Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 30/06/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 30 ga watan Yunin 2026.

Taƙaitattu

Skip Bidiyo and continue reading
  • Zanga-zanga a aAfirka ta Kudu
  • xxx
  • Ummulkhairi Aliyu
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Arsenal
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Kutama
  • xxx

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida, Haruna Kakangi, da Ahmad Kabo Idris.

  1. Dubban mutane a Venezuela na tsananin buƙatar abinci da matsuguni - MDD

    UN

    Asalin hoton, Getty Images

    Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa dubban mutane na buƙatar abinci da matsuguni cikin gaggawa bayan tagwayen girgizar ƙasa da ta auku a Venezuela.

    Hukumar ‘yan gudun hijira ta Majalisar ta ce ƙarancin abinci ya yi ƙamari, ayyukan yau da kullum sun tsaya cik, kuma sadarwa ta takaita sosai a birnin La Guaira, inda girgizar kasar ta fi muni.

    Rundunar sojin Amurka ta sake buɗe tashar jirgin ruwa a birnin domin kai kayan agaji da ake matukar buƙata.

    Yawan mutanen da aka tabbatar sun mutu a girgizar ƙasar zuwa yanzu ya kai kusan dubu biyu, yayin da dubban mutane kuma ba a san inda suke ba.

  2. Kotun kolin Amurka ta yanke hukunce-hukunce kan masu sauya jinsi

    US Court

    Asalin hoton, Getty Images

    Kotun kolin ta Amurka kuma ta yanke wasu hukunce-hukunce biyu da suka dadada wa 'yan jam’iyyar Republican.

    Alƙalan sun tabbatar da dokokin jihohi biyu da Republican ke mulki da suka hana 'yan wasa masu sauya jinsi shiga wasanni a makarantun, hukuncin da zai zama na dogaro ga sauran jihohin ƙasar.

    Daya hukuncin kuma da kotun ta yi wanda ka iya shafar zaɓen rabin wa’adi, shi ne, kotun ta soke yawan kudin da aka iyakance za a iya kashewa a yaƙin neman zaɓe na tarayya.

    'Yan Republican na da fifiko sosai na yawan kudi, yayin da ake shirin zaben na watan Nuwamba.

  3. Gwamnatin Najeriya na son tara naira tiriliyan 2.5 daga kuɗaɗen haraji a 2026

    Tinubu

    Asalin hoton, Bayo Onanuga/X

    Gwamnatin Najeriya ta ƙudiri aniyar samun naira tiriliyan 2.5 na kuɗaɗen shiga na cikin gida a shekarar 2026.

    Mukaddashin Shugaban Hukumar Kula da Ɗa'a a Harkokin Kasafin Kuɗi ta Ƙasa, Charles Abana ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa tsakanin shugabannin hukumar da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, a Abuja.

    A wata sanarwa da mai magana da yawun Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Chris Ugwuegbulam, ya fitar, Mista Abana ya ce an ɗauki wannan mataki ne bayan hukumar ta sa ido kan kuɗaɗen shiga na kusan naira tiriliyan 1.84 da ma'aikatun gwamnati da hukumominta suka samar zuwa watan Satumban 2025.

    Ya ce, "Ta hanyar ƙara sa ido kan rarar kuɗaɗen shiga na kamfanonin gwamnati da kuma kuɗaɗen shiga da ma'aikatu da hukumomin gwamnati ke samarwa, hukumar ta lura da kuɗaɗen shiga na kusan naira tiriliyan 1.84 zuwa watan Satumban 2025, kuma yanzu ta ƙudiri aniyar samun naira tiriliyan 2.5 a matsayin kuɗaɗen shiga na shekarar 2026."

  4. Trump ya sha kaye a Kotun Ƙoli kan dokar zama ɗan Amurka

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Kotun Ƙolin Amurka ta yi watsi da umarnin shugaban ƙasar, Donald Trump ya aiwatar, wanda ya nemi kawo ƙarshen bai wa jariran da aka haifa a ƙasar izinin zama 'yan ƙasa kai tsaye.

    Alƙalan kotun shida sun amince da hukuncin inda suka tabbatar da cewa haƙƙin zama ɗan ƙasa ta hanyar haihuwa yana kunshe cikin kundin tsarin mulkin Amurka, yayin da uku kuma suke da ja.

    Donald Trump ya bayyana hukuncin a matsayin "abin takaici" amma ya ce "Majalisar Dokoki za ta iya kafa doka akan hakan."

    Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama sun yi maraba da hukuncin.

    A watan Afrilu ne, Mista Trump ya zama shugaban Amurka na farko da ke kan mulki da ya halarci zaman Kotun Ƙoli yayin sauraron shari'ar, duk da cewa ya fice kafin a kammala zaman.

  5. China ce kaɗai ke ci gaba da sayen man Iran - Amurka

    Oil

    Asalin hoton, Getty Images

    Sakataren Baitul Malin Amurka ya ce China ce kaɗai ƙasar da ke ci gaba da sayen man Iran, yayin da sauran ƙasashe ke kauce wa sayensa saboda fargabar yiwuwar dawo da takunkuman Amurka.

    Scott Besant ya shaida wa kafar watsa labarai ta Fox News cewa, "Iran ba ta samu damar sayar da man fetur ɗinta yadda ya kamata ba, saboda masu saya na fargabar cewa takunkumi na iya dawowa."

    Bayan cimma fahimta tsakanin Iran da Amurka, Ma'aikatar Baitul Malin Amurka ta bayar da wani izini na bai ɗaya, wadda ta dakatar da takunkuman da aka ƙakaba kan man Iran da kayayyakin da ake samarwa daga man fetur na tsawon kwanaki 60.

    Mista Besant ya ce baya ga China, wadda ta ci gaba da sayen man Iran tun lokacin da takunkuman ke aiki, babu wata ƙasa da ta sayi man Iran, abin da ya sa har yanzu ake sayar da shi ƙasa da farashin kasuwa.

    Ya ƙara da cewa ƙarancin masu sayen man Iran na ƙara ƙarfafa yunƙurin Tehran na neman jan hankalin Washington.

  6. China ce kaɗai ke sayen man Iran - Amurka

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Sakataren baitul malin Amurka ya bayyana cewa China ce kaɗai ke ci gaba da sayen man Iran, inda ya ce sauran ƙasashe na kauce wa hakan saboda fargabar sake dawo da takunkumin Amurka.

    A cewarsa, damuwar yiwuwar tsaurara matakan tattalin arziki na sa masu saye su yi taka-tsantsan wajen shiga kasuwar man Iran.

    Ya ce duk da wata yarjejeniya da aka samu tsakanin Amurka da Iran, wadda ta sa aka sassauta takunkumi na tsawon kwanaki 60 kan man fetur da kayayyakin mai, Iran har yanzu ba ta samu gagarumin sauƙi wajen sayar da man nata ba.

    Wannan na nuna cewa sassaucin bai ja hankalin sabbin masu saye daga ƙasashe daban-daban ba.

    Sakataren ya kara da cewa China ce kawai ta ci gaba da siyan man Iran tun lokacin takunkumi, yayin da babu wasu ƙasashe da suka shiga sayen a hukumance.

    Hakan ya sa ake sayar da man Iran a farashi mai rahusa a kasuwa domin jawo hankalin masu saye.

  7. Yadda ake zanga-zangar ƙyamar baƙi a Afrika ta Kudu

    Bayanan bidiyo, Latsa wannan alamar domin kallon bidiyon

    Ana ci gaba da gudanar da zanga‑zangar ƙyamar baƙi a sassa daban‑daban na Afirka ta Kudu, lamarin da ya sa aka jibge jami’an tsaro saboda fargabar rikice‑rikice.

    Shugaba Cyril Ramaphosa ya buƙaci masu zanga‑zangar su guji tashin hankali, yana mai jaddada cewa dole ne a gudanar da zanga‑zanga cikin lumana ba tare da tsoratarwa ba.

    Zanga‑zangar na da alaƙa da wa’adin da wasu ƙungiyoyi suka bai wa baƙin da ba su da takaddar izinin zama cikin ƙasar da su fice.

  8. Ba a shirya wata ganawa tsakanin Iran da Amurka ba a Doha - Qatar

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙasar Qatar ta tabbatar da cewa babu wani babban jami’in Iran da ke birnin Doha a halin yanzu da sunan tattaunawar zaman lafiya duk da cewa manyan wakilan shugaban Amurka Donald Trump sun isa ƙasar

    Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Qatar, Majid Ansari, ya ce Steve Whittaker da Jared Kushner sun isa Doha ne domin ganawa da masu shiga tsakani, tare da tattauna wasu batutuwan yankin ciki har da halin da ake ciki a Lebanon.

    Ya jaddada cewa babu wata ganawa da aka shirya tsakanin Iran da Amurka a kwanaki masu zuwa.

    Wannan bayani ya yi daidai da matsayar jami’an Iran, amma ya sha bamban da abin da Donald Trump ya faɗa cewa za a yi wata babbar ganawa da Amurka a Doha bisa buƙatar Iran.

    Iran ta faɗa tun da farko cewa babu wata tattaunawa da aka tsara tsakaninta da Amurka tare da bayyana cewa ziyarar da jami'anta za su kai Doha kan batun kuɗaɗenta ne da aka ƙwace.

  9. Kamfanin ƙera motoci ya dawo da ma'aikatan da ya kora bayan gazawar AI

    xxx

    Asalin hoton, Getty Images

    Kamfanin ƙera motoci na Amurka, Ford, ya sake ɗaukar tsofaffin ma’aikata sama da 300 bayan fasahar AI ta kasa cika aikin duba inganci yadda ake tsammani.

    Da farko kamfanin ya rungumi AI domin rage kuɗin aiki, har ma ya girke kyamarori masu basirar AI a masana’antunsa. Amma shugabanninsa sun amince cewa tsarin bai kai matakin da ake buƙata ba.

    Mataimakin shugaban injiniyoyi, Charles Poon, ya ce AI na aiki ne gwargwadon ingancin bayanan da aka horar da shi a kai, yana mai jaddada cewa an yi watsi da ƙwarewar gogaggun ma’aikata wanda ya sa yanzu ake sake komawa gare su don inganta aiki da rage kura-kurai.

  10. Rukuni na uku na ƴan Najeriya da aka kwashe daga Afrika ta Kudu ya isa Lagos

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Rukuni na uku na ‘yan Najeriya da aka kwashe daga kasar Afirka ta Kudu sun isa birnin Lagos, yayin da gwamnati ke ci gaba da kokarin dawo da ‘yan kasar cikin aminci.

    Jirgin da ya kawo su ya sauka ne a filin jirgin sama na Murtala Muhammed, inda jami’an gwamnati da na kula da ‘yan gudun hijira suka tarbe su.

    Ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta ce waɗanda aka dawo da su sun kai 264 wanda ya haɗa da maza, mata da yara,

    Wasu daga cikin wadanda suka iso sun ce sun sha wahala sakamakon rashin tsaro, da kuma takurawa rayuwa a wasu yankunan kasar ta Afirka ta Kudu.

    An fara kwaso mutanen ne bayan shafe makonni ana zanga-zangar ƙyamar baƙi a wasu sassan Afirka ta Kudu, da kuma cikar wa’adin ranar 30 ga Yuni da masu zanga-zangar suka bai wa baƙin da ba a wa rijistar zama a ƙasar ba su bar ƙasar. Lamarin ya janyo wasu ‘yan Afirka neman taimakon komawa ƙasashensu.

    A baya, kusan mutum 270 aka dawo da su a jirgin farko, yayin da kusan 66 suka biyo baya a rukuni na biyu. Wasu ‘yan Najeriya na cewa zanga-zangar ta bar su cikin damuwa da rashin tabbas kan makomarsu.

    Kakakin ma’aikatar, Kimiebi Ebienfa, ya ce gwamnati ta shirya kwaso mutanen ne saboda kare lafiyarsu, yana mai cewa duk wanda ya yi rajista don dawowa shi dole ne a taimaka masa.

    Ya kuma bayyana cewa an shirya karin jirage uku a ranakun 3, 6 da 9 ga Yuli ga waɗanda suka yi rajista suna son a dawo da su.

    Gwamnati ta shawarci ‘yan Najeriya da ke can da su bi dokokin ƙasar kuma su guji rikici, tana mai lura da yadda lamura ke tafiya.

  11. Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 13 a Ghana

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Aƙalla mutum 13 ne suka mutusakamakon ambaliyar ruwa da ta afku a babban birnin Ghana, Accra, bayan ruwan sama mai ƙarfi da aka yi a ranar Litinin.

    Ambaliyar ta kuma lalata gidaje da kadarori da dama.

    Hukumar kashe gobara ta ƙasar ta ce ana fargabar yawan mutanen da suka mutu na iya ƙaruwa yayin da ake ci gaba da aikin ceto.

    Bidiyoyi da ke yawo a kafafen sada zumunta sun nuna gidaje da motoci sun nutse a cikin ruwa, musamman a ƙananan yankuna da suka fi fama da ambaliyar, lamarin da ya haddasa tsaikon zirga-zirga.

    Duk da cewa yawancin ruwan ya ragu, mutanen da abin ya shafa na ci gaba da ƙididdige asarar da suka yi.

    Shugaban ƙasar, John Mahama, ya bayar da umarnin rusa dukkan gine-ginen da aka yi a hanyoyin ruwa, yana mai cewa irin waɗannan ayyuka na jefa al’umma cikin haɗari.

    Haka kuma ya bayyana cewa ana samun ƙaruwa a yawan ruwan sama sakamakon sauyin yanayi, inda aka samu milimita 140 na ruwan sama a rana guda, fiye da adadin da aka samu a bara.

    Gwamnatin ƙasar ta shawarci mazauna yankunan da abin ya shafa su koma wurare mafi tsaro, tare da gargadin direbobi da su guji hanyoyin da ruwa ya mamaye.

    Ambaliyar ta kuma katse wutar lantarki a wasu sassan birnin, yayin da aka tura jami’an tsaro da na agaji domin taimakawa waɗanda iftila'in ya shafa.

  12. Za a yi sauye-sauye a tsarin shirin NYSC

    ....

    Asalin hoton, NYSC/X

    Majalisar zartarwa ta Najeriya (FEC) ta amince da yin manyan sauye-sauye a tsarin shirin bautar ƙasa na NYSC, ciki har da mayar da shugabancinsa hannun farar hula maimakon sojoji, da kuma tsawaita lokacin atisaye a sansani daga makonni uku zuwa shida.

    An cimma wannan matsaya ne a taron FEC na ranar Litinin a Abuja, wanda shi ne karo na farko da aka yi cikakken bita ga shirin tun bayan kafa shi a shekarar 1973.

    A ƙarƙashin sabon tsarin, farar hula za su jagoranci harkokin NYSC, yayin da sojoji za su ci gaba da bayar da tsaro ga masu yi wa ƙasa hidima.

    Gwamnatin tarayya ta kuma umarci Babban Lauyan Ƙasa da Ma’aikatar kula da ci gaban matasa su gyara dokar NYSC da sauran ƙa’idoji domin bai wa sauye-sauyen cikakken tushe na doka.

    Ministan kula da matasa, Ayodele Olawande, ya ce an aiwatar da wannan matakin ne domin inganta NYSC ya koma shiri da ke haɓaka ƙwarewa da samar da damar aikin yi.

    Ya ƙara da cewa za a ɓullo da tsarin kiran masu yi wa ƙasa hidima da tura su bisa la’akari da tsaro, tare da mai da hankali kan koyar da shugabanci da kasuwanci da ƙwarewar zamani.

  13. Ba mu yarda da maƙiyanmu ba, zaune muke a shirye - Iran

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan tsaron Iran na riƙo ya ce ƙasar ba ta yarda da maƙiyanta ba, kuma zaune ƙsar take a shirye wajen fuskantar duk wani hari, yana gargadin cewa idan aka karya yarjejeniyar tsagaita wuta za su mayar da martani cikin gaggawa da ƙarfi.

    A cewarsa, Iran a shirye take ta kare kanta a kowane lokaci, inda ya jaddada cewa rundunar ƙasar na cikin cikakken shirin tunkarar duk wani hari daga waje.

    Wannan jawabi ya zo ne yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da mataimakin firaministan Qatar kuma ministan tsaro, inda ɓangarorin biyu suka tattauna batutuwan tsaro da kuma yiwuwar ƙara haɗin gwiwar tsaro tsakaninsu.

    Ministan ya kuma nuna damuwa kan yadda wasu ƙasashen waje ke shiga harkokin yankin, yana mai cewa hakan ba ya samar da tsaro sai dai yana ƙara rikici da rashin amincewa tsakanin ƙasashe, yana mai kira da a bar ƙasashen yankin su kula da tsaronsu da kansu.

    Wannan dai na zuwa ne yayin da rikici ya ƙaru tun bayan hare‑haren Amurka da Isra’ila a ranar 28 ga Fabrairu, wanda ya sa Iran ta mayar da martani har da kai farmaki kan wasu wurare a Qatar.

    A yanzu haka, Qatar tare da Pakistan na ƙoƙarin shiga tsakani domin samar da yarjejeniyar zaman lafiya ta dindindin tsakanin Iran da Amurka.

  14. Ba mu tsara wata tattaunawa da Amurka ba a Doha - Iran

    ....

    Asalin hoton, Tasnim news agency

    Iran ta musanta iƙirarin Trump cewa za a fara sabbin tattaunawa da Amurka a Doha, tana mai cewa ba ta tsara wata ganawa ko tattaunawa da Amurka ba a wannan lokaci ba.

    Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta ce wakilan ƙasar da ke tafiya Doha ba don tattaunawa ba ne, sai dai domin bibiyar batun kuɗaɗen ƙasar da aka ƙwace a ƙasashen waje.

    Wannan matsaya na Tehran ya zo ne duk da cewa Trump ya bayyana cewa za a gudanar da ganawa tsakanin wakilan ƙasashen biyu a babban birnin Qatar.

    Sai dai jami’an Iran sun musanta wannan batu, suna jaddada cewa babu wani shiri na ganawa ko tattaunawa da suka shirya yi da Amurka a kwanaki masu zuwa.

    A wani ɓangare, Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya ce kimanin dala biliyan 6 daga cikin biliyan 12 na kuɗaɗen Iran da aka ƙwace za su sake dawowa da su hannun gwamnati nan ba da jimawa ba.

    Ya ce ana ci gaba da bin matakan da suka dace domin ganin an saki kuɗaɗen, wanda ake ganin zai taimaka wajen karfafa tattalin arzikin ƙasar.

    Haka kuma, Iran ta yi martani ga bayanan da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi, inda ta jaddada cewa ita kaɗai ce ke da ikon gudanar harkokin mashigin Hormuz.

  15. An fara zanga-zangar ƙyamar baƙi a Afrika ta Kudu bayan cikar wa'adi

    ...

    An fara zanga‑zangar ƙyamar baƙi a sassa daban‑daban na Afirka ta Kudu, lamarin da ya sa aka jibge jami’an tsaro saboda fargabar rikice‑rikice.

    Shugaba Cyril Ramaphosa ya buƙaci masu zanga‑zangar su guji tashin hankali, yana mai jaddada cewa dole ne a gudanar da zanga‑zanga cikin lumana ba tare da tsoratarwa ba.

    Zanga‑zangar na da alaƙa da wa’adin da wasu ƙungiyoyi suka bai wa baƙin da ba su da takaddar izinin zama cikin ƙasar da su fice.

    Hakan ya sa mutane da dama suka fara tserewa saboda tsoron hare‑hare, yayin da hukumomi suka ce an riga an mayar da sama da mutum 25,000 kasashensu, yawancinsu daga wasu ƙasashen Afirka.

    ...

    A birnin Johannesburg, inda ake gudanar da wasu daga cikin zanga‑zangar, an samu tsaiko a harkokin yau da kullum, inda shaguna da dama suka rufe, kuma aka samu yanayi na tsoro da shiru.

    Dubban baƙi kuma na cigaba da jiran a kwashe su a sansanonin wucin gadi domin tsira da lafiyarsu.

    ....

    A gefe guda, Shugaba Ramaphosa ya tunasar da jama’a cewa baƙin da ke zaune bisa doka na da haƙƙi kamar kowa, yana mai cewa suna taka muhimmiyar rawa wajen gina tattalin arziƙin ƙasar.

    A Durban kuwa, ana rushe sansanonin da ke ɗauke da ‘yan Malawi, yayin da wasu ke bayyana takaicinsu na barin iyalansu da rayuwar da suka fara ginawa sakamakon matsin lamba da matsalar tsaro.

    ...
    ....