Bene mai hawa uku ya ruguje a Abuja
Wani bene mai hawa uku ya ruguje a yankin Wuse Zone 4 da ke Abuja, sa'o'i kaɗan bayan sashen kula da ci gaban birane ya rufe ginin tare da umartar mutanen da ke cikinsa su fice.
Hotuna da bidiyon da suka yaɗu a kafafen sada zumunta sun nuna ginin ya ruguje, yayin da mutane suka taru a wurin bayan faruwar lamarin.
Ba a bayyana dalilin rugujewar ginin nan take ba.
Haka kuma, ba a tabbatar da ko akwai mutane a cikin ginin lokacin da ya ruguje ba, ko kuma ko akwai wadanda tarkacen ginin ya danne.
Sai dai Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya ta ce ta samu kiran gaggawa game da lamarin da misalin ƙarfe 7:45 na daren Litinin.
A cewar kakakin rundunar a Abuja, Josephine Adeh, an tura tawagar ’yan sanda zuwa wurin domin kai agajin gaggawa.