Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya 02/04/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku rahoto kan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 02 ga watan Afrilun 2026.

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Haruna Kakangi

  1. Ƙasashen Gulf sun yi kira kan amfani da ƙarfi a buɗe mashigar Hormuz

    Majalisar ƙasashen Gulf ta buƙaci kwamitin tsaro ta Majalisar ɗinkin duniya kan ta amince da amfani da ƙarfi wajen kare mashigar Hormuz daga hare haren Iran.

    Sakatare janar na Majalisar Jasem Mohamed Al Budaiwi, ya yi kira ga mambobin kwamitin tsaron da su ɗauki dukkan matakan da suka dace wajen kare jiragen da ke bi ta mashigar, wadda ta kasance hanyar da kashi biyar na mai da iskar Gas ɗin da ake amfani da su a duniya ke bi.

    A gefe guda kuma, fiye da ƙasashe arba'in sun yi wata tattaunawa kan yadda za a lalaubo maslaha ta hanyar diflomasiyya kan yadda za a sake buɗe mashigar, duk da dai ba a samu wasu kwararan sakamako ba.

  2. Pakistan da Afghanistan na tattaunawa domin kawo ƙarshen yaƙi

    Jami'ai daga Pakistan da Afghanistan sun ce suna tattaunawa a China domin kawo ƙarshen rikici mafi muni tsakaninsu tun bayan da Taliban ta ƙwace iko a Kabul shekaru biyar da suka gabata.

    Islamabad ta ce ana tattaunawar ne a birnin Urumqi na China, kuma suna ƙoƙarin lalubo hanyoyin kawo ƙarshen rikicin kan iayakar.

    Rikicin wanda aka soma tun watan Oktoban bara, ya yi sanadin mutuwa gomman mutane a ɓangarorin biyu.

    Rahotanni sun bayyana cewa ana sa ran za a tattauna ne kan yiwuwar tsagaita wuta, da kuma sake buɗe kan iyakar ƙasashen domin bayar da damar yin tafiye tafiye da kuma kasuwanci.

  3. Ko Iran ta yi wa Amurka da Isra'ila ba-zata?

    Lokacin da Amurka da Isra'ila suka ƙaddamar da hare-haren haɗin gwiwa kan Iran ranar 28 ga Fabrairun 2026, tambayar ita ce tsawon wani lokaci yaƙin zai ɗauka?

    Yanzu lamarin ya wuce kwanaki, makonni zuwa watanni kuma babu alamar kawo karshensa nan kusa.

    A ranar 31 ga Maris (Talata), wata guda da kwana uku da soma yaƙin, Donald Trump ya ce Amurka za ta fice daga Iran cikin "makonni biyu zuwa uku".

    Abin da haka ke nufi shi ne, yaƙin ba zai kare nan take ba.

    Tun da aka soma yaƙin, duk abubuwan da Trump ya yi fata ba su faru ba.

  4. Falle Ɗaya: Me take nufi kuma daga ina ta samo asali?

    Idan akwai wata kalma da za ta samu karɓuwa a wurin ƴan siyasa musamman a arewacin Najeriya to ita ce kalmar Falle Ɗaya wadda a yanzu haka amonta kawai ake ji na tashi a cikin wake da waƙoƙin siyasa.

    Masana adabi da na kimiyyar siyasa na cewa ƴan siyasa kan yi amfani da salo na kalmomi a magana ko kuma a cikin waƙe domin jan hankali masu zaɓe.

    Za a iya cewa a mafi yawancin lokaci irin waɗannan kalamai na jan hankali na samo asali ne daga birnin Kano wanda shi ne cibiyar siyasar arewacin Najeriya.

    BBC ta yi nazari dangane da wannan kalma da asalinta da ma'anarta da kuma irin tasirin da za ta iya yi a kakar zaɓen 2027 da ke tafe a Najeriya.

  5. Kamaru na shirin dawo da muƙamin mataimakin shugaban ƙasa

    Majalisar dokokin Kamaru na duba yiwuwar wani ƙudurin da zai ƙirƙiri muƙamin mataimakin shugaban ƙasa,

    Wannan na daga cikin buƙatun da shugaba Paul Biya ya gabatar a ƙokarinsa na gyara kundin tsarin mulkin ƙasar.

    Gwamnatin ƙasar ta ce, matakin na daga cikin alƙawuran da Biya ya ɗauka na ganin ya samar da sauye-sauye da za su inganta harkokin gwamnati.

    Wani ƙuduri da BBC ta gani, ya nuna cewa shugaban ƙasa na da hurumin naɗawa ko cire mataimakinsa, kuma shi zai ci gaba da jan ragamar mulki idan shugaban ya mutu, ko ya kasance ba shi da ƙoshin lafiyar gudanar da mulki.

    Sai dai kuma, shugaban riƙon ba shi da ikon gyara kundin dokokin ƙasar ko ya yi takarar shugaban ƙasar.

    A baya dai, shugaban majalisar dattawa ne ke da ikon ya gaji shugaban ƙasar, amma kuma a wannan sabon ƙudurin an bayyana cewa za a ɗauki matakin ne domin ba majalisar damar maida hankali kan ayyukanta na dokoki.

    Sai dai a sabon ƙudurin, za a ci gaba da riƙe ofishin Firaminista, duk da akwai mataimakin shugaban ƙasa.

    Bugu da ƙari, za a buƙaci dukkanin masu riƙe da muƙaman siyasa a ƙasar, kama daga shugaban ƙasa da mataimakinsa, da Firaminista, da ministoci da ƴanmajalisa da sauran masu muƙamai a jihohi su bayyana kadarorinsu a farko da kuma ƙarshen wa’adin mulkinsu.

    Daga shekarar 1961 zuwa 1972, Kamaru na bin tsarin shugaba mai cikakken iko, domin mutunta dukkanin bangarorin ƙasar da ke amfani da yaren turancin da faransanci

    A lokacin, akwai ofishin mataimakin shugaban ƙasa. Amma kuma daga shekarar 1972, aka yi gyaran dokoki, inda aka koma amfani da tsarin Firaminsta.

    An daɗe dai ana cece-ku-ce ka wanda zai gaji Biya idan ya bar mulki, kuma har yanzu babu tabbaci game da makomar Kamaru duk da ana kokarin maido da ofishin mataimakin shugaban ƙasa.

    Bayan nazari kan ƙudurin ne, ake sa ran ƴanmajalisar ƙasar su kaɗa ƙuri’a kan amincewa da gyaran kundin dokokin ƙasar ko akasin haka.

    Jam’iyar Biya ce dai ita ce ke da rinjaye a duka majalisun ƙasar, inda masu sharhi ke ganin akwai alamun za a amince da buƙatar.

  6. Ministocin harkokin waje ban da Amurka za su tattauna buɗe mashigar Hormuz

    Ministocin harkokin waje daga kasashe da dama, ban da Amurka, za su gudanar da wani taro a yau domin tattauna hanyoyin sake buɗe mashigar Hormuz da tabbatar da tsaron zirga-zirgar jiragen ruwa.

    Shugabannin kasashe 35 sun rattaba hannu kan wata sanarwa ta hadin gwiwa, inda suka ce a shirye suke su bayar da gudunmawa domin tabbatar da tsaron wucewar jiragen ruwa ta wannan muhimmiyar mashiga.

    Ana sa ran ministocin harkokin wajen wadannan ƙasashe za su tattauna hanyoyin diflomasiyya da siyasa da za su taimaka wajen sake buɗe mashigar.

    Tun da Iran ta ce mashigar zai kasance a rufe ga ƙasashen da ke da alaƙa da Amurka da Iran, Firaministan Birtaniya Keir Starmer ya bayyana cewa buɗe ta ba zai zama aiki mai sauki ba.

    ƙasashe irin su Birtaniya, Faransa, Jamus, Australia da kasashen yankin Gulf na cikin wadanda ake sa ran za su halarci taron, amma Amurka ba za ta shiga ba.

    Sakatariyar harkokin wajen Birtaniya, Yvette Cooper, za ta halarci wannan taro ita ma.

    Babban taron buri shi ne tabbatar da zirga-zirgar jiragen ruwa cikin aminci, rage farashin mai, da kuma kara samar da takin zamani domin bunkasa noma da samar da abinci.

  7. Tinubu ya gana da shugaban Chadi

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya karɓi baƙucnin shugaban Chadi Idriss Déby a ranar Alhamis.

    Sun yi ganawar ce cikin sirri a fadar shugaban Najeriya da ke Abuja, inda ake sa ran sun tattauna kan batutuwa da suka shafi tattalin arziki da kuma haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu.

    Ganawar na zuwa ne gab da shugaba Tinubu zai tafi jihar Filato domin yin jaje game da kashe-kashen da suka faru.

    Najeriya da Chadi na taka muhimmiyar rawa wajen yaƙi da matsalar tsaro a yankin tafkin Chadi.

  8. MDD ta buƙaci Amurka da Isra'ila su dakatar da yaƙi da Iran

    Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya (MDD), António Guterres ya buƙaci a dakatar da yaƙin da ake yi tsakanin Amurka da Isra'ila da Iran nan take.

    Ya koka kan yadda yaƙin ya haifar da tashin farashin kayan masarufi da makamashi a duniya.

    Guterres ya ce al'umma na shan wahala saboda yaƙin.

    "Idan aka ci gaba da rufe mashigar Hormuz, masu ƙaramin ƙarfi ne za su sha wahala," in ji shi.

    Ya kuma yi kira da a samar da masalaha cikin ruwan sanyi, domin jin daɗin jama'a kuma a mutunta dokokin mallakar makamin nukiliya.

    Ya ce: "Kira na ga Amurka da Isra'ila shi ne, su dakatar da yaƙin, saboda yana jefa al'umma cikin matsanancin hali’

    "Ita kuma Iran, ta daina kai hare-hare kan maƙotanta".

  9. ADC ta buƙaci a cire shugaban INEC ba tare da ɓata lokaci ba

    Jam'iyyar adawa ta ADC a Najeriya ta buƙaci a cire shugaban hukumar zaɓen ƙasa INEC, Farfesa Joash Amupitan.

    ADC ta ce hukumar ta koma ƴan amshin shatar jam'iyya mai mulki ta APC, kuma ba za ta iya amincewa da hukumar a zaɓen 2027.

    Hukumar zaɓen Najeriya, INEC da ta cire sunan Sanata David Mark a matsayin shugaban jam'iyyar ADC tare da Abdulra'uf Aregbesola a matsayin sakatare janar na jam'iyyar daga na'urarta.

    A wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, INEC ta ce ta ɗauki matakin hakan ne sakamakon hukuncin kotun ƙoli da kuma shari'ar da ke gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja dangane da rikicin da ake yi tsakanin ɓangarori biyu wato David Mark da na Nafi'u Gombe.

    Sai dai jagororin ADCn, a wani taron manema labarai ƙarkashin jagorancin Sanata David Mark, sun ce hankalin jam'iyyar bai kwanta da shugabancin INEC ba.

    "Muna buƙatar a cire shugaban INEC ba tare da ɓata lokaci ba, da kuma sauran kwamishinonin zaɓe na ƙasa. Hukumar ba za ta iya gudanar da sahihin zaɓe ba."

    Jama'iyyar ADCn ta yi watsi da matakin da hukumar zaɓen ƙasar INEC ta ɗauka inda ta ce za ta ci gaba da gudanar da harokokinta.

    "Za mu ci gaba da gudanar da lamuran jam'iyyar mu kamar yadda muka tsara, saboda babu wata dokar da ta ce sai INEC ta halarci tarukanmu," in ji Mark.

  10. Harin Isra'ila ya kashe mutum biyu a Iran

    Mutum biyu sun mutu sakamakon wani hari da Isra'ila ta kai kan wata gada da ke yankin Karaj, kusa da birnin Tehran.

    Matamakin babban jami'in tsaro na ofishin gwamnan Alborz, ya ce mutane da dama sun jikkata sakamakon harin, kamar yadda kafofin yaɗa labaran ƙasar suka ruwaito.

    Sai dai ba a sake kai wani hari kan gadar ba bayan wannan.

    Wakiliyar BBC ta ce, ta samu labarin ana ta ɗauke wuta a wasu yankunan garin bayan harin.

    BBC ta tuntuɓi rundunar tsaron Isra'ila IDF, amma ta ce ba ta da masaniya game da harin.

  11. Samar da tsaro ba aikin gwamnatin tarayya ba ne kawai - Aliyu

    Gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu ya ce “kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu ba aiki ne na gwamnatin tarayya kawai ba’’, inda a dalilin hakan ne ya ce gwamnatinsa ke ƙoƙarin ganin ta tallafa wajen inganta tsaro a jihar.

    Gwamnan ya faɗi haka ne sa’ilin da ya gana da babban sufetan ƴansandan Najeriya Olatunji Disu a Abuja, babban birnin Najeriya.

    Sokoto na daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ke fama da matsalar tsaro, inda ƴan fashin daji ke far wa ƙauyuka suna kashewa tare da garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa.

    A jawabin da ya yi lokacin da ya gana da babban sufetan, Aliyu ya ce duk da matsalar tsaro da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa a jihar Sokoto, amma jami’an tsaro sun samu nasara a yaƙin da suke yi da matsalar.

    Ya bayyana cewa tun bayan zama gwamnan jihar Sokoto, ya sayo tare da raba motocin sintiri guda 200 ga jami’an tsaro domin taimaka musu a yakin da suke yi da matsalar tsaro a yankunan jihar.

    “Mun yi hakan ne saboda mun yi amannar cewa tsaron rayuka da dukiyar mutanenmu nauyi ne na kowa da kowa,” a cewar gwamna Aliyu.

    Duk da ƙoƙarin da gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce tana yi, har yanzu ƴan fashin daji na kai hare-hare tare da garkuwa da mutane a yankin arewa maso yammacin ƙasar, yayin da ake fama da harin ƴan bindiga a jihohin arewa ta tsakiyar ƙasar.

  12. Yadda nake kula da ƴata mai lalurar 'Autism'

    Albarkacin ranar faɗakarwa kan lalurar Autism, mun zanta da wata mahaifiya wadda take wayar da kan iyaye a shafukan sada zumunta kan lalurar. Ta kuma faɗa mana yadda take kula da ʼyarta wadda ke fama da lalurar.

    Furodusa - Aisha Aliyu Jaafar/Isiyaku Muhammed

    Tace hoto - Fatima Othman

  13. Iran ta tabbatar da kashe kwamandan rundunar Fatehin ta IRGC

    Kafofin yaɗa labaran Iran sun ruwaito cewa an kashe Mohammad Ali Fathalizadeh, kwamandan rundunar Fatehin.

    Kamfanin dillancin labaran soji na “Holy Defense” ya ruwaito cewa an kashe Fathalizadeh ne a hare-haren jiya.

    A cewar waɗannan kafafen yaɗa labarai, Fathalizadeh ne mataimakin shugaban ayyuka rundunar juyin juya halin Iran sannan kuma kwamandan rundunar musamman ta Fatehin ƙarƙashin Basij.

  14. Iran ta harba makamai masu linzami 19 da jirage marasa matuƙa 26 kan UAE

    Ma’aikatar tsaron ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) Iran ta kai wa ƙasar hare-haren makamai masu linzami guda 19 da kuma jirage marasa matuki guda 26 a yau.

    A wata sanarwa da ma’aikatar ta wallafa a shafinta na X, ta bayyana cewa tun bayan fara wannan rikici, rundunar tsaron sararin samaniyar ƙasar ta kakkaɓo kusan makamai masu linzami 457 da kuma jirage marasa matuki 2,038.

    Hukumomin sun jaddada cewa suna cikin shiri koyaushe domin kare tsaron ƙasa da kuma mayar da martanin gaggawa ga duk wata barazana.

  15. China ta bukaci dakatar da hare-haren soji kan Iran

    China ta yi kira ga dakatar da dukkan harkokin soji a Gabas ta Tsakiya, bayan shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar kai hare-hare masu ƙarfi kan Iran nan gaba.

    Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Waje ta China, Mao Ning, ya ce, “Matakin soja ba zai magance matsalar ba, kuma ƙara tayar da rikici ba ya amfanar kowanne bangare.”

    Ya kuma yi kira ga “duk ɓangarorin da abin ya shafa da su dakatar da matakin soja nan take.”

    Haka kuma, wani mai magana da yawun ma’aikatar ya ce babban dalilin katsewar jigilar jiragen ruwa ta mashigin Hormuz shine “hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai kan Iran."

  16. Ƙauyen da ake zargin ƴansanda sun ƙona a Kano

    Al'ummomin wasu garuruwa a yankin ƙaramar hukumar Wudil a jihar Kano, da ke Najeriya, sun zargi ƴansanda da ƙone musu gidaje da wuraren sana'a da kayan abinci da kuma dabbobi a sanadiyyar wata hatsaniya kan mallakar gonaki.

    Rikicin, wanda yanzu haka yake gaban ƙotu, na da alaƙa da batun mallakar gonakin wata fadama a yankin ƙananan hukumomin Wudil da Bunkure.

  17. Za mu bar jiragen da ba su da alaƙa da Amurka su bi ta mashigar Hormuz - Iran

    Iran ta ce za ta buɗe mashigar Hormuz ga jiragen ruwa da ba su da alaka da Amurka ko Isra’ila.

    Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Waje ta Iran, Esmail Baghaei, ya ce Iran za ta bar jiragen ruwa su wuce ta mashigin Hormuz – hanya mafi muhimmanci wajen jigilar man fetur – muddin “na su da alaƙa da Amurka ko Isra'ila.”

    A wata hira da tashar talabijin Newzroom Afrika, Baghaei ya ce jiragen ruwa za su samu izinin wucewa ta mashigin ne “bayan haɗa kai da hukumominmu kamar yadda ya dace.”

    Yayinda yake magana kan rikicin gabaɗaya, Baghaei ya ce Iran ba za ta lamunci “zagayowar yaƙi da tattaunawa ko tsagaita wuta ba".

    A watan Yuni, wani yaƙi na kwanaki 12 tsakanin Iran da Isra’ila ya haɗa da hare-haren Amurka kan wasu wuraren nukiliya da sojin Iran.

    Ya ce, “Sun ce mu dakata, mun dakata, amma bayan watanni tara, su suka sake farawa.”

  18. Iran ta ce za ta faɗaɗa hare-harenta bayan barazanar Trump

    Wani mai magana da yawun rundunar sojin Iran ya yi gargaɗi cewa Amurka da Isra’ila za su “ɗanɗana kuɗarsu” kan tashin hankalin da suka haifar sakamakon hare-haren da suke kai wa inda ya ce Iran za ta faɗaɗa hare-harenta bayan narazanar Trump na jaddada anniyarsa ta ci gaba da kai mata hare-hare

    A cikin wata sanarwa da gidan jaridar Tasnim da kafofin Fars suka fitar, mai magana da yawun rundunar ya ce kasashen biyu ba su da cikakken bayani game da ƙarfin soji da kayan aikin Iran.

    Ya kuma bayyana cewa samar da kayan yaƙi a Iran “yana gudana a wurare da ba ku sani ba kwata-kwata,” inda ya yi watsi da iƙirarin Trump cewa Iran ta yi ƙasa da kayan yaƙi sosai.

  19. Mun kakkaɓo wani jirgi mara matuƙi da aka harba mana - Iran

    Rundunar juyin juya halin Iran ta tabbatar da cewa dakarunta sun kakkaɓo wani jirgin yaƙi mara matuƙi ƙirar Hermes 900 da aka harba mata.

    Rundunar ta ce ta kakkaɓo makamin ne daga sararin samaniyar birnin Shiraz a safiyar yau.

    Yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila dai na ƙara tsananta inda duka ɓangarorin ke ci gaba da kai wa juna hari da makamai masu linzami da na jiragen yaƙi mara matuƙa.

  20. Iran ta zantar da hukunci kisa kan ɗaya daga cikin masu zanga-zanga

    Hukumar labarai ta Mizan wacce ke da alaƙa da kotun Iran ta ce, an kashe Amir Hossein Hatami, ɗaya daga cikin waɗanda aka kama yayin zanga-zangar watan Janairu, a yau.

    Mizan ta bayyana cewa, “Amir Hossein Hatami tare da wasu masu tayar da tarzoma sun kai hari wani muhimmin wurin soja a Tehran, bayan sun lalata shi tare da ƙona shi.”

    Kafofin shari’a na Iran sun rubuta cewa, “Bayan jami’an tsaro sun kama Hatami kuma ya amincewa da tuhumar da ake masa, ya bayyana rawar da ya taka wajen lalatawa da ƙona wannan wurin na soja lokacin shari’a.”

    Har yanzu ba a fitar da cikakken bayani ba game da tuhumar da kuma yadda aka gudanar da shari’ar ba.

    Wannan shi ne hukuncin kisa ta biyu da aka yanke a Iran cikin wannan wata.