Bikin al'ada a Morocco da na mabiya addinin Kirista cikin hotunan Afrika

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Ƙayatattun hotunan Afirka da na ƴan nahiyar a wasu sassan duniya cikin makon da ya gabata

.
Bayanan hoto, Ranar Litinin yayin da wata matashiya ke wucewa ta gefen zane.
A ranar Laraba ne aka ƙawata wani yanki a birnin Alexandra da ke Afrika ta Kudu da kayan adon da aka samar ta hanyar amfani da shara don tsaftace kogi.
Bayanan hoto, A ranar Laraba ne aka ƙawata wani yanki a birnin Alexandra da ke Afrika ta Kudu da kayan adon da aka samar ta hanyar amfani da shara don tsaftace kogi.
Wasu mutane a Senegal
Bayanan hoto, Ranar Juma'a lokacin shirin taron nuna kayan da aka ƙirƙira ta hanyar amfani da kwali don wayar da kai game da matsalar sauyin yanayi a Senegal.
Ya yin Palm Sunday mabiya addinin Kirista sun taru a cocin Regina Mundi da ke jihar Lagos don gudanar da ibada.
Bayanan hoto, Ya yin Palm Sunday mabiya addinin Kirista sun taru a cocin Regina Mundi da ke jihar Lagos don gudanar da ibada.
A ranar ne kuma dubban mabiya addinin Kirista daga ƙasashen Ethiopia da Lebanon suka gudanar da ranar Palm Sunday.
Bayanan hoto, A ranar ne kuma dubban mabiya addinin Kirista daga ƙasashen Ethiopia da Lebanon suka gudanar da ranar Palm Sunday.
Mabiya Addinin Kirista a Coci
Bayanan hoto, Haka yanayin ya kasance a cocin Legio Maria da ke Nairobi babban birnin ƙasar Kenya.
Mun ga yadda aka haɗa wani tsohon ƙwarangwal a Afirka ta Kudu ranar Talata.
Bayanan hoto, Mun ga yadda aka haɗa wani tsohon ƙwarangwal a Afirka ta Kudu ranar Talata.
Jama'a sun taru a Kudancin Morocco don gudanar da bukin al'adun gargajiya ranar Juma'a.
Bayanan hoto, Jama'a sun taru a Kudancin Morocco don gudanar da bukin al'adun gargajiya ranar Juma'a.
maza sun yi gasar wasan ƙwallon hockey a Morocco
Bayanan hoto, Washegari maza sun yi gasar wasan ƙwallon hockey.
Wasu ƙwararru sun kirƙiri wata mota ta hanyar amfani da tsoffin ƙarafuna a Nairobi.
Bayanan hoto, A ranar ne kuma ƙwararru suka kirƙiri wata mota ta hanyar amfani da tsoffin ƙarafuna a Nairobi.
Ƴan ƙasar Mali da dama sun fusata sakamakon zargin da Algeria ta yi cewar dakarunsu sun kakkaɓo wani jirgi maras matuƙi na Algeria a kusa da iyaka.
Bayanan hoto, Ƴan ƙasar Mali da dama sun fusata sakamakon zargin da Algeria ta yi cewar dakarunsu sun kakkaɓo wani jirgi maras matuƙi na Algeria a kusa da iyaka.
Jama'a sun halarci gangamin da hukumar matasa ta Mali ta shirya a Bamako babban birnin ƙasar ranar Lahadi.
Bayanan hoto, Jama'a sun halarci gangamin da hukumar matasa ta Mali ta shirya a Bamako babban birnin ƙasar ranar Lahadi.
Yadda yaƙin basasa a Sudan ya lalata muhimman kayan tarihi a cibiyar ajiyar kayan tarihi da ke Khartoum.
Bayanan hoto, Yadda yaƙin basasa a Sudan ya lalata muhimman kayan tarihi a cibiyar ajiyar kayan tarihi da ke Khartoum.Birnin ya shekara biyu ƙarƙashin ikon dakarun RSF kafin sojoji sun karɓe ikon birnin a baya-bayan nan.
Sansanin ƴangudun hijira na Zamzam
Bayanan hoto, Sansanin ƴangudun hijira na Zamzam wanda dakarun RSF suka ƙona a baya-bayan nan. Wasu daga cikin waɗanda suka tsere sun faɗi a hanya sakamakon tsananin ƙishirwa da gajiya.