Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Liverpool na son maye gurbin Salah da Diomande, Arsenal na son Alvarez
Tottenham ta sake nuna sha'awarta a kan cinikin dan wasan gaba na gefe na Manchester United Savinho, dan Brazil mai shekara 22, a kan fam miliyan 60. (Mail), external
Liverpool ta fi son maye gurbin Mohamed Salah, da matashin dan wasan RB Leipzig, Yan Diomande, mai shekara 19, dan Ivory Coast, wanda kwantiraginsa ya tanadi damar sayar da shi a kan fam miliyan 86.
Haka kuma daga cikin zabin da Liverpool din ke dubawa akwai dan wasan Newcastle da Ingila Anthony Gordon, mai shekara 25, da kuma dan gaban Paris St-Germain da Faransa Bradley Barcola, mai shekara 23. (Telegraph)
Sai dai kuma suma zakarun gasar Jamus - Bundesliga - Bayern Munich suna son Gordon din na Newcastle, kuma Bayern za ta iya hadawa da mai tsaron ragar Jamus Alexander Nubel mai shekara 29, ta bayar a cinikin na Gordon. (Bild)
Barcelona za ta yi sabuwar tattaunawa da Manchester United kafin wasan Kofin Duniya, domin kammala cinikin Marcus Rashford, inda kungiyar ta Sifaniya tauni ta kammala yarjejeniya tsakaninta da dan gaban na Ingila mai shekara 28 (Talksport)
Dan wasan tsakiya na Chelsea da Argentina Enzo Fernandez, mai shekara 25, ya zama wanda Manchester City ta fi son saye a kasuwar bazara. (Fichajes)
Roma na sha'awar sayen dan wasan gaba na Marseille Mason Greenwood, mai shekara 24, da Joshua Zirkzee na Manchester United, dan Netherlands mai shekara 25, da kuma, Crysencio Summerville na West Ham, mai shekara 24 shi ma dan Netherlands, a shirin da kungiyar ta Italiya ke yi na tunkarar gasar Zakarun Turai mai zuwa.(La Gazzetta dello Sport )
Julian Alvarez na son barin Atletico Madrid, kuma ana ganin Arsenal, za ta dage wajen ganin ta dauki dan wasan na gaba na Argentina mai shekara 26. (Teamtalk)
Yayin da Aston Villa ke shirin tunkarar gasar Zakarun Turai ta kaka mai zuwa, tana sa ran sayen dan wasan gaba na gefe na Newcastle kuma dan Ingila Harvey Barnes, mai shekara 28. (Mail)
Juventus na dab da cimma yarjejeniya a cinikin mai tsaron ragar Liverpool da Brazil Alisson, wanda ke da ragowar sama da wata 12 a kwantiraginsa da Liverpool. (Goal Italia)
Liverpool ta shiga gogayyar sayen matashin danwasan tsakiya na Jamus Kennet Eichhorn, mai shekara 16, daga Hertha Berlin. (Sky Germany)
Bernardo Silva ya yi tattaunawa mai armashi da Atletico Madrid a yunkurin da kungiyar ta Sifaniya ke yi na yi wa Juventus shigar sauri a kan danwasan na tsakiya na Manchester City da Portugal, mai shekara 31, wanda zai tafi a matsayin wanda babu wani kwantiragi a kansa. (Teamtalk)
Masu horad da 'yan wasa, Scott Parker, mai shekara 45, wanda a kwanan nan ya bar Burnley, da kuma na Strasbourg Gary O'Neil, mai shekara 43, dukkansu 'yan Ingila, na daga cikin wadanda West Ham, ke so idan ta rabu da kociyanta Nuno Espirito Santo, dan Portugal mai shekara 52, a bazaran nan. (Guardian)
AC Milan ta tuntubi wakilan kociyan Bournemouth Andoni Iraola, dan Sifaniya mai shekara 43, bayan da kungiyar ta Italiya ta kori kociyanta Massimiliano Allegri mai shekara 58. (Sky Sports).