Illoli 7 da zafin rana ke yi wa ƙananan yara da yadda za a kauce musu

Lokacin karatu: Minti 4

A yayin da zafin rana ke ƙaruwa a sassa daban-daban na Najeriya, masana kiwon lafiya na gargadin cewa yara, musamman jarirai, na cikin rukunin da suka fi fuskantar barazana.

Sauyin yanayi da tsananin zafi na iya janyo matsaloli iri-iri ga lafiyar yara, daga rashin ruwa a jiki zuwa cututtukan fata da kuma matsalolin numfashi.

Wannan ya sa ake ƙara kira ga iyaye mata su ɗauki matakan kariya domin tabbatar da lafiyar ƴaƴansu a wannan lokaci.

Yara ƙanana ba su da cikakken ƙarfin jure zafi kamar manya.

Jikinsu ba ya iya daidaita zafin jiki yadda ya kamata, lamarin da ke sa su cikin saurin kamuwa da matsalolin da ke tattare da zafi.

Dr. Amina Yusuf, likitar yara a Najeriya, ta ce ɗaya daga cikin manyan haɗurran da ke tattare da zafi shi ne rashin ruwa a jiki.

Abubuwan da tsananin zafi ke haddasa wa yara

A hirarta da BBC, Dr Amina ta bayyana cewa tsananin zafi na iya janyo matsaloli masu yawa ga yara, musamman jarirai da ƙananan yara da jikinsu bai kai ga daidaita zafi yadda ya kamata ba.

Ga wasu daga cikin muhimman abubuwan da zafi ke haddasawa, kamar yadda likitar yaran ta bayyana.

Rashin ruwa a jiki

Likitar ta ce wannan shi ne babban haɗari da ke tattare da zafi.

Yana faruwa ne idan jiki ya rasa ruwa fiye da yadda jiki ke buƙata.

"Alamomi wannan sun haɗa da bushewar baki da rashin fitsari akai-akai, da kasala'', in ji ta.

Ta ci gaba da cewa ''idan ba a kula da shi da wuri ba, yana iya zama barazana ga rayuwa''.

Zazzaɓi mai tsanani

Zafi na iya haddasa tashin zafin jiki, wanda ke sa yaro ya ji zafi a jikinsa sosai da ka iya sa ya zama mai kuka, ko ya kasa sukuni.

''Wannan na iya ƙara janyo wasu matsaloli na lafiya'', in ji Dr. Amina

Kumburin fata da ƙuraje

A cewar likitar saboda yawan zufa, yara kan samu ƙaiƙayi da ƙananan kuraje a fata.

''Wannan yana faruwa ne idan gumi ya toshe ramukan fata, yana janyo rashin jin daɗi ga yaro." in ji Likitar.

Amai da rashin cin abinci

Zafi na iya saka yaro ya fara amai ko ya kasa cin abinci in ji Dr. Amina.

Ta ƙara da cewa hakan na rage ƙarfinsa kuma yana iya ƙara janyo rashin ruwa a jiki.

Matsalar numfashi

Likitar yaran ta ce wasu yara kan fuskanci wahalar numfashi idan zafi ya yi yawa, musamman idan iska ba ta busawa yadda ya kamata ba.

Rashin bacci da damuwa

Likitar ta ce zafi kan hana yara samun isasshen bacci, wanda ke sa su zama masu kuka da rashin natsuwa.

Gajiya mai tsanani

Yara da ke wasa a waje a lokacin rana mai zafi na iya fuskantar gajiya mai tsanani.

Alamunta sun haɗa da zufa mai yawa da jiri da dai sauransu.

Idan ba a kula da wuri ba, likitar ta ce zai iya rikiɗewa zuwa mummunar cuta.

Yadda za a kula da yara a lokacin zafi

Dangane da yadda iyaye mata za su kula da yara a irin wannan yanayi, likitoci sun bayar da shawarwari masu muhimmanci kamar haka

  • Ba yara ruwa akai-akai

Likitar ta jaddada cewa yara ya kamata su riƙa shan ruwa akai-akai, ko da ba su nuna ƙishirwa ba. Wannan na taimakawa wajen hana rashin ruwa a jiki, wanda ka iya janyo kasala da rashin lafiya mai tsanani.

  • Shayar da jarirai nono akai-akai

Ga jarirai, shayar da su nono a kai a kai na da matuƙar muhimmanci. Nono yana ɗauke da ruwa da sinadarai da ke taimakawa wajen kare su daga zafin jiki da kuma rashin ruwa a jiki.

  • Tsayawa a wurare masu sanyi da iska

Ana shawartar iyaye su tabbatar da cewa yara suna zama a wuri mai sanyi, mai iska mai kyau, domin rage tasirin zafi a jikinsu. Wannan na taimakawa wajen hana gajiya da rashin natsuwa.

  • Guje wa fita a lokacin zafi mai tsanani

Likitar ta ce ya kamata a guji fita da yara lokacin da rana ke tsananin zafi, musamman daga rana zuwa yamma. Wannan lokaci shi ne mafi haɗari ga yara saboda zafin rana yana ƙaruwa sosai.

  • Sanya tufafi masu laushi marasa nauyi

Idan dole ne yara su fita, ya kamata a saka musu tufafi masu laushi da marasa nauyi. Wannan yana taimakawa wajen rage zafin jiki da hana yawan zufa.

  • Kula da tsaftar jiki

Dr. Amina Yusuf ta bayyana cewa wanka ko goge jikin yara da ruwa mai ɗumi (ba mai zafi ba) na taimakawa wajen rage zafin jiki. Haka kuma, tsaftar jiki da muhalli na kare yara daga cututtukan da ka iya biyo bayan zafi.

  • Kula da sauye-sauyen halayen yara

Iyaye mata su kasance masu lura da duk wani sauyi kamar zazzaɓi mai tsanani, yawan kuka ba tare da dalili ba, ko rashin kuzari. Waɗannan alamomi na iya nuna cewa yaro na cikin haɗari.

  • Kai yaro asibiti a kan lokaci

Idan aka ga alamun rashin lafiya mai alaƙa da zafi, ya zama dole a garzaya da yaro asibiti domin samun kulawar likita cikin gaggawa. Wannan na taimakawa wajen hana matsalar ta tsananta in ji likitar.

Likitar ta bayyana cewa yayin da zafi ke ci gaba da ƙaruwa, kulawa da yara ya zama wajibi fiye da kowane lokaci.