Me ya sa har yanzu Houthi ke samun nasara wajen kai wa Saudiyya hari?

.
    • Marubuci, Lamis Al-Talibi, Ahmed Munaim, Dalal Gabriel, Mark Allison
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Fact Check
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Yayin da rikici ke ƙara tsananta tsakanin Saudiyya da ƙungiyar Houthi (Ansarullah), hankula na karkata kan irin makaman da ɓangarorin biyu ke amfani da su.

Duk da cewa Saudiyya na daga cikin ƙasashen da suka fi kashe kuɗi wajen tsaro a duniya, Houthi sun ci gaba da nuna cewa suna da damar kai hare-hare ta amfani da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa.

Amma waɗanne makamai ne kowanne ɓangare ke amfani da su, kuma me ya sa wasu hare-haren ke yin nasara duk da na'urorin kariya na zamani?

Waɗanne makamai Houthi ke amfani da su?

.

A cikin 'yan shekarun nan, ƙungiyar Houthi ta sauya daga ƙungiyar 'yan tawaye zuwa wata rundunar mayaƙa da ke da ƙarfin amfani da makamai na zamani waɗanda za su iya kai wa wurare hari masu nisan ɗaruruwan ko ma dubban kilomita daga yankunan da take iko da su.

Daga cikin makaman da suka fi ɗaukar hankalin masana harkokin tsaro akwai makamai masu linzami masu cin dogon zango, waɗanda ke iya kai hari kan wurare masu nisa.

Ana kyautata zaton cewa wasu daga cikin makaman sun samo asali ne daga fasahar Iran, ko da yake Tehran na ci gaba da musanta cewa tana bai wa Houthi makamai kai tsaye.

Ɗaya daga cikin fitattun makaman shi ne makami mai linzami na Zulfiqar (Barkan 3), wanda ake cewa yana da ƙarfin kai hari fiye da kilomita 1,200 tare da ɗaukar ɗaruruwan kilogram na abubuwan fashewa.

Haka kuma Houthi na iƙirarin cewa suna da makamai masu linzami na hypersonic, waɗanda ke tafiya cikin sauri, lamarin da ke sa su zama masu wahalar kakkaɓowa yayin da suke sararin samaniya.

Jirage marasa matuƙa sun sauya salon yaƙi

Baya ga makamai masu linzami, jirage marasa matuƙa sun zama ɗaya daga cikin muhimman makaman da Houthi ke amfani da su.

Tana amfani da jirgin maras matuƙi na Rajum wajen kai hare-hare na kusa, kuma yana iya ɗaukar bama-bamai masu nauyi.

Ƙungiyar na kuma da jiragen leƙen asiri marasa matuƙa kamar Samad-1, waɗanda ake amfani da su wajen tattara bayanan sirri ko kuma amfani da su domin ɗaukar abubuwan fashewa da kai hare-hare.

Saboda tsadarsu ba ta kai ta jiragen yaƙi ba, jirage marasa matuƙa sun bai wa Houthi damar kai hari kan sansanonin soji, filayen jiragen sama da muhimman kayayyakin more rayuwa a cikin Saudiyya.

Saudiyya na mayar da martani da manyan makaman yaƙi

A ɓangaren Saudiyya kuwa, ƙasar na da ɗaya daga cikin rundunonin soji mafiya kayan aiki na zamani a yankin Gabas ta Tsakiya.

Ƙasar na amfani da jiragen yaƙi na zamani, da tsarin kariyar sararin samaniya, da kuma jiragen yaƙin Apache masu saukar ungulu, waɗanda ke iya ɗaukar makamai masu linzami tare da ƙaddamar da hare-hare dare da rana.

Saudiyya ta kuma fara amfani da jirage marasa matuƙa na zamani irin su SkyWasp, waɗanda ke iya gudanar da ayyukan leƙen asiri da kuma kai hare-hare daga nesa.

Sai dai daga cikin makaman da suka fi jan hankali a rumbun makaman Saudiyya akwai tsarin kariyar sararin samaniya na Patriot da THAAD, waɗanda Amurka ta ƙera.

F 15

Me ya sa Saudiyya ba ta iya dakatar da kowane hari?

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tambayar da mutane da dama ke yi ita ce: idan Saudiyya na da irin waɗannan ingantattun tsarin kariya, me ya sa har yanzu wasu makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa na Houthis ke samun nasarar tsallake kariyarta?

A cewar Nawaf Obaid, babban mai bincike a Sashen Nazarin Yaƙi na King's College da ke Landan, nasarar da wasu hare-hare ke samu ba tana nufin cewa tsarin kariyar Saudiyya ya gaza ba.

Ya ce ƙididdiga na nuna cewa Saudiyya ta yi nasarar lalata tsakanin kaso 89 zuwa 90 cikin 100 na makamai masu linzami da sauran makaman da Houthi suka harba.

Babban ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta shi ne girman faɗin ƙasarta. Saudiyya na da manyan yankuna masu faɗi, tare da tashoshin man fetur, filayen jiragen sama, tashoshin jiragen ruwa da sauran muhimman kayayyakin more rayuwa da suka bazu a sassa daban-daban na ƙasar.

Bugu da ƙari, ana kai wasu hare-haren ne lokaci guda ta amfani da makamai masu linzami na ballistic, da na cruise, da kuma jirage marasa matuƙa, abin da ke ƙara wahalar daƙile su gaba ɗaya a lokaci ɗaya.

Yaƙin da fasahar zamani

Wannan rikicin ya nuna yadda yaƙe-yaƙe na zamani ke ƙara dogaro da fasaha fiye da yawan sojoji kaɗai.

A wani ɓangaren, Saudiyya na amfani da tsarin kariyar sararin samaniya da jiragen yaƙi na zamani masu tsada. A ɗaya ɓangaren kuma, Houthi na amfani da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa waɗanda galibi ba su da tsada sosai, amma za su iya haifar da mummunar ɓarna idan suka kai ga inda aka nufa.

Sakamakon haka, rikicin ya koma wani yaƙi na fasaha, inda kowanne ɓangare ke ƙoƙarin samun rinjaye ta hanyar sabbin dabarun soja da kuma amfani da nagartattun hanyoyin kai hari da kariya.

Yayin da rikicin ke ci gaba, babbar tambayar da ke ci gaba da tasowa ita ce: shin tsadar tsarin kariya za ta iya ci gaba da jure wa hare-haren jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami masu araha amma masu ƙara inganci?

Wannan ita ce tambayar da yaƙin da ke tsakanin Saudiyya da Houthi ke ci gaba da bayar da amsarta a kullum.