Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Waɗanne saƙonni APC ke son aikawa a tarukan da take yi a jihohi?
- Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
- Aiko rahoto daga, BBC News Hausa
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta fara gangamin siyasa gabanin babban zaɓen 2027, inda ta gudanar da wani babban taro a Kano a ranar Asabar, wanda ya samu halartar manyan ƴan jam'iyyar daga ciki da wajen jihar.
A yayin taron, jam'iyyar ta karɓi wasu manyan ƴan siyasa da magoya bayansu da suka sauya sheka zuwa APC.
Jam'iyyar ta ce sama da mutum 136,000 ne suka shiga cikinta, ciki har da Sanata Rufa'i Hanga da tsohon gwamnan Kano, Sanata Kabiru Gaya.
Taron ya kuma samu halartar gwamnoni, sanatoci da sauran manyan jiga-jigan APC, inda suka nuna goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, tare da jaddada aniyar jam'iyyar ta samun nasara a zaɓen 2027.
Sai dai masu sharhi kan siyasa na kallon irin waɗannan taruka a matsayin wani yunƙuri na nuna ƙarfin jam'iyya da haɗa kan magoya baya, musamman a jihohin da ke da muhimmiyar rawa wajen samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa.
Hakan ne ya sa BBC ta yi nazari kan saƙonni biyar da APC ke son aikawa ta hanyar irin waɗannan taruka.
1. Nuna goyon baya ga sake zaɓen Tinubu
Ɗaya daga cikin saƙonnin da APC ke son isarwa ta irin waɗannan taruka shi ne cewa tana da goyon bayan jama'a, musamman a matakin ƙasa, wajen sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027.
Shugabannin jam'iyyar sun ce yawan mutanen da ke halartar tarukan na nuna cewa goyon bayan Tinubu da manufofin gwamnatinsa na ƙaruwa.
Sai dai Farfesa Kamilu Sani Fagge, masanin kimiyyar siyasa a Najeriya, ya ce irin waɗannan taruka ba su zama hujja kai tsaye ta yadda jama'a ke kallon gwamnati ba.
Ya ce sau da yawa ana ganin tururuwar mutane daga wasu jihohi zuwa irin waɗannan taruka ne domin nuna cewa suna tare da Shugaba Tinubu da jam'iyyarsa.
"Suna ƙoƙarin nuna wa duniya cewa jam'iyyar na kan daidai kuma suna mubaya'a da tsarin Shugaba Bola Ahmed Tinubu," in ji shi.
Sai dai ya ce a nasa ra'ayin, yawanci wannan ba ya wuce farfaganda, domin hatta wasu ƴan jam'iyyar sun san cewa manufofin gwamnatin ba su yi wa al'umma daɗi ba.
"Sanin kansu su ƴan jam'iyyar ne, ƙudurce-ƙudurcensu ya tagayyara rayuwar talaka kuma ta taɓarɓare," in ji shi.
2. Wayar da kan masu zaɓe
Ɗaya daga cikin saƙonnin da APC ke son isarwa ta irin waɗannan taruka shi ne wayar da kan masu zaɓe da kuma bayyana musu manufofin jam'iyyar gabanin zaɓen 2027.
Farfesa Kamilu Sani Fagge ya ce tun da aka riga aka fara harkokin siyasa gabanin zaɓen, dole ne jam'iyyu su yi ƙoƙarin jan hankalin masu kaɗa ƙuri'a.
Ya ce sukan yi amfani da irin waɗannan taruka wajen wayar da kan mutanen da ba ƴan jam'iyyarsu ba, domin bayyana musu tsare-tsaren da suke da su idan aka zaɓe su.
Sai dai masanin na ganin cewa ta wannan hanya ne kuma ƴan siyasa ke samun damar yin abin da ya kira "romon baka", domin jan hankalin wasu da samun goyon bayansu.
Ƴan jam'iyyar sun bayyana tarukan a matsayin wani ɓangare na shirin wayar da kan jama'a da neman goyon bayan masu zaɓe, domin samun nasara a Kano da sauran sassan ƙasar a zaɓen 2027.
3. Karɓar dubban masu sauya sheƙa zuwa APC
Wani saƙon da APC ke son aikawa in ji Farfesa Kamilu ta irin waɗannan taruka shi ne nuna cewa tana ƙara samun karɓuwa, ta hanyar karɓar ƴan siyasa da dubban magoya bayansu da suka sauya sheka daga wasu jam'iyyun adawa.
Ya ce a irin waɗannan taruka ne APC ta yi ƙoƙarin karɓar wasu gwamnoni, ƴan siyasa da sauran jiga-jigan adawa domin ƙara wa jam'iyyar ƙarfi.
A taron Kano, jam'iyyar ta karɓi wasu fitattun ƴan siyasa da kuma dubban magoya bayansu da suka sauya sheƙa zuwa cikinta. APC ta gabatar da hakan a matsayin wata alama ta ƙarin ƙarfinta da tasirinta a jihar.
Sai dai Farfesa Kamilu Sani Fagge ya ce karɓar waɗannan mutane na iya kasancewa wani ɓangare na dabarun ƴan siyasa na nuna cewa suna da karɓuwa a wajen jama'a.
"To waɗannan karɓar mutane na cikin tsare-tsaren ƙumbiya-ƙumbiya ta ƴan siyasa su nuna cewa suna da karɓuwa."
Sai dai ya ce ba lallai ne duk waɗanda ke sauya sheka su yi hakan saboda ra'ayinsu ba, domin wasu na iya yin hakan ne domin kauce wa wata barazana.
"Duk wannan farfaganda ce domin ganin an nuna jam'iyyar na da tagomashi," in ji shi.
4. Nuna muhimmancin Kano
Wani saƙon da APC ke son aikawa ta irin wannan taro shi ne nuna muhimmancin Kano a siyasar Najeriya da kuma irin rawar da jihar za ta iya takawa wajen samun nasara a zaɓen 2027.
Farfesa Fagge ya ce: "Kano na da muhimmanci a siyasar Najeriya."
Ya ce hakan ya samo asali ne daga yawan masu kaɗa ƙuri'a a jihar, wanda ya sa Kano ke da tasiri sosai a lissafin siyasar ƙasar.
A cewarsa, irin dandazon da jam'iyyar ta yi a jihar na daga cikin ƙoƙarin nuna cewa tana da dubban magoya baya da za su iya taimaka mata wajen samun nasara.
Haka kuma, ya ce yawancin masu zaɓe a Kano matasa ne, musamman ganin cewa jagoran ƙungiyar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya fito daga jihar, kuma ƙungiyar tana da matuƙar tasiri a tsakanin matasan jihar.
5. Haɗa kan ƴan jam'iyyar
Masu ruwa da tsaki a APC sun bukaci mambobin jam'iyyar da ƙungiyoyin da ke goyon bayanta su kasance haɗa kai, tare da yin aiki tare domin faɗaɗa tasirinta da matsayinta a siyasa.
Sai dai masanin siyasar ya ce a tsakanin masu zaɓe akwai rukuni uku: waɗanda ke goyon bayan jam'iyyar APC, waɗanda ke adawa da ita kuma ba za su zaɓi wata jam'iyyar ba komai zai faru, da kuma waɗanda ba su da wata jam'iyya.
Ya ce rukuni na ƙarshe ne ya fi muhimmanci ga jam'iyyun siyasa, saboda su ne za su iya sauya sakamakon zaɓe.
"Waɗanda suka fi muhimmanci su ne waɗanda ba su da jam'iyya. Su ake wa farfaganda domin a rinjaye su, domin su ga cewa ana tururuwa zuwa irin wannan taro, domin su kaɗa kuri'unsu a inda ba za ta yi tasiri ba."
Farfesa Fagge ya ce wannan na daga cikin dalilan da suka sa jam'iyyar ke shirya irin waɗannan taruka, domin nuna cewa tana da haɗin kai da kuma cikakken goyon bayan mambobinta.
Taron, wanda ƙungiyar Tinubu Support Group (TSG) ta shirya a Kano, wani yunƙuri na haɗa ƙungiyoyi daban-daban da ke yaɗa manufofin sake zaɓen Shugaba Tinubu a ƙarƙashin tsari guda. An ƙaddamar da tsarin TSG 2.0 tare da kafa rassan ƙungiyar a matakin ƙasa, jiha da ƙananan hukumomi.
Kafin taron, ƙungiyoyi masu yawa da ke goyon bayan Tinubu a Kano suna gudanar da ayyukansu daban-daban, ba tare da wata haɗaɗɗiyar hanya ta bai ɗaya ba. APC ta ce tana son kawo ƙarshen wannan rarrabuwar, domin a samu tsari guda, saƙo guda da kuma dabarar yaƙin neman zaɓe guda yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.
Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ce jam'iyyar za ta tantance tare da haɗa dukkan ƙungiyoyin da ke goyon bayan Tinubu domin kauce wa maimaita abin da ya faru a zaɓen 2023, lokacin da wasu ƙungiyoyi suka riƙa gudanar da ayyukansu ba tare da haɗin kai ba, har wasu lokuta suna yaɗa saƙonni daban-daban.
A wajen taron na Kano, an kuma samu manyan shugabannin APC, ciki har da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da tsohon shugaban jam'iyyar na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje. Shugabannin sun yi kira ga magoya bayan jam'iyyar da ƙungiyoyin goyon bayan Tinubu su ƙara ƙaimi wajen wayar da kan jama'a da kuma neman goyon bayan Shugaba Tinubu a zaɓen 2027.