Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yadda aljani ya aure ni'
- Marubuci, Anne Ngugi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Swahili
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Idan Vennie Katoti ta fara ba ka labarinta, za ka zata cewa fim kake kallo ko kuma ka yi tsammanin wani fim ne irin na dodanni ko fatalwa.
To amma labari ne na gaskiya, abu ne da ya faru a zahri.
Vennie, wadda aka haifa a ƙasar Kenya, ta bai wa BBC labarin ne a lokacin tana da shekara 31 a duniya.
Ta ce a lokacin yaruntarta ta taso kamar kowane bil'adama, amma sai abubuwa suka sauya a lokacin da ta hadu da saurayinta.
Yadda abin ya fara
Bayan ta kai shekara 18, sai Vennie ta haɗu da wani saurayi, wanda suka fara soyayya.
Bayan tafiya ta yi tafiya har wani abu ya shiga tsakani suka yi kwanciyar aure.
Ta ce al'amura sun yi nisa har saurayin nata ya shaida wa iyayensa game da soyayyar da ke tsakaninsu, kuma ya tabbatar mata cewa yana so ya aure ta.
Sai dai bayan wani lokaci sai ba ta ga al'adarta ta wata-wata ba.
A wani dare bayan ta haƙiƙance cewa tana da juna-biyu, sai ta yi mafarkin tana kwanciyar aure da wani, amma ba ta gane ko wane ne ba.
A lokacin da gari ya waye Vennie ta ji tamkar da gaske ta kwanta da namiji, amma kuma babu kowa a ɗakin.
Nan take sai ta ji cewa mutumin ya burge ta.
"Kasancewar na taɓa kwanciya da saurayina, wanda shi ne mahaifin ɗana, na san yadda ake ji," in ta.
"Saboda haka a lokacin da na farka da safe bayan na yi mafarkin wani ya kwanta da ni a cikin dare, na fahimci lallai tabbas an kwanta da ni, amma ban faɗa wa kowa ba."
Rushewar soyayya
Daga lokacin da Vennie ta fara kwanciya da wannan abin na cikin mafraki sai aka fara samun matsala a soyayyar da ke tsakaninta da saurayinta.
Lamarin ya kai ga cewa sai da ta rabu da saurayin nata, wanda a dalilin haka ya yi nesa da ita.
Kuma bayan wata 9 ta haifi ɗa, namiji.
Vennie ta ce an ci gaba da kwanciya da ita a cikin mafarki a tsawon lokacin da take da juna-biyu, kuma lamarin sai ya ƙara ƙamari bayan ta haihu.
Ta ce kuma abin na faruwa ne kodayaushe a cikin dare.
Misali, a cewarta, ba ta shiga cikin irin wannan yanayin da rana, lokacin da take gudanar da harkokinta na yau da kullum, amma da zaran ta kwanta bacci sai abin ya faru.
Ta ce a wasu lokutan ma aljanin da ke kwanciya da ita na zuwa mata ne ta siffar wata dabba.
"Zan iya tunawa kimanin wata 6 bayan na haihu, na ga wani maciji a farfajiyar gidanmu. Sai na ji a kowane lokaci ina son ganin macijin. Nakan je waje na riƙa dubawa, ina jira domin ganin macijin," in ji Vennie.
Ta ce haka nan aka riƙa kwanciya da ita a mafarki, har abin ya zama mata jiki.
Vennie ta ce ta sha wahala kan yadda za ta fito ta faɗa wa wani abin da ke faruwa da ita.
Cutar da kai
Vennie ta ce shaƙuwar da ta yi da mutanen ɓoye a rayuwarta ta sirri, ta sanya maza bil'adama sun fita daga ranta.
Ta ce a duk lokacin da ta hadu da wani mutum namiji wanda ya nuna yana son ta ko yin abota da ita sai alaƙar ta ruguje ba tare da sanin dalili ba.
Wannan lamari ya kai ga cewa ta fara yin wasu ɗabi'u da ke cutar da rayuwarta, da kuma waɗanda suka nemi yin wata alaƙa ta ƙut da ƙut da ita.
Ta riƙa keɓance kanta daga al'umma, ba ta kula da tsafta kuma ba ta wata hulɗar arziƙi da na kusa da ita.
Da gaske aljani zai iya auren mace?
Wannan wani abu ne da ke janyo muhawara a ɓangarori da dama, kamar ta fannin addini da kuma masana.
Masana tunanin bil'adama da malaman addini kan sha bamban a wannan ɓangare.
Masana tunanin ɗan'adam na ganin cewa irin wannan ɗabi'a kan samo asali ne daga abin da mutum ke tunani cikin ƙwaƙwalwarsa.
Suka ce idan mutum na yawan tunanin saduwa, to hakan zai riƙa tasiri kan abubuwan da ke faruwa a mafarkinsa.
Abin da malaman addinin Musulunci suka ce
Malamin Musulunci Sheikh Halliru Maraya da ke Najeriya ya ce: "E, amma sharia'a ba ta ambaci hakan ba.
"Dalilin aure shi ne haihuwa, amma a zahiri ba a taɓa ganin wadda aljani ya aura ya yi kwanciyar aure da ita ba har ta haihu," in ji Sheikh Maraya.
Ya ƙara da cewa "mafarki ba zahiri ba ne, saboda haka a shari'a babu wadda za a ce mata ta je ta yi wankan janaba saboda aljani ya yi kwanciyar aure da ita."
A cewar malamin aljani zai iya shiga jikin mace, ya kasance tare da ita amma ba aure kamar yadda ɗan'adam ke yi ba.
Sai dai a ɓangare ɗaya Sheikh Abdullahi Idris Muhammad, na cibiyar Danfodiyo Islamic Center da ke Kano ya ce : "Gaskiya ne, aljani na iya auren mace".
Ya ƙara da cewa "aljanu na auren mata ne sanadiyyar tsiraici da suke nunawa domin burge ɗan'adam, a saboda haka sai aljani ya yi sha'awarta kuma ya aure ta.
"Zai sadu da ita a cikin mafarki, za ta haihu a cikin mafarki kuma za ta shayar da jaririn a cikin mafarki, sannan yaran da ta haifa za su riƙa ziyartar ta a cikin mafarki," in ji Idris.
Malamin ya bayyana cewa aljanin da ke shigar mace saboda soyayya na daga cikin mafi "wahalar sha'ani domin suna da wahalar cirewa.
"Sai dai idan matar ta dage da karatun Qur'ani da zikiri, amma kuma mafi yawan lokaci aljanin zai hana ta karatun Qur'ani domin idan ta yi, tamkar tana azabtar da shi ne."
Sai dai Fasto T Mwangi, wanda mai bayar da shawarwari ne kan yadda za a rabu da miyagun ɗabi'u na ganin cewa wannan lamari na Vennie, wadda ta bayyana a cewa ƙauyensu sun yi imani da camfe-camfe da tsafi, ba abin mamaki ba ne idan wasu abubuwa na rayuwarta sun sanya miyagun aljanu sun shiga jikinta kuma suka riƙa cutar da ita.
Haka nan masana sun ce mutane da ke fama da ɗabi'un cutar da kai ko yawan shan barasa ko yawan saduwa, matsalar na farawa ne a hankali kafin ta gawurta daga baya, ta yadda abin yake zama mai wahala ga mutum ya rabu da ita.