Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yaushe aka fara gano man fetur a Najeriya?
- Marubuci, Isiyaku Muhammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 7
Kusan shekara 70 ke nan da Najeriya ta gano ɗanyen mai na kasuwanci. Amma duk da wannan tsawon lokacin da ƙasar ta kasance tana fitar da miliyoyin ganga na ɗanyen, tambayar da ake yi ita ce: me wannan arziki ya kawo wa Najeriya, kuma me ƙasar ta rasa saboda dogaro da shi?
A wani rahoto da ma'aikatar man fetur ta Najeriya ta wallafa kan tarihin ɗanyen mai a Najeriya, ta ce a shekara ta 1956, kamfanin Shell-BP ya gano ɗanyen mai na kasuwanci a Oloibiri, a jihar Bayelsa ta yanzu.
Rahoton ya ƙara da cewa shekara biyu bayan, wato a 1958, Najeriya ta fara fitar da ɗanyen mai zuwa kasuwannin duniya, wanda shi ne ya buɗe wani sabon babi a tattalin arzikin ƙasar.
A wani binciken da babban bankin Najeriya CBN ya yi, ya gano cewa kafin gano mai, noma shi ne babban tushen arzikin ƙasar, wanda ke samar da kuɗaɗen shiga na gwamnati, amma daga baya kuɗaɗen da Najeriya ke samu daga fitar da mai suka zama ginshiƙin tattalin arzikin ƙasar.
Lokacin da mai ya sauya Najeriya
A shekarar 1971, Najeriya ta shiga ƙungiyar ƙasashe masu arzikin man fetur, OPEC, a lokacin da samar da mai ke ƙaruwa kuma gwamnati ke ƙara neman ƙara ƙarfi a hada-hadar man.
Shafin intanet na ma'aikatar man fetur ɗin Najeriya ya bayyana cewa a shekarar ce kuma aka kafa Nigerian National Oil Corporation, NNOC.
A tsakankanin shekarun 1970, man fetur ya ƙara zama muhimmin ginshiƙin tattalin arzikin Najeriya.
Binciken da babban bankin Najeriya ya gudanar ya ce kuɗaɗen da ake samu daga fitar da mai sun zama ƙashin bayan tattalin arzikin ƙasar, yayin da kasafin kuɗin gwamnati ya ƙara dogaro da kuɗaɗen shiga daga ɗanyen mai.
Amma binciken CBN ya kuma yi gargaɗin cewa dogaro da mai fiye da ƙima na iya sa tattalin arzikin ƙasa ya zama mai rauni idan farashin mai a kasuwannin duniya ya sauya.
A cewar binciken, faɗuwar farashin mai a duniya na iya rage kuɗaɗen shiga da gwamnati ke samu, wanda hakan ke shafar tattalin arziki da kuma ikon gwamnati na gudanar da ayyukanta.
Talauci, matsalar tsaro a yankunan haƙo mai
Yayin da Najeriya ke samun kuɗaɗen shiga daga mai, yankin Neja-Delta ya fuskanci manyan matsalolin muhalli da zamantakewa da suka shafi ayyukan masana'antar mai.
Binciken na CBN kan tasirin haƙar man fetur a Neja-Delta ya danganta ayyukan masana'antar da matsalolin da suka shafi muhalli, ciki har da gurɓatar ruwa da ƙasa da kuma illolin da hakan ke haifarwa ga rayuwar al'ummomin yankin.
A wasu yankunan da ake haƙo mai, lalacewar muhalli ta shafi sana'o'in da suka dogara da ƙasa da ruwa, kamar noma da kamun kifi.
Wannan ya taimaka wajen haifar da ƙorafe-ƙorafe daga al'ummomin masu arzikin mai kan rabon arzikin ƙasar, wanda daga bisa ya rikiɗe zuwa rikice-rikice, har aka fara garkuwa da mutane.
Binciken CBN ya ce yawan dogaro da kuɗaɗen mai da kuma batun yadda ake raba arzikin mai sun kasance cikin muhimman abubuwan da suka haifar da muhawara a Najeriya.
Shekara kusan 70 bayan gano mai a Oloibiri, Najeriya har yanzu na cikin manyan masu samar da ɗanyen mai a Afirka.
Wannan yana nuna cewa duk da sauye-sauyen da tattalin arzikin duniya ke fuskanta, man fetur har yanzu yana da muhimmiyar rawa a tattalin arzikin Najeriya.
Kuma farashin mai a yau fa?
A ranar 1 ga Oktoba 2026, ma'aunin farashin Brent ya tashi zuwa kusan dala 101.20 kan ganga ɗaya.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya danganta tashin farashin da matsin lamba kan samar da man fetur a duniya, ciki har da dakatarwar da China ta yi kan fitar da wasu kayayyakin mai da kuma matsalolin samar da makamashi da suka shafi wasu sassan duniya.
Farashin Brent yana da muhimmanci ga Najeriya saboda ɗanyen mai da take samarwa ana sayar da shi ne a kasuwar duniya.
Wani muhimmin sauyi a hada-hadar man fetur ta Najeriya shi ne ƙara samar da damar tace ɗanyen mai a cikin gida.
Hakan na da muhimmanci saboda Najeriya ta daɗe tana fitar da ɗanyen mai sannan tana shigo da wani bangare na kayayyakin da ake samu daga tace shi.
A shekarar 2026, NUPRC ta ce an samu ƙarin samar da ɗanyen mai ga matatun cikin gida. Tsakanin watan Afrilu da Yuni 2026, an samar da ganga miliyan 53.7 ga matatun cikin gida, abin da hukumar ta ce ya kai kashi 97.4 na aikin da aka tsara a wannan lokaci.
A cikin wannan lokacin, matatar Dangote ta nemi ganga miliyan 63, yayin da masu samar da mai suka gabatar da ganga miliyan 68.1 ga matatar, a cewar NUPRC. Daga cikin wannan adadin, matatar ta karɓi ganga miliyan 52.6.
Albarka ko tsinuwa?
A Najeriya, ana yawan danganta ɗimbin arzikin man fetur da ci gaban ƙasa. Sai dai masanin tattalin arzikin man fetur, Farfesa Ahmed Adamu, ya ce yawan arzikin mai kaɗai ba ya tabbatar da ci gaba, domin abin da ya fi muhimmanci shi ne yadda ake amfani da kuɗaɗen da ake samu daga albarkatun wajen bunƙasa tattalin arziki da rayuwar al'umma.
"Wasu ƙasashen da suke da man fetur sun fi Najeriya ci gaba, haka kuma akwai ƙasashen da ba su da wani albarkatun mai amma suka fi Najeriya ci gaba," in ji Farfesa Adamu. "Don haka ba a auna ci gaban ƙasa da yawan man fetur da take da shi ba, ana auna shi ne da yadda aka yi amfani da wannan arziki wajen ciyar da ƙasar gaba."
Masanin ya bayyana cewa ƙasashen da suka yi amfani da kuɗaɗen mai wajen gina masana'antu, ilimi, kiwon lafiya da ababen more rayuwa sun samu ci gaba mai dorewa. Ya bayar da misalin kasashen Saudiyya, Qatar da Kuwait, inda ya ce kuɗaɗen man fetur suka taimaka wajen sauya tattalin arzikinsu.
Sai dai ya ce a ƙasashen da suka dogara kacokan kan kuɗin man fetur ba tare da samar da wasu hanyoyin bunƙasa tattalin arziki ba, sau da yawa suna fuskantar abin da masana ke kira "resource curse", wato "tsinuwar albarkatun ƙasa".
"Duk ƙasar da ta dogara da man fetur da iskar gas kaɗai, ana samun kuɗin ne a kashe shi domin buƙatun yau, ba tare da gina tattalin arzikin gobe ba. Wannan shi ne abin da ake kira tsinuwar mai," in ji shi.
Fetur tsinuwa ce ga Najeriya?
Farfesa Ahmed Adamu ya ce bayan fara samun kuɗaɗen shiga masu yawa daga man fetur, Najeriya ta karkata hankali ga rabon kuɗaɗen mai maimakon bunƙasa sauran ɓangarorin tattalin arziki.
"An kai wani mataki da shugabanni suka fara cewa kuɗi ba matsalar Najeriya ba ne, yadda za a kashe su ne matsalar. Sai aka mayar da hankali kan kashe kuɗaɗe da bayar da tallafi, amma ba a gina makomar tattalin arziki ba," in ji shi.
A cewarsa, sakamakon hakan ne ake ganin Najeriya na ci gaba da fama da talauci, matsalolin tsaro da karancin ababen more rayuwa duk da dimbin kudaden da kasar ta samu daga man fetur cikin shekaru masu yawa.
"Albarkatun mai ba za su ba ƙasa arziki da kansu ba sai an yi amfani da su yadda ya kamata. A nan ne muhimmancin nagartaccen shugabanci yake fitowa," ya kara da cewa.
Da aka tambaye shi ko man fetur tsinuwa ne ga Najeriya, Farfesa Adamu ya ce akwai hujjojin da ke nuna hakan idan aka duba yadda aka yi watsi da sauran ɓangarorin tattalin arziki bayan gano mai.
"Kafin man fetur, yankuna da jihohi suna dogaro da abin da suke samarwa kamar noma, kasuwanci da ƙere-ƙere. Amma bayan kuɗin mai sun fara shigowa sosai, mutane da gwamnatoci suka zama tamkar masu jiran rabon kudin mai," in ji shi.
Ya ce hakan ya sa aka rage mayar da hankali kan kayayyakin da Najeriya ke fitarwa zuwa kasashen waje kamar auduga da sauran amfanin gona.
"Sai kowace jiha ta fara jiran kudin man fetur daga tarayya maimakon bunkasa albarkatun da take da su."
Masanin ya yi imanin cewa idan aka bai wa jihohi damar bunƙasa albarkatun da suke da su yadda ya kamata, hakan zai rage dogaro da kuɗin man fetur.
"Idan kowace jiha ta mayar da hankali kan albarkatun da take da su, za a samu gasa mai amfani tsakanin jihohi kuma za a daina zaman jiran kuɗin mai kawai," in ji Farfesa Adamu.
Ya yi gargaɗin cewa idan aka ci gaba da dogaro da mai kaɗai, duk lokacin da farashinsa ya fadi a kasuwar duniya, tattalin arzikin jihohi da na ƙasa zai shiga mawuyacin hali.
"Lokacin da farashin mai ya karye, jihohin da suka dogara da kuɗin mai za su shiga matsala, jama'a za su ƙara fadawa talauci, har ma tattalin arzikin ƙasa zai iya durƙushewa."
Me zai faru idan duniya ta rage buƙatar mai?
Rahotanni na baya-bayan nan na nuna cewa duniya na ci gaba da rage dogaro da man fetur, kuma tasirinsa ba zai tsaya kan tattalin arziki da muhalli kaɗai ba. Masana sun yi gargaɗin cewa idan ƙasashen da tattalin arzikinsu ya ta'allaka kan man fetur ba su shirya wa wannan sauyi ba, za su iya fuskantar matsalolin kuɗi, rashin kwanciyar hankali a siyasa, yawaitar ƙaura da kuma rikice-rikice.
Wani rahoto mai suna "The End of the Oil Era" da cibiyar bincike ta E3G ta wallafa ya bayyana cewa ƙasashe irin su Aljeriya, Najeriya, Angola, Iran, Iraki da Libiya na daga cikin waɗanda suka fi dogaro da kuɗaɗen man fetur wajen tafiyar da kasafin kuɗinsu da kuma samar da ayyukan gwamnati.
Rahoton ya ce waɗannan ƙasashe na da ƙarancin hanyoyin samar da kuɗaɗen shiga daga wasu fannoni na tattalin arziki, kuma ba su da isassun kadarori da za su taimaka musu shawo kan barazanar raguwar kuɗaɗen mai.
Wani sharhi da jaridar The Guardian ta Birtaniya ta wallafa ya yi hasashen cewa buƙatar mai a duniya za ta fara tsayawa cak sannan ta fara raguwa cikin shekaru goma masu zuwa. Wannan zai iya tilasta wa ƙasashen da ke samar da mai yin gogayya a kasuwa da ba ta da wani faɗi.
Rahoton ya ce ƙasashen da ke samar da mai cikin sauƙi da ƙarancin kuɗi, kamar Saudiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), za su iya jure irin wannan matsin fiye da ƙasashen da ke fuskantar tsadar haƙowa ko kuma waɗanda ba su bunƙasa wasu sassa na tattalin arzikinsu ba.