Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Su wane ne ƴankwallon da suka fi arziki a duniya?
Kimanin shekara 10 ke nan da fitaccen dankwallon Portugal da Al Nassr ta Saudiyya Cristiano Ronaldo ya zama dankwallo na farko da ya kai biloniya.
A lokacin da ya bar Real Madrid ya koma Juventus ne arzikinsa ya karu matuka.
Yanzu haka Ronaldo yana samun dala miliyan 300 ne duk shekara, sai Messi da ke biye masa.
Karim Benzema ne na uku da ke samun dala miliyan 104 a shekara. Kylian Mbappé ne na hudu, inda yake samun dala miliyan a shekara. Wannan ne tarin kudin da suke samu a shekara daga albashi da tallace-tallace da sauran su.
Amma shin wane ne daga cikinsu ya fi tarin arziki??
1. Christian Ronaldo
Za a iya cewa Ronaldo ya cimma muhimman abubuwan da ake bukata a harkar tamaula. Duk da yanzu haka ya kai shekara 41, yana taka leda ne tamkar wani matashi da yanzu yake farawa.
Har yanzu yakan yi kuka idan aka doke kungiyarsa. Ko kadan bai yarda da rashin nasara a wasa.
Abu daya da rage wa Cristiano shi ne lashe gasar cin kofin duniya, kuma zai iya samun nasarar lashewa a gasar ta gaba.
Ya taso ne cikin wani irin hali, inda mahaifinsa ya kasance talaka.
Ronaldo na cikin 'yan kwallon kafa da suka kai arziki biloniya.
Ya saya kashi 25 na kungiyar UD Almeria ta Spain.
Ya bunkasa arzikinsa ne ta hanyar kasuwancin gidaje da otel-otel na alfarma, sannan yana da gidan ajiye tarihi a birnin Lisbon na Portugal da ke yawan samun masu ziyar.
Yana jirgin hawa na alfarma da motocin alfarma. Tun daga komawarsa Al Nassr zuwa yanzu ya samu kusan fan miliyan 200, bayan kudaden day ake samu na tallace-tallace.
Mujallar Fobes ta ruwaito cewa arzikinsa ya kai dala biliyan 1.4 .
2- David Beckham
Tsohon dan wasan Ingila da Manchester United, David Beckham ya zama dankwallon farko dan Birtaniya da ya kai matakin biloniya.
Mujallar Sunday Times Rich ta ce Beckham yana da arziki da ya kai fam biliyan 1.185.
Shi ne ya mallaki kungiyar kwallon kafa ta Inter Miami da ke Amurkaz wadda ta kai darajar fam biliyan 1.45.
Ya kuma yi aiki da kamfanoni manya irin su Adidas da Hugo Boss, sannan matarsa ta taimaka wajen arzikin gidan ta hanyar tallace-tallace da take yi.
3. Lionel Messi
Wasu dai na cewa babu dankwallon kafa kamar shi. Ya lashe kusan komai da ake bukatar lashewa a harkar tamaula, ciki har da gasar cin kofin duniya.
Ya buga wasa a kungiyoyin Barcelona da PSG, sannan yanzu yana Inter Miami.
A bana kawai ya samu kusan dala miliyan 28.3, sama da abin da sauran kungiyoyin gasar Amurka suka samu jimilla.
Shi ma ya mallaki jirgin hawa da motocin hawa na alfarma.
Yana samun karin kudaden daga tallace-tallace daga kamfanoni da dama.
Arzikinsa ya haura dala biliyan 1.
4- Neymar
Neymar na cikin 'yan kwallon kafa matasa da suka zama miloniya cikin kankanin lokaci.
Bayan komawa PSG ne arzikinsa ya karu, sannan daga Faransa ya shiga kwantiragin shekara biyu da Al Hilal kan kudi fam miliyan 400 a shekara.
Duk da cewa yana yawan fama da raunuka, Neymar yana samun makudan kudade daga albashi da tallace-tallace.
Sannan yana kasuwancin gidaje da sauran kasuwancin.
Mujallar Fobes ta ruwaito cewa arzikinsa ya haura dala miliyan 350.
5- Kylian Mbappe
An haifi Kylian Mbappé ne a gidan kwallon kafa. Mahaifinsa dan asalin kasar Kamaru ne, sannan mahaifiyarsa 'yar Algeria ce.
Kylian Mbappé ya fara samun albashi mai tsoka ne tun yana da shekara 17 lokacin da ya koma PSG daga AS Monaco a kan kudi fam miliyan 180.
Haka kuma shi ma yana kasuwanci, sannan yana tallace-tallace da sauran su.
Benzema
A lokacin da Karim Benzema yake taka leda a Real Madrid, a zamanin ne akwai Cristiano Ronaldo da Bale. Amma duk da haka ya nuna bajintarsa.
Yanzu haka yana samun makudan kudade a kungiyar Al Hilal ta Saudiyya, sannan yana tallace-tallace.
Yanzu arzikinsa ya kai dala miliyan 220.
Arzikin Zlatan Ibrahimovic ya kai dala miliyan 190 million, na Wayne Rooney ya kai dala miliyan 170 sai Erling Haaland da ya ke da arzikin dala miliyan 100.
Yanzu haka Mohamed Salah na cikin 'yan kwallon kafa da suka fi samun albashi mai tsoka a duniya, kuma arzikinsa ya kai dala miliyan 90.