An kashe ƴan ƙungiyar Al-Shabab guda 27

Asalin hoton, Getty Images
Rahotanni daga Somalia na cewa dakarun gwamnati sun kashe mayaƙan Al‑Shabab 27, ciki har da manyan kwamandojinsu, a wani samame da suka kai a kudancin ƙasar.
Rahoton ya ce an gudanar da samamen ne a jihar Jubaland, kuma ya samu goyon bayan hare-haren jirage marasa matuƙi daga ƙawayen ƙasa da ƙasa.
A baya dai sojojin Amurka sun kai irin waɗannan hare-hare ta sama domin taimaka wa Somalia a yaƙin da take yi da Al‑Shabab.
Alshabab dai ta shafe sama da shekaru 20 tana tayar da ƙayar baya, da nufin kifar da gwamnati da kuma ƙaƙaba tsauraran dokokin addini.














