Gwamnoni da wasu sanatocin da suka samu takarar majalisar dattawa

..

Asalin hoton, BBC COLLAGE

Bayanan hoto, Gwamnoni 7 masu ci sun samu kujerun ƴan majalisar dattawan Najeriya
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Jam'iyyar APC mai mulki ta kammala zaɓen fidda gwani na ƴan majalisar dattawa da za su fafata a babban zaɓen kasar na 2027.

Kuma kamar yadda aka gudanar da na majalisar wakilai, shi ma na majalisar dattawa ya zo da mamaki kasancewar wasu manyan ƴan majalisar dattawan ba su kai bantansu ba kasancewar gwamnoni masu ci da suka kammala wa'adinsu biyu sun maye gurbinsu.

BBC ta tattaro sunayen da suka fi yin fice da suka tsallake da wadanda ba su kai ga gaci ba, kamar haka:

Gwamnoni masu ci da suka samu kujerar sanata

  • Dapo Abiodun: Gwamnan jihar Ogun
  • Hope Uzodinma: Gwamnan jihar Imo
  • Ahmadu Fintiri: Gwamnan jihar Adamawa
  • Abdullahi Sule: Gwamnan jihar Nasarawa
  • AbdulRahman AbdulRazaq: Gwamnan jihar Kwara
  • Muhammad Inuwa Yahaya: Gwamnan jihar Gombe
  • Mai Mala Buni: Gwamnan jihar Yobe .

Sanatoci masu ci da tsoffin gwamnoni

Wasu fuskokin da suka samu takara

Asalin hoton, Senator Prince Ned Nwoko, Dr. Ifeanyi Arthur Okowa, Prince Dr. Dapo Abiodun - MFR, Senator Michael Opeyemi Bamidele, Senator Godswill Akpabio/Facebook

  • Godswill Akpabio: Shugaban majalisar dattawan Najeriya mai ci.
  • Barau Jibrin: Mataimakin shugaban majalisar dattawa.
  • Ahmed Lawan: Tsohon shugaban majalisar dattawa.
  • Aliyu Wamakko: Tsohon gwamnan jiahr Sokoto
  • Ibrahim Ɗan Ƙwambo: Tsohon gwamnan jihar Gombe.
  • Simon Lalong: Tsohon gwamnan jihar Plateau
  • Malam Ibrahim Shekarau: Tsohon gwamnan jihar Kano
  • Sanata Kawu Sumaila
  • Ifeanyi Okowa: Tsohon mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa a 2023 a PDP
  • Yahaya Bello: Tsohon gwamnan jihar Kogi
  • Shehu Sani: Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya.
  • Philip Aduda - Tsohon sanatan birnin tarayya, Abuja.
  • Opeyemi Bamidele: Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa
  • Orji Uzor Kalu: Tsohon gwamnan jihar ABia
  • Sanata Adams Oshiomhole: Tsohon gwamnan jihar Edo.
  • Sanata Ali Ndume: Tsohon Shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa
  • Ben Bruce Murray: Sanata mai wakiltar jihar Edo.

Jerin sunayen waɗanda ba su yi nasara ba

..

Asalin hoton, Ovie Omo-Agege/Facebook

Bayanan hoto, Sanata Omo Agege lokacin da magoya baya suka zagaye shi a ranar Asabar 16 ga watan Mayun 2026.

Yawancin dai waɗanda suka rasa takarar sun samu tarnaƙi ne daga gwamnonin jihohinsu masu ci:

  • Rochas Okorocha: Tsohon gwamnan jihar Imo
  • Sanata Ɗanjuma Goje: Tsohon gwamnan jihar Gombe
  • Gbenga Daniel: Sanata daga jihar Ogun
  • Ovie Omo-Agege: Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa.

Zaɓen sanatoci a Zamfara

A jihar Zamfara kuwa a ranar Talatar nan ne ake sa-ran za a gudanar da zaɓen fitar da gwanin na sanatoci, to sai dai tuni wasu suka yi fatali da tsarin da za a fitar da 'yan takarar.

To amma Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura ya ce sun yi amfani da tsarin da APC ta bayar ne na yin maslaha amma ba kakaba 'yan takara suka yi ba.

‎Rahotanni na cewa tsarin maslaha da jam'iyyar APC ta ɗauka wajen fitar da ƴan takarar sanatan zai iya yi mata lahani saboda yadda ake ci gaba da samun korafi a wurare da dama, to sai dai bayanai na cewa jam'iyyar na cewa wannan tsari shi ne take ganin hanyar da zai rage mata ruɗani da rigingimu.