Za mu gudanar da zaɓukan fitar da gwani na 'yan takara kusan 300 — PRP

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Jam'iyyar PRP a Najeriya, ta ce ta kammala dukkan shirye-shirye domin gudanar da zaɓukan fitar da gwani tsakanin mutanen da suka nuna sha'awar yin takara a zaɓen 2027.

Shugaban jam'iyyar na ƙasa, Dr Hakeem Baba Ahmed, ya shaida wa BBC cewa, sun ɗauki lokaci domin cika dukkan sharuɗan doka kafin tsarin zaɓukan fitar da gwanin, wanda ya ce za a gudanar a faɗin Najeriya a ranar Litinin, 25 ga watan Mayun 2026.

Ya ce: "Mun ɗauki lokacin da doka ta bayar inda muka nemo mutanen da suka cancanta su tsaya wa jam'iyyarmu ta PRP takara a matakai daban-daban."

" A yanzu za mu yi zaɓen fitar da gwani na 'yan takara kusan 300 a duk faɗin Najeriya, kuma su 'yan takarar jam'iyyarmu ne suka zaɓi hanyar da suke gani za a bi a yayin zaɓen." In ji shi.

Ya ce: " Na farko inda duk babu 'yan takara da ya wuce mutum guda, to babu jayayya a wannan mazaɓa jaddada ɗan takara kawai za a yi.

Amma idan ya kasance akwai mutum biyu ko uku a mazaɓa da suke neman takara, to a nan ne aka ce za a zauna a gani ko za a yi maslaha idan kuma aka gaza samun maslaha to sai yi zaɓen ma'ana 'yar tinke."

Dr Hakeem Baba Ahmed, ya ce, " To Allah Ya taimake mu ma ba mu samu inda aka gaza samun maslaha ba a tsakanin 'yan takarar, sai a matakin shugaban ƙasa, domin a nan an samu rashin jituwa don ba a samu maslaha ba."

" Mutum biyar ne suka nemi tsayawa takarar shugaban ƙasa a PRP, to amma daga baya mun ta ce sai muka cire mutum biyu muka bar uku, saboda waɗancan biyun ba su cancanta ba, su ukun da muka tsayar dukkansu daga kudancin Najeriya suka fito. Daya daga jihar Abia, sai ɗaya daga jihar Edo da kuma gudan daga jihar Cross Rivers." Inji shi.

Ya ce: "Ba mu samu mutum ko ɗaya daga arewacin Najeriya da ya zo ya ce yana son tsayawa takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar PRP fa."

"Mun ji daɗi ma da babu wanda ya fito daga arewa yake neman takarar shugaban ƙasa a jam'iyyarmu domin dama ana ta raɗe-raɗin cewa jam'iyyarmu ta arewa ce, to ga shi dai yanzu 'yar manuniya ta nuna." In ji shi.

Jam'iyyu da dama sun gudanar da zubukansu na fitar da 'yan takara, inda a wasu jihohin jam'iyyun sun bi tsarin maslaha kuma tuni suka tabbatar da ƴantakarar.

Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, ‎na daga cikin jam'iyyun da suka bi tsarin maslaha, to amma akwai rahotanni da ke cewa tsarin maslahar da jam'iyyar ta ɗauka wajen fitar da ƴan takarar majalisar dattawa zai iya yi mata lahani saboda yadda ake ci gaba da samun ƙorafi a wurare da dama.

Sai dai bayanai na cewa jam'iyyar na cewa wannan tsari shi ne take ganin hanyar da za ta rage mata ruɗani da rigingimu.