Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sansanonin sojin Amurka 20 da Iran ta lalata
- Marubuci, Merlyn Thomas
- Marubuci, Alex Murray
- Marubuci, Matt Murphy
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Verify
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
Iran ta yi ɓarna a cibiyoyin sojin Amurka 20 tun fara yaƙi tsakaninsu, kamar yadda hotuna da bidiyon tauraron ɗan'adam da BBC Verify ta tantance suka nuna, kuma an fahimci cewa hare-haren na da ƙarin girma a kan yadda aka nuna a zahiri.
Iran ta riƙa kai wa muhimman cibiyoyi farmaki a faɗin Gabas ta Tsakiya guda takwas tun a ƙarshen watan Fabrairu, inda ta haddasa ɓarnar miliyoyin daloli ga na'urorin tsaron samaniya na zamani da jirgin zuba wa jiragen yaƙi mai a sama, da na'urorin hango jirage na rada.
Tehran ta riƙa kai hare-hare ne kan sansanonin sojin Amurka da kuma cibiyoyin soja na haɗin gwiwa don mai da martani ga hare-haren Amurka da Isra'ila a faɗin Iran da Lebanon cikin wata ukun da suka wuce. Ma'aikatar tsaron Amurka, Pentagon ta ce ta kai hari kan wurare fiye da 13,000 a Iran tun fara Aikin sojin da suke kira 'Epic Fury'.
Amurka ta nemi taƙaita ganin hotunan tauraron ɗan'adam na tantance ɓarnar yaƙin Iran inda ta roƙi Planet, wani babban kamfanin sadarwar tauraron ɗan'adam a kan ya sa takunkumin "sai-baba-ta-gani" kan sabbin hotunan Iran da na mafi yawan Gabas ta Tsakiya.
Kamfanin ya kafa hujjar ɗaukar matakin, yana cewa so yake yi, ya tabbatar "abokan gaba" ba su yi amfani da hotunansa "wajen kai hari ga dakarun Nato da sojojin ƙawance da kuma fararen hula" ba.
Sashen BBC Verify ya yi amfani da hotunan tauraron ɗan'adam daga sauran kamfanonin sadarwar tauraron ɗan'adam daga sauran ƙasashen duniya da kuma tsofaffin hotuna daga kamfanin Planet wajen bin diddigin ɓarnar da hare-haren Iran suka haddasa. Sansanonin na cikin ƙasashen Saudiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Qatar da Kuwait da Iraqi da Jordan da Bahrain da kuma Oman.
Haƙiƙanin adadin na iya fin haka, amma wasu masharhanta sun bayyana adadin sansanonin da Iran ta kai wa hari da yawan 28.
Mojtaba Khamenei, shugaban addini na Iran, ya yi ƙoƙarin fito da nasarorin sojojinsa wajen kai hare-hare a kan sansanonin Amurka. A wata sanarwarsa ranar Talata ya yi iƙirarin cewa Gabas ta Tsakiya ba za ta sake zama "wuri mai aminci" ga sansanonin Amurka ba.
Yayin da Fadar Shugaban Amurka ta nanata iƙirarin cewa ta kusa shafe sojojin Iran daga doron ƙasa, masharhanta sun ce ɓarnar da aka gani a sansanonin Amurka na nuna cewa hare-haren ramuwar gayya na Iran sun yi matuƙar tasiri kuma girmansu ya fi yadda jami'an Amurka suka amsa cewa an yi tun da farko.
Wani jami'in tsaron Amurka ya ƙi cewa uffan ga abubuwan da BBC Verify ta bankaɗo, inda ya kafa hujja da "dalilan aikace-aikacen tsaro".
Lalata na'urar kakkaɓo makamai ta THAAD
Daga cikin na'urori masu matuƙar muhimmanci da aka lalata akwai na'urorin zamani masu kakkaɓo makamai masu linzami guda uku a Al Ruwais da sansanin sojojin sama na Al Sader a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da sansanin sojin sama na Muwaffaq da ke Jordan.
An san Amurka na amfani da na'urorin kakkaɓo makamai masu linzami guda takwas ne kawai waɗanda ake kira THAAD a taƙaice. An ƙera na'urorin da aka kai sansanonin soji daban-daban a faɗin duniya a kan kuɗi kimanin dala biliyan ɗaya. Duk na'ura ɗaya tana buƙatar dakaru kimanin 100 domin sarrafa ta, sannan tana harba makamin kakkaɓo makami mai linzami duk guda ɗaya a kan kimanin dala miliyan 12.7.
Tsohon kwamandan rundunar tsaron Ireland, Vice-Admiral Mark Mellett, ya faɗa wa BBC Verify cewa na'urorin suna cikin wani ruhin harkokin tsaron yankin mai "matuƙar sarƙaƙiya" waɗanda ba za a iya "maye gurbinsu cikin sauri da sauƙi" ba.
Hare-haren Iran sun kuma yi matuƙar lalata jirgin zuba wa jiragen yaƙi mai a sama da bin diddigin abokan yaƙi a Sansanin sojin sama na Yarima Sultan a ƙasar Saudiyya, nazarin ƙwararru a kan hotunan tauraron ɗan'adam ya nuna, ga kuma lalataccen jirgin da hayaƙi daga ramukan da makamai suka yi ƙiri-ƙiri ana iya gani.
Jirgi guda ɗaya da wani mai sharhi daga MAIAR ya tantance shi ne jirgin sintirin bin diddigin abokan yaƙi ƙirar E-3. Kafofin labaran Amurka sun ba da rahoton cewa yana kai wa fiye da dala miliyan 700 kafin a maye gurbinsa.
A can wani gefen kuma, hare-haren Iran sun faɗa kan Sansanin sojin sama na Ali Al Salem da Sansanin Arifjan na Kuwait. masharhanta a MAIAR sun tantance rumbun ajiyar mai na ƙarƙashin ƙasa da aka lalata, rumfunan ajiye jiragen sama da wurin kwanan sojoji a hotunan tauraron ɗan'adam na sansanin, wanda aka kai masa hari a karo da dama lokacin da ake yaƙin.
Haka kuma a Sansanin Arifjan kamfanin ayyukan leƙen asirin tsaro mai suna Janes ya tantance gagarumar ɓarna a na'urorin sadarwar tauraron ɗan'adam.
Sansanin sojin sama na Ali Al Salem, Kuwait
Girman ɓarnar da aka yi wa cibiyoyin Amurka na da wahalar kimantawa, amma wani ƙiyasi a watan Mayu daga ma'aikatar tsaro ta Pentagon ya haɗa jimillar lissafin a kan dala biliyan 29 - inda mafi yawan kuɗin mai yiwuwa aka kashe su wajen "gyara ko maye gurbin na'urorin" da aka lalata a yaƙin.
'Yan jam'iyyar Dimokrat sun ce wannan mai yiwuwa bai kai haƙiƙanin kuɗin da aka kashen ba.
Rahoton ya kuma gano cewa aƙalla jiragen sama 42 ciki har da jiragen yaƙi ƙirar F-15 da F35 da jirage marasa matuƙi ƙirar MQ-9 Reaper da wani ƙaramin jirgin kai hari ƙirar A-10, ko dai an lalata su ko kuma an yi musu illa tun cikin watan Fabrairu.
Idan aka kwatanta da na'urorin yaƙi masu tsada da sojojin Amurka ke amfani da su. An ba da rahoton cewa Iran na amfani da jirage marasa matuƙi masu arha da sauƙin maye gurbi wajen kai hare-hare kan wurare a faɗin Gabas ta Tsakiya.
Ƙwararrun da suka yi magana da Sashen BBC Verify sun ce dabarun yaƙin da Iran ta ɓullo da su a tsawon lokacin yaƙi, ta hanyar canzawa daga fantsama ruwan makamai masu linzami da ke faɗa wa birane da sansanonin soji a faɗin Gabas ta Tsakiya, zuwa hare-hare masu faɗa wa daidai inda aka nufa.
"Luguden makaman da [Iran] ta fara yi, ta tsara su ne a kan yawa—ta shirya su a kan rubdugu don kanainaye na'urorin kakkaɓo makamai masu linzami da na tsaron samaniya ta hanyar zubo su rututu da yawa," cewar Dr Kelly Grieco, wata mai sharhi a cibiyar masu zurfin nazari ta Stimson Centre da ke Amurka.
"Cikin 'yan kwanaki, amma, sai Iran ta sauya dabara zuwa luguden makamai ƙanana da suka fi faɗa wa daidai kan inda aka harba su, inda suke tattalin sauran makamai masu linzami da jirage marasa matuƙi don kai wa wasu wurare masu muhimmanci hari da karkata luguden wuta inda hatta kuskurewar hari da kaɗan, na iya haddasa gagarumar ɓarna."
Wani mai sharhi a MAIAR ya faɗa wa Sashen BBC Verify cewa dakarun sojin Amurka "ga alama zuciyarsu ta karɓi laifi na gagarumin sakaci a farkon yaƙin" ta hanyar gaza kwashe jiragen saman da hare-haren jirage marasa matuƙi da makamai masu linzamin Iran za su iya faɗawa yayin da Tehran ke ɓullo da sabbin dabaru.
Sun ce kamar a abin da ya faru a sansanin sojin sama na Yarima Sultan an kai hari cibiyar kafin kuma a sake kai harin da ya lalata jirgin saman.
Jagoran Addinin Iran Mojtaba Khamenei ya lashi takobin cewa "ƙasashe da sassan yankin sun daina zama garkuwa ga sansanonin sojin Amurka," ya kuma ce: "Amurka ba za ta sake samun wurin kwanciyar hankali a yankin ba (har) tana yin jamhuru da kafa sansanonin sojoji, sannan kullum za ta yi ta ƙara samun koma-baya daga tsohon matsayin da take kai."
Kalamansa na zuwa ne kwanaki ƙalilan kafin tsagaita wutar Amurka da Iran ta sake lalacewa. A ranar Alhamis, rundunar juyin juya halin Musulunci ta Iran ta ce ta kai wani hari kan sansanin Amurka a yankin, bayan sabbin hare-haren da Amurka ta kai kudancin Iran.
Dr Grieco ta yi gargaɗin cewa idan yarjejeniyar tsagaita wutar Amurka da Iran mai tangal-tangal ta ruguje kuma yaƙi ya dawo ɗanye, ɓarnar da aka riga aka yi wa sansanonin sojin Amurka yanzu na nuna cewa cibiyoyin da ke faɗin yankin Gulf na iya kasancewa cike da rauni.
"Yaƙin da ake yi yanzu ya lamushe rumbunan makaman tsaron Amurka da na ƙawayenta masu yawan gaske," in ji ta.
"Babu hanyar maye gurbin makaman cikin sauri, abin da ke nufin duk wani sabon hari daga Iran zai gamu da ɗan taƙi ne kawai na makaman kakkaɓo hare-hare da ake da su lokacin da yaƙin ya fara."