China ta shiga tsaka-maiwuya bayan ɓullo da tsarin taƙaita haihuwa

Hoton wani jariri.

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 6

Miliyoyin al'umma a China na bikin sabuwar shekarar Gargajiya ta Lunar, inda za a yi bukukuwa da abinci, shagulgula da kuma addu'o'i. Sai dai ga waɗanda ba su yi aure ba lokaci ne na raɗaɗi, saboda iyayensu na ware kwanaki don sukar su da yin alawadai da su saboda kasa aure ko kuma haihuwa.

Rashin samun ɗa batu ne da ya daɗe yana jawo cece-kuce a China (da kuma wasu wurare a gabashin Asiya) kuma yanzu lamarin ya tsayawa hukumomi a zuciya.

Batun ya sake tashi a watan da ya gabata, yayin da gwamnati ta fitar da sabbin alkaluma da ke nuna yadda aka samu raguwar haihuwa matuka a ƙasar.

Alkaluman sun nuna cewa an samu haihuwa kashi 5.63 cikin mutum 1,000 wanda ba abu ne da ba a taɓa gani ba tun kafa Jamhuriyar China a 1949 - kuma abu ne da hukumomin ƙasar ba su taɓa tsammani za a samu ba.

Wani karamin yaro yana cin ƴaƴan itace.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Alkaluman haihuwa a China ya yi ƙasa sosai a 2025, duk da kokarin gwamnati na ɓullo da tsarin inganta haihuwa

Hukumar kididdiga ta ƙasar ta fitar da alkaluma a watan Janairu waɗanda suka nuna cewa China ta samu haihuwa jarirai miliyan 7.92 kaɗai a 2025, kuma an fi samun mutuwa kan haihuwa a cikin shekara huɗu a jere, abin da ke nufin cewa yawan al'ummar ƙasar ya ragu da kusan miliyan 3.4

Kwararru a Majalisar Ɗinkin Duniya sun ce al'ummar China za ta ci gaba da raguwa, inda ta yi kiyasin cewa ƙasar za ta rasa sama da rabin al'ummarta a karshen ƙarni.

Sai dai shekaru 20 da suka wuce lamarin ya sha bamban. Hukumomin China sun yi hasashen cewa al'ummar ƙasar za ta ci gaba da ƙaruwa har sai zuwa 2033, inda ƴan ƙasar za su kai biliyan 1.5. Maimakon haka, an kai kololuwar hakan cikin shekara 12 kaɗai - inda aka samu gazawar mutum miliyan 100 kaɗai cikin hasashen.

Shin ta yaya masu tsara yawan jama'ar China suka samu kuskuren yanayin da ƙasar da ta fi yawan jama'a a duniya ke ciki yanzu?

Yin caca kan batun haihuwa

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Yayin da al'ummar China ta doshi biliyan ɗaya a shekarun 1970, gwamnatin ƙasar ta fara nuna damuwa kan irin tasirin da hakan zai yi ga tsarinta na gina tattalin arziki.

A shekara ta 1979, gwamnatin Deng Xiaoping ta ɓullo da tsarin taƙaitawa iyalai haihuwar yaro ɗaya tal.

An assasa hakan a ƙasar baki ɗaya ta hanyar samarwa mutanen da suka yi na'am da tsarin kuɗi da kuma ayyukan yi, samar da ƙwayoyin hana haihuwa da kuma kama waɗanda suka saɓa wa umarni.

An kuma ɓullo da ƙari mataki masu tsauri, ciki har da tilasta zubar da ciki.

Tsarin ya cimma manufarsa - gwamnatin China ta yi kiyasin cewa an hana haihuwa kusan miliyan 400 (duk da cewa an kalubalanci alkaluman) - sai dai hakan ya kuma shafi daidaito tsakanin zuri'a.

Damuwar ta sake komawa kan cewa al'ummar da ta ci gaba da tsufa za ta janyo cikas wajen cigaban tattalin arziki saboda raguwar ma'aikata matasa, ga kuma raguwar masu biyan haraji da masu karɓar fansho.

A tsawon shekaru, masu tsara yawan al'ummar China sun ɗauka cewa raguwar haihuwa na lokaci kaɗan ne kawai, kuma da zarar an ɗage umarnin takaita hakan, ma'aurata za cu ci gaba da samun ƴaƴa.

'Ci gaba da raguwa'

Wani yaro rike da kwallon kwando.

Asalin hoton, Getty Images

China ta kasance tana fuskantar raguwar haihuwa tun da daɗewa, kafin ma a ɓullo da tsarin haihuwar ɗa ɗaya, a cewar Farfesa Kerry Brown, malami birnin Landan.

"Raguwar haihuwa a China ya fara ne haka nan tun farkon shekarun 1970 zuwa sama - an samu kololuwar girman al'umma ne a cikin iyalai a 1950 da kuma 1960," kamar yadda ya faɗa wa BBC.

Ya yi imanin cewa daga shekarun 1980, akwai mutane da yawa da suka yanke shawarar haihuwar yaro ɗaya ko biyu kaɗai saboda matsin tattalin arziki da kuma wasu dalilai, ba wai kawai don hukumomin ƙasar sun ɓullo da tsarin ba.

"Ban tsamman cewa gwamnati ta san wahalar da iyaye ke sha wajen kula da yaransu ba, da kuma irin tunanin da suke yi na kula da su ko kuma a'a.

"Mun ga irin waɗannan sauye-sauye a wasu wurare a duniya, sai dai abin ya faru cikin sauri a China," in ji shi.

Farfesa Brown ya ce gwamnatin China ta lura da batun sauyin zamantakewa da kuma tattalin arziki ne cikin saur, shi ya sa tayi haka.

Rashin daidaiton jinsi

Wani mutum kan bishiya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, China na da miliyoyin maza fiye da mata, abin da ya sa maza ke wahala wajen samun matan aure

Tsarin haihuwar yaro guda, ya kuma janyo cikas a ɓangaren daidaiton jinsi a China.

Iyayen da suka san cewa za su dogara da yaro ɗaya da zai kula da su idan suka tsufa, suna zubar da cikin da aka san cewa mace za a haifa, abin da ya janyo bambanci tsakanin maza da mata.

Wannan ya janyo matsalar yawaitar tuzurai, inda dubun-dubatar maza suka kasa samun matan da za su aura.

Mazan da ba su da digiri na shan wahala, yayin da waɗanda suka fi karatu ke samun damar aure, inda mata da yawa suka fi maza zuwa jami'a.

"Wannan ya jawo yawan tuzurai da suka kasa aure," in ji Farfesa Brown.

A ɗaya gefen, matan da suka yi karatu, na zaɓar yin aure daga baya ko kuma su ki yin auren baƙi daya - ana ƙara samun irin waɗannan mata.

Domin kokarin karfafa musu su yi aure, kafofin yaɗa labaran China sun koma kiransu da "sheng nu" wato waɗanda aka rage.

"Kalma ce mai muni - inda yake kwatanta hakan da matan da ake tsangwama saboda shekarunsu da kuma suka kasa yin aure tare da mayar da hankali ga karatu maimakon yin aure," a cewar Farfesa Brown.

Zuwa 2023, yawan matan da suka kai shekara 25 zuwa 29 waɗanda ba su yi aure ba ya kai kashi 43, inda hakan ya rage buƙatar son haihuwa.

Tallafin kuɗi ga jarirai

Beijing ta ɓullo da tsare-tsare da dama don daƙile raguwar haihuwa, ciki har da tallafin kuɗi na yuan 3,600 (wato dala 500) ga duk yaron da ke ƙasa da shekara uku.

Wasu matakan sun haifar da cece-kuce. Misali, harajin kashi 13 na bana kan ƙwayoyin hana ɗaukar ciki - ciki har da kwaroron roba, maganin hana haihuwa da na'urori - sun haifar da damuwa game da ɗaukar ciki da kuma cutar HIV.

Sai dai tallafin ya ƙasa sauya ɗabi'ar mutane, yayin da matasan China suke bayyana cewa tsadar renon yara ne dalilin da ya sa ba su haihu ba.

Likita riƙe da jariri.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Beijing ta ɓullo da matakai da dama do ƙarfafawa iyaye

Me hakan ke nufi ga China - da kuma duniya baki ɗaya?

China ce ƙasar da aka fi samun raguwar haihuwa matuka a duniya , inda kowace mace ke haihuwar yaro ɗaya tal, kuma hakan ya yi kasa da adadin 2.1 wanda aka kayyade na girman al'umma.

Raguwar al'umma na da tasiri ga zamantakewa da kuma tattalin arziki ga ƙasa ta biyu mafi girman tattalin arziki a duniya, abin da rage yawan ma'aikata da raunana buƙatar masu saye.

Raguwar al'ummar China zai janyo tasiri mara kyau ga tattalin arziki a duniya, inda zai jawo ƙaruwar farashin kayayyaki a faɗin duniya.

Wasu ƙasashe a yankin su ma ba su da yawan haihuwa - amma suna da tattalin arziki mai kyau, abin da ke bai wa gwamnatoci damar daidaiton al'umma da ke tsufa.

Babban haɗari a China shi ne al'ummar na tsufa kafin a samu arzikin.

"A ɗaukacin yankin, al'umma na raguwa kuma tana tsufa. Abin ba shi da kyawu a wasu wurare kamar Japan da Taiwan, amma sauyi da ke China ya fi zama babba," a cewar Farfesa Brown.

"China ba ta kai matakin daƙile tsufan al'ummar ba ta hanyar samar da ababen more rayuwa ga kowa da kuma kula da tsofaffi," kamar yadda ya yi gargaɗi.

Idan, kamar yadda cibiyar nazarin ilimin zamantakewar al'umma ta China ta yi imani, masu karɓar fansho na ƙaruwa, kuma lokaci ya fara kurewa ƙasar wajen samar da isassun kudade don kula da al'ummar da ta fara tsufa.

Duk da haka Farfesa Brown yana kyautata zaton cewa China za ta warware matsalar yawan jama'arta cikin lokaci.

"Wataƙila za su yi ƙoƙari su yi amfani da fasaha kuma suna da kowane irin tsari na sauƙaƙe waɗannan abubuwa," in ji shi.