Rahoton kwamitin Premier League mai zaman kansa ya bayyana lamarin a sarari.
“An yi karin gishiri sosai kan kuɗin shiga na ƙungiyar da sama da fam miliyan 830.”
Kamar yadda kwamitin ya sanar, Manchester City ta kauce wa dokokin kuɗin gasar na tsawon wasu shekaru ta hanyar zuba kuɗi cikin ƙungiyar, wanda bai kamata a rubuta shi a matsayin kuɗin tallafi ba.
Hukuncin da ya bayyana matsalar ya zo ne kasa da kwanaki biyar bayan Manchester United ta gabatar da cikakken rahotonta na Kasuwar Hannun Jari ta New York (NYSE), inda ta bayyana asusun kuɗinta na shekarar da ta ƙare a ranar 30 ga watan Yunin 2026.
A cikin rahoton akwai kuɗin ruwa na fam miliyan 37, wanda ya karu daga fam miliyan 34 a shekarar da ta gabata.
Shahararren mai nazarin harkokin kuɗin shiga a ƙwallon ƙafa, Swiss Ramble, ya kiyasta cewa kuɗin ruwa da Manchester United ta biya tun bayan da ƙungiyar ta koma karkashin iyalan Glazer ta hanyar bashi a shekarar 2005 ya kai jimillar fam miliyan 852.
Kenan an tabbatar da cewa daya kungiyar ta birnin Manchester, mamallakanta sun zuba hannun jari cikin ƙungiya, wanda ya yi daidai da wani babban adadi na kuɗi da aka fitar daga ɗayan ƙungiyar wajen biyan ruwa kan bashi.
Carlos Baleba har yanzu bai fara buga wa Manchester United wasan farko a babbar ƙungiyar ba.
Sabbin asusun kuɗin United sun ƙunshi wannan bayani daga babban jami’in gudanarwa, Omar Berrada:
“Duk da cewa waɗannan sakamakon sun tabbatar da cewa muna kan turbar da ta dace, za mu ci gaba da bin tsarin kula da kashe kuɗi cikin tsanaki, domin tabbatar da cewa harkokin kuɗinmu sun kasance mai ɗorewa.”
Wannan ya zo ne bayan United ta kammala gasar Premier League a matsayi na uku a kakar da ta wuce, abin da ya tabbatar da komawarta gasar Champions League a bana, bayan shafe shekara biyu ba tare da shiga wasannin ba.
Samun kuɗin shiga mafi yawa a tarihin ƙungiyar da ta yi, wato fam miliyan 677.6, wanda ake hasashen zai iya kaiwa fam miliyan 760 a kakar 2026-27, abu ne da za a iya murna da wannan ci gaban.
Sai dai taka-tsantsan da Berrada ya nuna ya bayyana wasu muhimman abubuwa game da halin kuɗin ƙungiyar.
United ta tabbatar da cewa ta kashe fam miliyan 191.7 wajen sayen sabbin ’yan wasa da kuma wasu kuɗin da suka shafi su, musamman Carlos Baleba, Andrey Santos da Youri Tielemans, baya ga ’yan wasan karamar ƙungiyar kamar Tynan Thompson.
An bayyana cewa za a biya wasu daga cikin waɗannan kuɗin “a cikin shekara biyar masu zuwa”.
United ta kuma bayyana cewa ta sake karɓar ƙarin bashi na fam miliyan 90, lamarin da ya kai jimillar bashin da ake bin ƙungiyar zuwa fam biliyan 1.15.
Domin fahimtar girman wannan bashin a cikin asusun kuɗin da aka lissafa zuwa karshen watan Yuni 2021, adadin kwatankwacin wannan ya kasance fam miliyan 667.
Kafin ranar 30 ga watan Yuni, bashin dake kan United kan cinikayyar ’yan wasa ya kai fam miliyan 375.
Daga cikin wannan adadi, fam miliyan 218 dole ne a biya kafin ranar 30 ga watan Yuni 2027.
United ta kuma ce baya ga Baleba, Santos da Tielemans, za ta biya ƙarin fam miliyan 122.8 a matsayin wasu kuɗin kwangila idan ’yan wasan da ta riga ta saya suka cimma wasu sharuddan da aka amince da su tun farko.
Sai dai ana iya cewa ƙungiyar za ta samu sarari ne idan har ta kai ga biyan wannan kuɗin, domin hakan zai nuna cewa ’yan wasan sun cimma sharadodin da aka gindaya musu.