Wankan safe ko na dare: Wanne ya fi amfani?

.

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Wanka da safe ko da yamma?
    • Marubuci, Jasmin Fox-Skelly
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Future
  • Lokacin karatu: Minti 4

A wannan duniya mai faɗi da muke rayuwa a ciki akwai wata tambaya da ta banbanta mu da juna fiye da komai: ka na wanka da safe ko kana cikin waɗanda ba kullum suke wanka ba?

To ko a wacce matsaya ka ke, ka na tunanin mene ne tasirin zaɓin naka kan lafiyar ka.

Da dama daga cikin mu bayan tashi daga bacci da safe abu na farko da muke yi shi ne wanka.

Masu wanka da safe su na iƙirarin cewa bayan wankan mintuna 10 da ruwan zafi, saukar ruwan zafi a jikinsu ya na taimaka musu wajen wartsakewa da fuskantar ranar cikin shiri.

Yayin da waɗanda suke wanka da yamma suka yi ikirarin cewa wanka kafin kwanciyar bacci ya na taimaka musu wajen wanke dauɗar rana kafin su yi bacci mai daɗi.

Ko wanne ne ya fi muhimmanci gare mu a kimiyyance?

Zama da ƙwayoyin cuta

Idan ba ka yi wanka kafin kwanciya ba ɓurɓushin ƙwayoyin cuta zasu sauka kan zanin gadon ka da matashin kai.

Sannan fatar jikin na cakuɗe da ƙananan ƙwayoyin halitta.

Idan aka duba fata ƙarƙashin na'ura za a gano wasu ƙwayoyin hallitta kusan 10,000 ne ke rayuwa a jiki kuma su na zuƙar sindarin da ke fita daga ƙofofin gashin jikin ka.

Gumi shi kaɗai ba ya haifar da warin jiki amma sinadarin sulphur da ƙwayoyin cuta irin su staphylococcus na haifar da warin jiki.

Ana iya cewa yin wanka kafin kwanciya bacci kamar ya fi tsafta.

Sai dai kamar kowanne lokaci tantance gaskiya abu ne mai wahala

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Da dama sun fi son yin wanka kafin kwanciyar bacci don su wayi gari fes.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

''Idan ka yi wanka da yamma za ka kwanta cikin tsafta, amma kuma zaka ci gaba zubda gumi cikin dare,'' in ji Primrose Freestone masaniyar ƙwayoyin halitta a jami'ar Leicester da ke Burtaniya.

Freestone ta ƙara cewa ko a cikin sanyi mutum ya na ci gaba da fidda gumi na kusan rabin lita a kan gado yayin da fatar jiki ke karkaɗe ƙwayoyin halittar fata da yawansu ya kai sama da 50, 000.

''Don haka ko da ka yi wanka kafin kwanciyar bacci, saboda fatar jiki na fidda wani wari kaɗan da ƙwayoyin cutar da ke jikin fata suke ci. Idan ka tashi da safe jikin ka zai yi wari kaɗan" cewar Freestone.

Wankan dare zai yi amfani ne kawai idan ka na yawan wanke kayan shimfidar ka.

Ƙwayoyin cuta zasu iya rayuwa a jikin kayan shimfiɗar gado har tsawon makowanni.

Ƙwari da funfuna kan iya taruwa musamman idan akwai danshi a matashin kai.

Yayin da mutane masu ƙarfin garkuwar jiki zasu iya jurewa harin ƙananan ƙwayoyin cuta, kashi 76 na mutanen da suke fama da cutar asma su na kamuwa da cutuka..

Shaƙar funfuna kamar Aspergillus fumigatus zai iya haifar da ciwon hunhu mai tsanani ga mutaen da suke fama da cutar tarin fuka da kuma cutuka masu dangantaka da sarƙrwar numfashi.

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yawan sauya kayan shimfiɗa ya na hana taruwar ƙwarin da ƙura ke janyowa.

''Ana ganin wanke kayan shimfiɗa ya fi muhimmanci kan wankan dare,'' a cewar Holly Wilkinson Farfesa a fannin warkewa daga ciwo a jami'ar Hull da ke Burtaniya.

'' Saboda idan ka yi wanka kuma ka bar kayan shimfiɗar ka tsawon wata ɗaya cike da ƙwayoyin cuta da dauɗa, ƙura da ƙwari zasu samu wurin zama.''

Hakan zai iya cutar da lafiya.

Amfanin bacci

Waɗanda suka zaɓi wankan dare sun ce ya na taimaka musu wajen samun isasshen bacci kuma mutane da dama sun goyi bayan wannan iƙirari.

Wani bincike da masana lafiya suka gudanar ya gano yadda yin wankan mintina 10 da ruwan zafi sa'o'i 1 zuwa 2 kafin kwanciya bacci ya na sa bacci da wuri.

Akwai yiwuwar ƙarawa jiki ɗumi kafin sanyaya shi ya na sa jiki ya fara shirin bacci, bincike ne zai iya tabbatar da wannan.

La'akari da waɗannan bayanai, wacce ce amsa game da tambayar da ke cewa wanne ne ya fi amfani tsakanin wanka da safe ko wanka da yamma?

Freestone ta zaɓi wanka da safe saboda ya na wanke gumi da ƙwayoyin cutar da fata ta fitar.

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Hawa da saukan ɗimin jikin mutum bayan wankan dare zai iya taimakawa mutane su yi bacci cikin sauƙi.

Zaɓin ka ba shi da wani tasiri sosai a lafiyar jikin ka; ya danganka da ra'ayin ka idan ka na buƙatar ka zauna cikin tsafta da rana ko da daddare.

"Idan ka na yin wanka ɗaya a rana zaɓin lokaci ya rage na ka," cewar Wilkinson.

Idan za ka wanke muhimman wurare a jikin ka, yin wanka sau biyu a mako ya isa ka rayu cikin lafiya da tsafta.

"Ya danganta da irin aikin ka; misali idan manomi ne kai za ka so yin wanka idan ka koma gida a ƙarshen rana, to amma ina ganin tsaftace kayan shimfiɗa ya fi komai muhimmanci ," kamar yadda Wilkinson ya bayyana