ya faru sun shaida wa BBC cewa babban sojan da ya jagoranci yunƙurin dakile harin Birgediya Janar Oseni Braimah na cikin waɗanda aka kashe.

    Kafar yaɗa labarai ta AFP ta bayar da rahoton kashe babban sojan, inda ta kafa hujja da bayanai daga majiyoyin tattara bayanan sirri, duk da cewa sojojin Najeriya ba su tabbatar da hakan ba.

    Harin na cikin hare-hare na baya-bayan nan da masu iƙirarin jihadi ke kaiwa kan sansanonin soji a arewa maso gabashin Najeriya, inda mayaƙa suka kwashe sama da shekara 10 suna kai hare-hare.

  2. Ko tattaunawar Iran da Amurka a Pakistan za ta yiwu?

    Ana shirye-shiryen tattaunawa tsakanin Iran da Amurka a Pakistan, wadda za ta gudana a cikin ƙarshen mako.

    Sai dai ya zuwa yanzu babu sanarwa a hukumance da ke nuna cewa tawagogin ɓangarorin biyu sun isa Islamabad, birnin da za a yi ganawar.

    Pakistan na ci gaba da kyautata fatan yiwuwar tattaunawar, da kuma fatan cewa za a samu fahimtar juna.

    To amma a halin yanzu kowa jininsa a ƙumba: A wani saƙon da aka wallafa a shafin sada zumunta, kafin daga baya aka goge, ministan tsaron Pakistan ya bayyana Isra'ila a matsayin "tsinuwa ga bil'adama".

    Isra'ila ta ce ba za a amince da irin haka ba daga ƙasar da ta ce za ta yi aikin sasanci.

  3. Yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Iran da Amurka na rawa

    Yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma tsakanin Amurka da Iran na fuskantar barazana, kwana ɗaya gabanin ganawar ƙeƙe-da-ƙeƙe da ake sa ran ɓangarorin biyu za su yi a Pakistan.

    Shugaba Trump na Amurka ya zargi Iran da karya sharuɗɗan yarjejeniyar ta hanyar ƙin buɗe mashigar Hormuz ga jiragen ruwan dakon man fetur.

    Hukumar kula da sufurin ruwa ta duniya ta ce jiragen ruwa ƙalilan ne suka samu damar ratsawa ta mashigar tun bayan cimma yarjejeniyar.

    A ɓangare ɗaya kuma Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare kan Hezbollah a ƙasar Lebanon - abin da Iran ta ce ya saɓa da sharuɗɗan yarjejeniyar.

  4. 'Ba haka muka yi da Iran ba': Trump kan mashigar Hormuz

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya zargi Iran da kin barin jiragen dakon mai su wuce ta mashigin Hormuz, yayin da yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma ke tanga-tangal, kafin hawa teburin sulhu a karshen makon nan a birnin Islamabad na Pakistan.

    A wasu jerin sakonni da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Mista Trump ya ce hakan ya saɓa wa yarjejeniyar da aka cimma, sannan ya gargaɗi Tehran da kada ta ƙaƙaba kuɗin wucewa ga jiragen ruwan.

    Buɗe mashigar Hormuz na daga cikin wani ɓangare na yarjejeniyar, to sai dai jirage tsiraru ne suka samu wucewa tun bayan fara aiki da yarjejeniyar.

    Tun da farko yayin wani jawabi da ya gabatar, jagoran addinin Iran din Ayatollah Mojtaba Khamenei, ya ce a yanzu mashigin na Hormuz ya shiga wani sabon mataki.

    A cikin wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin din kasar, Mojtaba Khamenei ya ce Iran na da yancin daukar fansa kan hare-haren Amurka da Isra’ila, kana za ta kare kawayenta, watau Hezbollah da sauran kungiyoyin yan turjiya a gabas ta tsakya.

    Ƙasar Pakistan ta ce tana da yaƙinin cewa tattaunawar zaman lafiyar da za a yi a Islamabad a karshen wannan mako za ta gudana kamar yadda aka tsara.

  5. Barka da warhaka!

    Barka da zuwa shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa, inda muke kawo muku labarai kan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya a wannan rana ta Juma'a 10 ga watan Afrilun 2026.

    Za ku iya yin sharhi kan labaran da muke sakawa a shafukanmu na sada zumunta: facebook, X, Instagram da kuma YouTube.

    Sannan ku shiga zaurenmu na BBC Hausa WhatsApp domin samun labarai da ɗumi-ɗumi.