Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dortmund ta nace wa Sancho, Tottenham ta matsa a kan Trafford
A karo na uku Borussia Dortmund za ta sake duba yuwuwar zawarcin danwasan gaba na gefe Jadon Sancho, dan Ingila mai shekara 26, wanda ke zaman aro a Aston Villa, kuma ake sa ran zai bar Manchester United, a matsayin wanda ba wani kwantiragi a kansa a bazaran nan. (Telegraph)
Tottenham na kara matsa lamba domin sayen mai tsaron ragar Manchester City, da Ingila James Trafford a bazaran nan, kuma golan mai shekara 23, na daga wadanda kungiyar ke matukar so ta saya a cefanen da za ta yi. (Teamtalk)
Arsenal na fatan ganin ta karfafa bayanta a bazaran nan,inda take son sayen dan bayan Real Madrid Victor Valdepenas, dan Sifaniya mai shekara 19, da kuma Jaco Ramon na kungiyar Como ta Sifaniya, wanda yake tawagar Sifaniya ta 'yan kasa da shekara 21, a cikin wadanda take son saye. (Caughtoffside)
Nottingham Forest na sa ran danwasan tsakiya na Ingila Elliot Anderson ya tafiko dai Manchester United ko kuma Manchester City, idan har ya bar kungiyar a bazaran nan, to amma kuma kungiyar tasa na neman kudin da ya kai fam miliyan 100 zuwamiliyan 120, a kan dan wasan mai shekara 23. (Florian Plettenberg)
Ba a sa ran Everton za ta nemi biyan fam miliyan 50 dominsayen danwasan gaba na gefer na Ingila Jack Grealish, kamar yadda tanadin yake a kwantiraginsa na aro zuwa Manchester City, to amma kungiyar tana da kwarin gwiwa cewa za a iya cimma sabuwar yarjejeniya da dan wasan mai shekara 30 ya ci gaba da zama a Merseyside. (Athletic)
Manchester City ta bi sahun sauran kungiyoyi da dama na Jamus (Bundesliga) da na Firmiya, wajen gogayyar sayen dan wasan tsakiya na Hertha Berlin, Kennet Eichhorn, dan Jamus mai shekara 16. (Fabrizio Romano)
Dan wasan gaba na gefe, Gabriel Martinelli, dan Brazil mai shekara 24, n matsa wa domin ganin ya ci gaba da zama a Arsenal, yayin da alamu ke nuna cewa kila kungiyar ta sayar da shi a bazaran nan. (Football Insider)
A shrye Leeds United take domin ta bar dan wasan gaba na Sifaniya Mateo Joseph, mai shekara 22, ya bar kungiyar a bazaran nan, bayan zaman aro da ya yi a Mallorca. (Football Insider)
Chelsea ba ta da niyyar sayar da matashin dan wasan baya na Ingila Josh Acheampong, mai shekara 19 a lokacin bazara, duk da cewa bai taka leda sosai ba a Chelsean. (Express)
Kociyan Plate, Eduardo Coudet da kansa ya tuntubi Chelsea, da dan wasan gaba na gefe na Argentina Alejandro Garnacho, mai shekara 21, a kan aro na shekara daya. (TyC via Football London)