Atiku da Obi da Kwankwaso sun jagoranci zanga-zanga a Abuja
Atiku da Obi da Kwankwaso sun jagoranci zanga-zanga a Abuja
Fitattun 'yan jam'iyyar haɗaka ta ADC da suka haɗa da Atiku Abubakar da Peter Obi da Rabiu Kwankwaso ne suka jagoranci zanga-zangar nuna adawa da matakin hukumar zaɓe mai zaman kanta Inec kan jam'iyyar da suka kira da "Ceto Dimokuradiyyar Najeriya" a yau, Laraba.
Sauran manyan jiga-jigan jam'iyyar da suka shiga zanga-zangar sun haɗa da tsohon gwamnan jihar Rivers Rotimi Amaechi da tsohon shugaban majalisar dattawa David Mar da, tsohon gwamnan Osun Rauf Aregbesola, da tsohon gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal, da sauran su.



