Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Su wane ne ke samar wa ƴansiyasa kuɗin yaƙin neman zaɓe a Najeriya?
A daidai lokacin da aka fara yaƙin neman zaɓen na shekarar 2027 a hukumance, hankali ya fara komawa ne kan irin rawar da kowace jam'iyya za ta taka wajen jan hankalin masu kada ƙuri'a.
Sai dai wani bangaren da ba'a cika mayar da hankali ba shi ne hanyoyin da jam’iyyun siyasa da ’yan takararsu ke bi wajen samun kudaden yakin neman zabe da kuma yadda suke bayar da su.
Maganar kuɗin kamfe ta sake tasowa ne bayan Dokar Zaɓe ta 2026 ta ƙara yawan kuɗin da doka ta amince wa ƴan takara su kashe a zaɓe.
Masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa dai suna ganin irin kudaden da ke kashewa a yakin neman zabe na kara bude kofar cin hanci da rashawa da kuma karkatar da dukiyar gwamnati.
Hukumar zaɓe ta ƙasar (INEC) tana da sashen da ke sanya ido kan yadda jam'iyyu da ƴan takara ke kashe kuɗi. Hukumar ta kan buƙaci jam'iyyu su gabatar da bayanan kuɗaɗen da suka shigo da kuma yadda aka kashe su bayan an kammala zaɓe.
Kuɗaɗen da doka ta amince a kashe
A ƙarƙashin Dokar Zaɓe ta 2026, ɗan takarar shugaban ƙasa zai iya kashe har zuwa naira biliyan 10, maimakon naira biliyan 5 da aka kayyade masa a baya. Yayin da kuɗin da ɗan takarar gwamna zai iya kashewa ta karu daga naira biliyan 1 zuwa biliyan 3.
Ga ’yan takarar majalisar dattawa, kudin ya tashi daga naira miliyan 100 zuwa miliyan 500, yayin da ɗan takarar Majalisar Wakilai zai iya kashe har zuwa naira miliyan 250, maimakon naira miliyan 70 da aka tanada a baya.
’Yan takarar majalisar dokokin jiha kuma za su iya kashe naira miliyan 100, maimakon miliyan 30 a baya. Yayin da ’yan takarar shugabancin ƙananan hukumomi da na kansiloli za su iya kashe naira miliyan 60 da miliyan 10 bi da bi.
Sai dai sabbin tsare-tsaren sun bar baya a kura ne, inda aka fara tafka muhawar: Ta yaya ’yan takara za su tara ɗimbin kuɗaɗen da ake buƙata domin fafatawa?
Yadda ake samun kuɗin takara
Wani jigo a jam'iyyar PDP, Umar Ibrahim Tsauri, ya ce matsalar ta daɗe tana wanzuwa a siyasar Najeriya ita ce yadda kuɗi ke taka muhimmiyar rawa tun daga matakin neman takara har zuwa lokacin gudanar da zaɓe.
Ya ce, "da yake Najeriya ƙasa ce da ba a cika amfani da doka sosai ba, shi ya sa ake yawaita irin waɗannan tambayoyi," in ji shi.
Ya ce idan aka dubi yadda tsarin neman takara yake, tun daga sayen fom ne ake fara ganin yadda kuɗi ke rinjayar siyasa.
"Za ka ga ana sayar da fom na takara kan miliyoyin nairori, wani lokaci har naira miliyan 100. Wannan kaɗai ya isa ya nuna cewa ba kowa ne zai iya shiga takara ba," ya bayyana.
Tsauri ya yi zargin cewa idan jam'iyya mai mulki ce, sau da yawa ana amfani da kuɗaɗe ne daga lalitar gwamnati wajen gudanar da harkokin yaƙin neman zaɓe.
"Idan jam'iyya tana mulki a jiha, yawanci kuɗin jihar ne ake amfani da su. Idan kuwa tana mulki a matakin tarayya, ana zargin cewa kuɗin lalitar gwamnatin tarayya ne ake amfani da shi wajen gudanar da yaƙin neman zaɓe," in ji shi.
Ya ƙara da cewa jam'iyyun adawa kuwa galibi suna fama da neman kuɗaɗen gudanar da kamfe ta hanyar gudunmawar mambobi, abokai da masu goyon baya.
Tsauri ya ce duk wanda ya yi iƙirarin cewa da "kuɗin mambobin jam'iyya kaɗai ne ake ɗaukar nauyin zaɓe, magana ce kawai," in ji shi.
Game da zarge-zargen cewa wasu ƴan siyasa ko jam'iyyu na samun kuɗaɗen tallafi daga ƙasashen waje, Tsauri ya ce babu wata hujja tabbatacciya da ke tabbatar da hakan.
"Akwai zargi ana yi, amma babu tabbacin da ke nuna haka. Sai dai idan ka ga irin kuɗin da wasu ke kashewa, za ka fara mamakin inda suka samo su," in ji shi.
Haka kuma Tsauri ya ce saɓanin yadda ake tsammani, yawancin mambobin jam'iyyun siyasa a Najeriya ba sa biyan kuɗaɗen gudunmawar wata-wata yadda ake yi a wasu ƙasashe, ballantana a samu kuɗin shiga.
"Sai lokacin takara idan an buƙaci mutum ya je ya biya wata gudunmawa, sai a ba shi rasit na kuɗin," in ji shi.
A cewarsa, ɗaya daga cikin manyan hanyoyin samun kuɗaɗen shiga ga jam'iyyu shi ne kuɗin sayen fom na takara.
"Lokacin zaɓe idan ya zo, kuɗin fom na kawo wa jam'iyya kuɗaɗe masu yawa. Wasu jam'iyyun suna amfani da kuɗin wajen gudanar da ayyuka daban-daban na jam'iyya," ya ce.
Tsauri ya ce a PDP, musamman a lokacin da jam'iyyar ke da gwamnoni da yawa, ana raba wani ɓangare na kuɗaɗen da aka samu daga sayar da fom ga jihohi da shiyyoyi domin ƙarfafa ayyukan jam'iyya.
"Idan an tara kuɗaɗe, ana ba jihohi da shiyya-shiyya wani kaso. Haka kuma ana ware wani kaso domin tallafa wa ɗan takara, sannan a ajiye sauran don gudanar da harkokin jam'iyya," in ji shi.
'Ba mai iya ɗaukar nauyin zaɓe shi kaɗai'
Tsauri ya jaddada cewa gudanar da yakin neman zabe a Najeriya ya kai matsayin da zai yi wuya ɗan takara guda ya iya ɗaukar nauyin komai daga aljihunsa.
"Ko da mutum yana da kuɗi, zai yi wuya ya iya ɗaukar dukan dawainiyar zaɓe shi kaɗai. Abokai, masu goyon baya da masu ruwa da tsaki kan taimaka, musamman idan sun ga yana da damar nasara," in ji shi.
A cewarsa, babu wanda ya fi son a samu nasara a zaɓe kamar ɗan takara da kansa, don haka shi ne ke kasancewa a gaba wajen neman hanyoyin samun kuɗaɗen gudanar da kamfen.
Sai dai Tsauri ya kuma yi iƙirarin cewa akwai wasu ƙananan jam'iyyu da ba sa shiga zaɓe domin neman nasara kai-tsaye, sai dai domin cin moriyar abin da za su samu a tsarin siyasa.
"Akwai wasu jam'iyyu da kusan ba a san su ba. Suna shiga zaɓe ne kawai domin cin gajiyar wasu damar da tsarin siyasa ke bayarwa. Amma ga manyan jam'iyyu da kuma manyan ƴan takara, manufar ita ce samun nasara a zaɓe," in ji shi.
Ya kammala da cewa har sai an samar da ingantaccen tsarin sa ido da aiwatar da dokokin kuɗaɗen zaɓe, za a ci gaba da samun tambayoyi kan yadda jam'iyyu da 'yan takara ke tara da kuma kashe kuɗaɗensu a Najeriya.
Kuɗin takara
Ɗaya daga cikin muhimman tanade-tanaden dokar zaɓen Najeriya shi ne ƙayyade adadin kuɗin da kowane ɗan takara zai iya kashewa wajen yaƙin neman zaɓe.
A sabuwar dokar zaɓe ta 2026, sashe na 92 ya ƙara adadin kuɗin kamfe da ƴan takara za su iya kashewa, inda aka bayyana cewa an yi hakan ne saboda hauhawar farashin kaya da tsadar gudanar da kamfe idan aka kwatanta da shekarun baya.
Bisa tanadin Sashe na 92 na dokar:
- Ɗan takarar shugaban ƙasa: ba zai kashe fiye da naira biliyan 10 ba.
- Ɗan takarar gwamna: ba zai kashe fiye da naira biliyan 3 ba.
- Ɗan takarar Sanata: ba zai kashe fiye da naira miliyan 500 ba.
- Ɗan takarar Majalisar Wakilai: ba zai kashe fiye da naira miliyan 250 ba.
- Ɗan takarar Majalisar Jiha: ba zai kashe fiye da naira miliyan 100 ba.
Sai dai masana shari'a sun bayyana cewa akwai bambanci tsakanin kuɗin da ɗan takara zai kashe da kuma kuɗin da yake da shi.
Barista Aminu AbdulRasheed, lauya a Najeriya, ya ce doka ba ta ce dole ne ɗan takara ya kashe wannan adadi ba idan ba shi da su, illa dai ta sanya iyakar da ba zai wuce ba.
"Misali, idan ɗan takarar shugaban ƙasa ya kashe naira biliyan huɗu kacal a kamfensa, bai karya doka ba. Amma idan ya kashe fiye da naira biliyan goma, zai iya fuskantar hukuncin da dokar ta tanada idan aka tabbatar da hakan," in ji shi.
Barista ya ce dokar ta ce da zarar an kammala zaɓe ƴan takara za su bayar da bayanin ƙididdigar abin da suka kashe.
Hanyoyin da aka haramta wa ɗantakara ya samu kuɗin kamfe
Duk da cewa dokar Najeriya ta amince ƴan takara su tara kuɗaɗen kamfen daga halastattun hanyoyi, ta kuma haramta wasu hanyoyin tara kuɗi.
Barista Aminu AbdulRasheed ya ce duk wata gudummawa da ta samo asali daga haramtacciyar hanya ko ake zargin tana da alaƙa da cin hanci, almundahana ko wasu laifukan kuɗi, ba ta halatta ɗan takara ya karɓa ba.
"Idan kuɗin da za a ba ɗan takara sun fito ne daga wata haramtacciyar hanya, ko kuma ana zargin sun shafi cin hanci, badaƙala ko wasu laifukan kuɗi, bai kamata ɗan takara ya karɓe su ba," in ji shi.
Ya kuma bayyana cewa dokar zaɓe ta haramta wa jam'iyyun siyasa da ƴan takara karɓar gudummawar kamfen daga ƙasashen waje ko wasu ƙungiyoyi na ƙetare.
Ya ƙara da cewa ba a yarda a yi amfani da kuɗaɗen gwamnati ko dukiyar al'umma wajen gudanar da yaƙin neman zaɓe.
"Ba a yarda a yi amfani da wata hukuma ta gwamnati, ko kuɗaɗen gwamnati, ko wani abu mallakin al'umma domin hidimar siyasa ko yaƙin neman zaɓe ba," in ji Barista AbdulRasheed.