Cikin Hotuna: Abin da ya faru a Afirka makon nan

Mutanen Sudan sun kararo cikin babban birnin kasar Khartoum, a cikin jirgin kasa domin murnar yarjejeniyar raba mukamai tsakanin sojoji da farar hula.
Bayanan hoto, Mutanen Sudan sun kararo cikin babban birnin kasar Khartoum, a cikin jirgin kasa domin murnar yarjejeniyar raba mukamai tsakanin sojoji da farar hula.
An wallafa
Dan damben Sudan ta kudu Hal Hal yayin da yake kai naushi ga na kasar Lesotho, Mokhesi Tlholohelo a wasan nahiyar a Morocco.
Bayanan hoto, Dan damben Sudan ta kudu Hal Hal yayin da yake kai naushi ga na kasar Lesotho, Mokhesi Tlholohelo a wasan nahiyar a Morocco
Rawar "Shelil", watau rawar gashi ke nan a wani biki a Eritrea.'Yan matan kabilar Tigre suna tanada gashinsu iya tsawon shkeara domin yin wannan rawar a wurin bikin aure.
Bayanan hoto, Rawar "Shelil", watau rawar gashi kenan a wani biki a Eritrea.'Yan matan kabilar Tigre suna tanadar gashinsu iya tsawon shekara domin yin wannan rawar a wurin bikin aure.
A kasar da ke kusa da su kuma, Ethiopia,wadannan yaran suna halartar wani bikin kwana uku da ake yi mai suna Ashenda.
Bayanan hoto, A kasar da ke kusa da su kuma, Ethiopia,wadannan yaran suna halartar wani bikin kwana uku da ake yi ne mai suna Ashenda.
A ranar Lahadi kuma a Misra, ma'aikata suna kokarin kokarin gyara fadar wani attajiri dan kasar Belgium, Edouard Empain wanda ya yi irin ginin fadojin kasar Cambodia shekara 100 da ta gabata.
Bayanan hoto, A ranar Lahadi kuma a Misra, ma'aikata suna kokarin kokarin gyara fadar wani attajiri dan kasar Belgium mai suna Edouard Empain, wanda ya yi irin ginin fadojin kasar Cambodia shekara 100 da suka gabata.
Nonhlanhla Thole wakiliyar Zambia a wasan mita 200 na gasar Iyo ta duniya a ranar Laraba.
Bayanan hoto, Nonhlanhla Thole kenan wakiliyar Zambia a wasan mita 200 na gasar linkaya ta duniya a ranar Laraba.
A ranar Talata, wasu yara suna nishadi a wani kogi a garin Jufureh.
Bayanan hoto, A ranar Talata, wasu yara suna nishadi a wani kogi a garin Jufureh.
Masu gudun motsa jini suna sassarfa a Kalk Bay harbour wall a birnin Cape Town da ke Afirka ta gudu a ranar Alhamis
Bayanan hoto, Wasu masu gudun motsa jiki suna sassarfa a Kalk Bay harbour wall a birnin Cape Town da ke Afirka ta Kudu a ranar Alhamis.
Wani Filfilo a Cape Town yayin da yake sauka a kan wani fure
Bayanan hoto, Wani Filfilo a Cape Town yayin da yake sauka a kan wani fure

Hotuna daga Reuters da EPA da Getty Images da AFP da kuma BBC