Hotunan zanga-zangar Ranar Ma'aikata a fadin duniya

An wallafa

A kowace shekara ana amfani da Ranar Ma'aikata Ta Duniya don yin wasu abubuwa - a wannan shekarar wasu sun yi macin ranar ne a zahiri wasu kuma sun yi a kan intanet.

Ga dai hotunan yadda abin ya kasance.

Protest in Athens
Bayanan hoto, Mambobin Kungiyar Kwadago ta Girka PAME, sun yi zanga-zanga a gaban Majalisar Dokokin kasar a cikin yanayi na yin nesa-nesa da juna da kuma rufe fuskokinsu da takunkumi
A woman hands out red carnations
Bayanan hoto, Gwamnatin Girkar ta roki kungiyoyi su dakatar da maci da kamar mako guda, amma kungiyar kwadago da ke jagorantar lamarin ta GSEE ta yi kira ga a tafi yajin aiki na gama-gari raa Ranar Ma'aikata
Turkish police clash with protesters
Bayanan hoto, A Turkiyya, an kama masu zanga-zanga da yawa wadanda ke yin maci a Dandalin Taksim da ke birnin Istanbul a Ranar Ma'aikata duk da dokar kulle da gwamnati ta sanya
Protest in Berlin
Bayanan hoto, An sanya dokar hana taron fiye da mutum 20 a Jamus, kuma hakan ya sa masu zanga-zangar Ranar Ma'aikata Ta Duniya suka dinga macin cikin tagawar da ba ta fi ta mutum ashirin-ashirin ba, maimakon yadda aka saba yi na mutane da yawa
A dog ine Rome
Bayanan hoto, Mutane sanye da takunkumi suna tattaki a Dandalin Piazza San Giovanni albarkacin Ranar Ma'aikata Ta Duniya a birnin Rome da ke Italiya
Red ribbon
Bayanan hoto, An daura jan kyalle a jikin dirkar fitila a Rome inda titunan da aka saba yin zanga-zangar Ranar Ma'aikata suka kasance fayau ba kowa
Demonstrators practice social distancing
Bayanan hoto, A Thessaloniki na Girka, wata mata tana rike da takarda mai dauke da rubutun da ke cewa: ''Ba mu yarda da yi wa mutane sata don ribar kasa ba''
Protest in Vienna
Bayanan hoto, A birnin Vienna na Austria kuwa, masu zanga-zanga ne suka rike kyallaye suka gudanar da zanga-zanga a fadin birnin
Painted floor to keep people apart
Bayanan hoto, Wasu daga cikin masu zanga-zangar na birnin Vienna kuma sun yi wa titin fenti da jan launi inda suka yi alamar da za su bi wajen yin nesa-nesa da juna. Suna yin macin ne don nuna adawa da tafiyar hawainiyar da gwamnati ke yin kan yaki da yaduwar korona
Riot police in Hong Kong
Bayanan hoto, A Hong Kong kuwa 'yan sandan kwantar da tarzoma ne suka killace wajen da masu zanga-zanga suka so mamayewa
Protest in Span
Bayanan hoto, Mambobin kungiyoyin kwadago a Barcelona da ke Sifaniya sun yi nasu macin a gaban wata cibiyar gaggawa ta lafiya, suna kira da a samar da yanayin aiki mai kyau da kuma kayayyakin kariya

Dukkan hotunan na da hakkin mallaka