Babu tabbacin Rashford zai ci gaba da zama a Barca, Gardon na son komawa Munich

..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Rashford
Lokacin karatu: Minti 2

Babu tabbacin cewar Barcelona za ta biya Manchester United Euro miliyan 30 (Fam miliyan 21.1) don siyan dan wasan gaban Ingila Marcus Rashford dan ci gaba da zamam a kungiyar a mastyin dan wasanta maimakon na aro. (Marca - in Spanish)

Ɗan wasan Newcastle United da IngilaAnthony Gordon na duba damarmakin da zai iya samu a wannan kaka, yayin da Bayern Munich ke son ɗaukar ɗan wasan.(Telegraph - subscription required)

Sai dai Arsenal ta matsa wajen ganin itama ta ɗauki Gardon ɗin, yayin da ya fi son ya ci gaba da taka leda a Landan kan wani birnin na daban. (Sun)

Manchester City da Bercelona na kan gaba wajen ganin ɗauko ɗan wasan Palmeiras Eduardo Canceicao. (Mail+ - subscription required)

Liverpool na da ƴan wasan 9 da za su bar ƙungiyar a wannan kaka, ciki har da ɗan wasan tsakiyar Argentina Alexis Mac Allister, da ke jan hankali a Turai, yayin da mai tsaron baya na Ingila Joe Gomez, ke ci gaba da kasancewa a komar Crystal Palace, Brighton da AC Milan. (Telegraph - subscription required)

Jurgen Klopp da Mauricio Pochettino na cikin wadan zai iya kasancewa mai horar da ƴan wasan Real Madrid idan suka yanke shawarar sallamar Alvaro Arbeloa. (Mail)

Ɗan wasan baya Matt Targett, da ke taka leda a matsayin ɗan wasan aro a Middlesbrough daga Newcastle, na cikin ƴan wasan da Everton d Leeds ke hari. (Teamtalk)

Tottenham na shirye-shiryen siyar da Conor Gallagher, yayin da ƙungiyoyin da ke gasar Premier ke son ɗauko ɗan wasan. (Football Insider)

Mai tsaron bayan Ingila Levi Colwill, na iya bin bayan takwaransa na Ecuador Moises Caicedo, komawa Chelsea. (Times - subscription required)

Liverpool ta yi wasti da tayin da Al-Hilal da ke Saudiya ta yi wa daraktan wasannin taRichard Hughes. (Talksport)

AC Milan na harin ɗan wasan Serbia Dusan Vlahovic, wanda kwantaraginsa zai ƙare da Juventus a kakar nan. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Marseille ta ƙwallafa ranta kan ɗan wasan Morrocco Adam Aznou, wanda har yanzu bai buga wa Everton ko da wasan ɗaya ba a gasar Premier.(Teamtalk)