An dawo da sabin ɗin intanet a yankin Tigray na Habasha

Asalin hoton, Getty Images
Sojojin gwamnatin tarayya sun karɓi iko da Mekelle, babban birnin yankin Tigray na Habasha, bayan dakarun Tigray sun janye daga birnin. Haka kuma, an dawo da hanyoyin sadarwar wayar tarho da intanet a wasu sassan yankin.
Kungiyar Tigray People's Liberation Front TPLF ta ce ta janye dakarunta daga Mekelle ne domin kauce wa asarar rayukan fararen hula. Ta kuma ce gwamnatin yankin za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta na wucin gadi daga wani wuri na daban.
Mazauna yankin sun ce yanzu an dawo da sabis na intanet da hanyoyin sadarwar tarho a wasu sassan Tigray bayan shafe mako guda ana fama da katsewar sadarwa.
Sabbin faɗace-faɗacen sun ƙara tayar da fargabar cewa rikicin na iya bazuwa fiye da iyakokin Habasha, ganin cewa tashin hankali ya riga ya yi ƙamari a yankin Kusurwar Gabashin Afrika.
Habasha ta zargi ƙasashen Eritrea, Masar da Sudan da goyon bayan ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai da ke adawa da gwamnati.
Tarayyar Afirka AU ta yi kira ga dukkan ƙasashe da su nuna matuƙar haƙuri tare da kauce wa duk wani mataki da zai ƙara ruruta wutar rikicin. Haka nan ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta yi irin wannan kira. Ta kuma yi gargaɗin cewa tashin hankalin da ke tsakanin Habasha da Eritrea na iya kawo cikas ga haɗin gwiwar da Amurka ke yi da ƙasashen yankin.
Sabon tashin hankalin ya sake tuno da mummunan yaƙin da ya addabi arewacin Habasha tsakanin shekarun 2020 zuwa 2022. Tarayyar Afirka ta kiyasta cewa fiye da mutane rabin miliyan ne suka rasa rayukansu a wannan rikici.
































