Fitattun mata 5 da ke takarar gwamna a Najeriya a 2027

Bayanan bidiyo, Fitattun mata 5 da ke takarar gwamna a Najeriya a 2027
Fitattun mata 5 da ke takarar gwamna a Najeriya a 2027
An wallafa

Batun ƙarancin wakilcin mata a siyasar Najeriya ya kasance abin tattaunawa tsawon lokaci, inda masu rajin kare haƙƙin mata ke kiran a ba su damar shiga harkokin mulki da siyasa yadda ya kamata.

A cewarsu, samun ƙarin mata a manyan muƙaman siyasa zai taimaka wajen samar da daidaito da kuma faɗaɗa wakilcin al'umma.