Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Rodri zai yanke makomarsa a Man City bayan kofin duniya

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga Litinin 01 zuwa Lahadi 07 ga watan Yunin 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Turkiya ta bayyana ƴan wasan da za su buga gasar kofin duniya, Gasar kofin duniya

    Kocin Turkiyya, Vincenzo Montella, ya sanar da jerin ƴan wasan da za su buga gasar Kofin Duniya, inda ya zaɓi ƙwararrun ƴan wasa kamar Hakan Çalhanoğlu da Arda Güler da Kerem Aktürkoğlu da Barış Alper Yılmaz domin jagorantar tawagar.

    An cire ɗan wasan tsakiya na Sporting Braga, Demir Ege Tıknaz, yayin da Montella ya mayar da hankali kan Kaan Ayhan na Galatasaray da Salih Özcan na Borussia Dortmund.

    A ɓangaren kai hari, an cire Aral Şimşir, wanda ya lashe ƙyautar gwarzon ɗan wasa a gasar Denmark, amma an saka İrfan Can Kahveci cikin tawagar.

    Turkiyya tana cikin Rukuni na huɗu a gasar Kofin Duniya, kuma za ta fara wasa da Australia, sannan ta kara da Paraguay da kuma Amurka, wadda ke ɗaya daga cikin masu karɓar bakuncin gasar.

    Jerin ƴan wasan tawagar Turkiya da za ta buga kofin duniya:

    Masu tsaron raga: Altay Bayindir (Manchester United), Mert Gunok (Fenerbahce), Ugurcan Cakir (Galatasaray)

    Masu tsare baya: Abdulkerim Bardakci (Galatasaray), Caglar Soyuncu (Fenerbahce), Eren Elmali (Galatasaray), Ferdi Kadioglu (Brighton & Hove Albion), Merih Demiral (Al-Ahli Saudi), Mert Muldur (Fenerbahce), Ozan Kabak (TSG 1899 Hoffenheim), Samet Akaydin (Caykur Rizespor), Zeki Celik (AS Roma)

    Masu buga tsakiya: Hakan Calhanoglu (Inter Milan), Ismail Yuksek (Fenerbahce), Kaan Ayhan (Galatasaray), Orkun Kokcu (Besiktas), Salih Ozcan (Borussia Dortmund)

    Masu cin ƙwallaye: Arda Guler (Real Madrid), Baris Alper Yilmaz (Galatasaray), Can Uzun (Eintracht Frankfurt), Deniz Gul (Porto), Irfan Can Kahveci (Kasimpasa), Kenan Yildiz (Juventus), Kerem Akturkoglu (Fenerbahce), Oguz Aydin (Fenerbahce), Yunus Akgun (Galatasaray)

  2. , Daga Jaridu

    Dan wasan Portugal Bernardo Silva na shirin rattaba hannu kan kwantiragin shekara biyu da Barcelona bayan ya bar Manchester City kuma dan wasan mai shekara 31 yana son a kammala cinikin a hukumance kafin karshen mako.(AS - in Spanish), external

    Watakila dan wasan Ingila Marcus Rashford, mai shekara 28, ya koma Manchester United a shirye-shiryen kakar wasa ta bana, yayin da komawarsa Barcelona, ​​inda ta kasance aro a kakar wasan da ta gabata, ta gamu da cikas.(Times - subscription required), external

    Manchester United na son ta cefanar da Rashford domin taimaka wa sabon kocin kungiyar Michael Carrick' samun kudin musayar 'yan wasa kuma Arsenal da Chelsea da Newcastle da Tottenham na bibiyar halin da ake ciki . Kungiyar dai ba ta son ta sayar da dan wasan ga daya daga cikin manyan abokan hammayarta. (Mirror), external

    Nottingham Forest za ta tattauna da dan wasan tsakiya Ibrahim Sangare, mai shekara 28, kan sabon kwantaragi yayin da Manchester United da Besiktas ke zawarcin dan kasar ta Ivory Coast.(Football Insider), external

  3. Mataimakin kocin Afirka ta Kudu ya samu bizar shiga Amurka ranar Talata, Gasar kofin duniya

    Mataimakin kocin Afirka ta Kudu, Helman Mkhalele, ya samu bizar shiga Amurka ranar Talata, kuma zai tashi zuwa sansanin tawagar a Pachuca, Mexico, bayan da ƴan wasa da sauran ma’aikatan suka tafi gasar ba tare da shi ba a ranar Litinin.

    Tafiyar Afirka ta Kudu zuwa gasar Kofin Duniya ta farko tun lokacin da suka karɓi bakunci a 2010 ta shiga rudani, bayan da aka gano cewa kuskuren gudanarwa ya sa yawancin ƴan wasa da ma’aikatan horarwa ba su samu bizar da ake buƙata ba a ranar da ya kamata su tashi da jirgin haya a ranar Lahadi.

    Za su fara wasa da ƙasashen da ke karɓar bakunci, Mexico, a wasan buɗe gasar a Mexico City a ranar 11 ga watan Yuni, kuma sun rasa aƙalla rana guda na shiri da sabawa da yanayin Pachuca.

    An fara ƙin amincewa da bukatar bizar Mkhalele da kuma Mdu Mbatha, daga Ofishin Jakadancin Amurka da ke Johannesburg saboda dalilan da ba a bayyana ba, amma yanzu an amince da su.

    Shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka ta Kudu, Danny Jordaan, ya ce: “Zan tabbatar da cewa Helman da Mbatha sun samu bizar su, kuma za su tafi su haɗu da tawagar ranar Laraba duk za su kasance tare.”

    Ya kuma ƙara da godiya ga ma’aikatan ofishin jakadancin Amurka.

    Afirka ta Kudu za ta buga wasan sada zumunci da Jamaica a ranar Juma’a.

    Suna cikin Rukunin A a gasar Kofin Duniya, inda bayan Mexico za su kara da Jamhuriyar Czech a Atlanta a ranar 18 ga watan Yuni, sannan su kara da Koriya ta Kudu a Monterrey kwanaki shida bayan nan.

  4. Rodri zai yanke makomarsa a Man City bayan kofin duniya

    Ɗan wasan tawagar Spain, Rodri, ya ce hankalinsa ya karkata ne kan Kofin Duniya, kuma zai yi magana kan makomarsa a Manchester City ne kawai bayan kammala gasar.

    Wanda ya lashe ƙyautar Ballon d’Or ta 2024 ya shiga shekararsa ta ƙarshe a kwantiraginsa da Etihad mai buga gasar Premier League, kuma ana danganta shi da yiwuwar komawa Real Madrid.

    Spain mai rike da kofin nahiyar Turai za ta kara da Cape Verde, Saudi Arabia da Uruguay a Rukunin takwas a gasar da za a fara daga 11 ga watan Yuni zuwa 19 ga watan Yuli a Arewacin Amurka.

    Rodri ya ce ya kuma bukaci abokan wasansa na Spain su yi koyi da jarumin wasan tennis Rafael Nadal bayan ya kalli shirin bidiyo (documentary) game da shi.

  5. , Daga Jaridu

    Dan wasan kasar Ivory Coast Evann Guessand, mai shekara 24, na nazari kan kungiyar da zai koma bayan karewar wa'adin aronsa daga Aston Villa zuwa Crystal Palace don mayar da cinikin na dindindin .(Evening Standard), external

    Aston Villa na son ta bar dan wasan Sifaniya Andres Garcia, mai shekara 23, barin kungiyar a matsayin aro a lokacin bazara, inda Valencia da Elche na cikin cikin kungiyoyin da ke zawarcinsa. (Tribuna Deportiva - in Spanish), external

    Tottenham ta bayyana dan wasan Eintracht Frankfurt Jean-Matteo Bahoya a matsayin dan wasan da take son ta saya, amma kungiyar ta Bundesliga ba za ta bar dan Faransa mai shekara 21 ya tafi a farashi mai rahusa ba.(Teamtalk), external

  6. Liverpool ta yi nisa kan tattaunawa da Iraola domin ba shi aikin koci, Liverpool

    Liverpool ta yi nisa kan tattaunawa da Andoni Iraola yayin da suke neman sabon kocin ƙungiya, bayan korar Arne Slot.

    Iraola ya bar Bournemouth a ƙarshen kakar wasan bana, kuma shi ne wanda ake ganin ya fi kusa da samun aikin horar da Liverpool a Anfield.

    Liverpool na son yin nadin koci da wuri-wuri, kuma tana neman kocin da ya dace da salon wasansu da suka fi so—wato ƙwallon ƙafa mai kai hari da kuma matsa wa abokin hamayya lamba.

    Har yanzu ba a fara tattaunawa kan ma’aikatan horarwa na Iraola ba, amma ɗan ƙasar Spain ɗin mai shekaru 43 yana sha’awar ɗaukar mataimakinsa a Bournemouth, Tommy Elphick, wanda kuma tsohon mai son Liverpool ne tun yana yaro, domin ya zo tare da shi.

  7. Chelsea ta yi watsi da tayin sayen Acheampong, Premier League

    Chelsea ta ƙi karɓar tayin da ƙungiyoyi da dama da suka yi domin sayen mai tsaron baya, Josh Acheampong.

    Ɗan wasan mai shekara 20, wanda ya fito daga makarantar horas da ƴan wasa ta Stamford Bridge, an ba shi matsayin “wanda ba za a taɓa sayarwa ba” dangane da makomarsa a ƙungiyar ɗin.

    Wannan ya sanya shi a cikin rukuni ɗaya da ƴan wasa kamar João Pedro da Cole Palmer a gaba, da kuma Moisés Caicedo.

    Hakan na zuwa ne duk da cewa ɗan wasan Ingila na ƴan kasa da shekara 21 ya buga wasa 17 a Premier League a kakar da ta gabata, inda tara daga cikinsu ya fara daga benci.

    Har yanzu ba a tabbatar ba ko Acheampong, wanda kwantiraginsa da Chelsea zai kare a 2029, yana son barin ƙungiyar.

    Sai dai Arsenal, Newcastle da Crystal Palace na sa ido kan halin da yake ciki, yayin da Bournemouth kuma ke ci gaba da nuna sha’awar sayensa tun a bara.

  8. Ƴan takarar shugabancin Fenerbahce na son sayen Greenwood, Kwallon kafa

    Mason Greenwood shi ne babban ɗan wasan da dukkan ƴan takarar shugabancin Fenerbahce biyu ke son saye.

    Tsohon ɗan wasan Manchester United da tawagar Ingila ya sha wahala a ƴan watannin nan a Marseille.

    Sabon daraktan wasanni na ƙungiyar, Gregory Lorenzi, ya ce a makon da ya gabata cewa a shirye yake ya saurari tayin sayen Greenwood, wanda ya rage masa shekara uku a kwantiragin shekaru biyar da ya kulla lokacin da ya bar Manchester United a watan Yulin 2024.

    Tsohon shugaba, Aziz Yildirim, na fafatawa da Hakan Safi kan kujerar shugabancin ƙungiyar ta Turkiyya, kuma ana sa ran za a sanar da sakamakon a ranar Lahadi.

    An ce ba a ganin cewa samun yarjejeniya da Greenwood zai zama matsala.

    Ɗan wasan ya koma gina rayuwarsa ne a wajen Manchester United duk da cewa an janye tuhumar da ake masa na yunƙurin fyade da cin zarafi a watan Fabrairu 2023.

    Bincike na cikin gida ya kammala cewa Greenwood ba zai sake buga wa United wasa ba. A watan Afrilu, sabon kocin Tottenham, Roberto De Zerbi, ya nemi afuwa bayan ya kare Greenwood a lokacin da yake Marseille.

    Ɗan wasan mai shekaru 24 ya zura kwallaye 48 a wasa 81 da ya buga wa Marseille. Ya gama kakar Ligue 1 da kwallaye 16, inda ya zo na biyu a jerin masu yawan cin kwallaye, bayan Esteban Lepaul na Rennes.

    Fenerbahce ta kare a matsayi na biyu a gasar Super Lig ta Turkiyya har sau biyar a jere, kuma za ta shiga gasar Champions League daga zagayen share fage na biyu a watan Yuli.

  9. An saka Partey cikin tawagar Ghana da za ta buga kofin duniya, Gasar kofin duniya

    Tsohon ɗan wasan Arsenal, Thomas Partey, yana cikin ƴan wasa tawagar Ghana Ghana da za ta halarci gasar Kofin Duniya a bana.

    Partey ya musanta laifuka guda bakwai na yi wa mata fyade da kuma ɗaya na cin zarafi, da ake zarginsa da aikatawa tsakanin 2020 zuwa 2022, dangane da korafe-korafe daga mata huɗu daban-daban.

    Ɗan wasan mai shekara 32, wanda yanzu ke buga wa Villarreal tamaula a La Liga, zai gurfana a gaban kotu a shekara mai zuwa.

    Partey ya buga wa Arsenal wasa 167 a dukkan fafatawa tsakanin 2020 zuwa 2025, amma ya bar Emirates a bazarar da ta gabata bayan kwantiraginsa ya ƙare.

    Kocin Ghana, Carlos Queiroz, ya saka Partey cikin jerin ƴan wasa 28 na wucin gadi domin atisaye kafin Kofin Duniya da kuma wasan sada zumunci da Wales a Cardiff a ranar 2 ga Yuni.

    Partey ya ci gaba da kasancewa cikin tawagar yayin da Queiroz ya cire masu tsaron raga Solomon Agbasi da Paul Reverson domin rage adadin zuwa ƴan wasa 26 na ƙarshe.

    An cire mai tsaron baya Alexander Djiku bayan da ya ji rauni a yayin da Spartak Moscow ta lashe kofin Russia, don haka aka maye gurbinsa da Derrick Luckassen, wanda aka haifa a Netherlands kuma ya fara buga wa Ghana tamaula a watan Maris.

    Haka kuma akwai Antoine Semenyo na Manchester City da Brandon Thomas-Asante na Coventry, tare da ƴan wasan Leicester Jordan Ayew da Abdul Fatawu.

    Joseph Anang, wanda ke buga wa St Patrick Athletic a League of Ireland, yana ɗaya daga cikin masu tsaron raga uku a tawagar.

    Mai taka leda a Tottenham, Mohammed Kudus bai samu goron gayyata ba, saboda raunin ƙafa da ya hana shi buga wasa tun watan Janairu.

    Jerin ƴan wasa 28 da Ghana ta bayyana:

    Masu tsaron raga: Benjamin Asare (Accra Hearts of Oak SC), Lawrence Ati-Zigi (St Gallen), Joseph Anang (St Patrick's Athletic).

    Masu tsaron baya: Baba Abdul Rahman (PAOK), Gideon Mensah (Auxerre), Marvin Senaya (Auxerre), Alidu Seidu (Rennes), Abdul Mumin (Rayo Vallecano), Jerome Opoku (Istanbul Basaksehir), Jonas Adjetey (Wolfsburg), Kojo Oppong Peprah (Nice), Elisha Owusu (Auxerre), Derrick Luckassen (Pafos).

    Masu buga tsakiya: Thomas Partey (Villarreal), Kwasi Sibo (Real Oviedo), Augustine Boakye (Saint-Etienne), Caleb Yirenkyi (Nordsjaelland), Abdul Fatawu Issahaku (Leicester City).

    Masu cin ƙwallaye: Kamaldeen Sulemana (Atalanta), Christopher Bonsu Baah (Al Qadsiah), Ernest Nuamah (Lyon), Antoine Semenyo (Manchester City), Brandon Thomas-Asante (Coventry City), Prince Kwabena Adu (Viktoria Plzen), Inaki Williams (Athletic Bilbao), Jordan Ayew (Leicester City).

  10. ‘Yansanda sun kama mutum 24 bayan soka wa mutum 6 wuka wajen bikin murnar lashe kofin Arsenal

    Yansanda sun kama mutum 24 a Landan bayan soka wa mutum 6 wuka a gangamin murnar lashe kofin da kungiyar Arsenal ta yi a birnin.

    Hukumar ‘yansanda birnin Landan ta ce wadanda aka soka wa wukar ba su samu munanan raunuka ba, sai dai an garzaya da wani matashi dan shekara 20 asibiti saboda yana cikin mawuyacin hali.

    ‘Yansandan sun ce an soki matashin ne a titin Hornsey, jim kadan kafin karfe 8:30 na daren ranar Lahadi.

    Fiye da ‘yansanda 500 ne aka baza a birnin Landan domin tabbatar da doka a bikin, wanda ya tara dubun dubatar magoya bayan kungiyar Arsenal domin murnar lashe kofin gasar Premier karon farko a cikin shekara 22.

  11. Ana sa ran Iraola ne zai maye gurbin Slot a Liverpool, Liverpool

    Andoni Iraola shi ne kan gaba da ake ganin za a bai wa akin kociyan Liverpool, bayan da ta kori, Arne Slot a ranar Asabar.

    An fahimci cewa Iraola ya riga ya tattaunawa da Crystal Palace da Bayer Leverkusen da kuma AC Milan tun bayan da ya sanar da zai bar Bournemouth da zarar an kammala kakar nan, amma yanzu da alama shi ne babban zaɓin Liverpool, inda daraktan wasanni Richard Hughes—wanda ya taɓa nada shi a Bournemouth—ke da tasiri a yanke shawarar.

    Ga bayan aikin kociyansa da lambobin girmamawa:

    – Iraola ya bar Bournemouth bayan ta shafe wasa 19 ba tare da rashin nasara ba, kuma ya kai zuwa gasar Europa League, wanda shi ne karo na farko da suka taɓa samun tikitin Turai a tarihinsu.

    – Bournemouth ta sha kashi sau bakwai kacal a gasar Premier League a kakar nan, inda ta kare a matsayi na shida. Arsenal da Manchester City ne kaɗai suke da ƙarancin rashin nasara a kansu, yayin da Liverpool ta sha kashi sau 12 duk da cewa ta kare a matsayi ɗaya sama da Bournemouth.

    – A cikin shekara uku da ya jagoranta, ƙungiyar ta yi nasara a wasa 47 cikin 127 (kashi 37%), ta yi canjaras 40, ta kuma sha kashi 40. Ta zura ƙwallaye 196.

    – Nasarar Bournemouth ta zo ne duk da yawan sayar da manyan ƴan wasa. A kakar da ta gabata, uku daga cikin ƴan baya huɗu sun tafi kafin fara kakar, inda ƙungiyar ta samu kusan £144.5m daga sayar da Milos Kerkez da Dean Huijsen da kuma Illia Zabarnyi.

    – Antoine Semenyo shi ne wanda ya fi zura ƙwallaye a zamanin Iraola da 31 a raga a dukkan fafatawa.

    – A baya, Iraola ya horar da AEK Larnaca inda ya lashe Cypriot Super Cup a 2018, Mirandés a Spain, da Rayo Vallecano inda ya taimaka musu zuwa LaLiga sannan suka kare a matsayi na 12 da na 11. A dukkan ƙungiyoyin da ya horar, yana da kashi 38.4% na nasara.

  12. Iraq ta sanar da ƴan wasan da za su buga mata kofin duniya, Gasar kofin duniya

    Kocin Iraq, Graham Arnold, ya sanar ranar Litinin jerin ƴan wasa 26 da za su buga Kofin Duniya, inda ya dogara sosai da babban rukuni na ƴan wasan da suka taimaka wajen samun tikitin shiga gasar ta hanyar wasannin share fage a tsakanin nahiyoyi.

    Ɗan wasan da ke buga gaba, Aymen Hussein ana sa ran zai jagoranci gurbin kai hare-hare a tawagar Iraq a wasannin da za ta buga a Arewacin Amurka. Wannan tsohon ɗan wasan, wanda ake kallonsa a matsayin gwarzo, shi ne zai jagoranci sahun gaba tare da Ali Al-Hamadi na Ipswich Town da kuma matasan ƴan wasa masu basira da ya haɗa da Ali Jassim da kuma Youssef Amyn.

    Wani abin lura shi ne rashin sunan Dario Naamo daga cikin tawagar. An cire ɗan wasan Dundee, bayan da ya canza ƙasar da yake wakilta a wasannin ƙasa da ƙasa, bayan da ya taɓa bugawa Finland a matakin matasa.

    Zaɓin ƴan wasan tsakiya na Arnold ya ƙunshi ƙwararru da suka saba da ƙwallon ƙafa a Turai, inda Zidane Iqbal na Utrecht da Aimar Sher na Heerenveen ke kan gaba a jerin.

    Haka kuma, Arnold ya yanke shawarar barin mai tsaron raga, Kamil Saadi cikin tawagar atisaye a matsayin kariya idan aka samu rauni.

    Iraq na komawa gasar Kofin Duniya a karon farko cikin shekaru 40, bayan ta doke Bolivia da ci 2-1 a watan Afrilu domin samun tikitin ƙarshe.

    An saka su a Rukunin I tare da Faransa da Senegal da kuma Norway.

    Masu tsare raga: Fahad Talib, Jalal Hassan, Ahmed Basil

    Masu tsaren baya: Hussein Ali, Manaf Younis, Zaid Tahseen, Rebin Sulaka, Akam Hashem, Merchas Doski, Ahmed Yahya, Zaid Ismail, Frans Putros, Mustafa Saadoon

    Masu buga tsakiya: Amir Al Ammari, Kevin Yakob, Zidane Iqbal, Aimar Sher, Ibrahim Bayesh, Ahmed Qasim, Youssef Amyn, Marko Farji Masu cin ƙwallaye: Ali Jassim, Ali Al Hamadi, Ali Yousef, Aymen Hussein, Mohanad Ali

  13. , Daga Jaridu

    Kocin Arsenal, Mikel Arteta, ya nuna aniyar dauko dan wasan Aston Villa da Ingila Morgan Rogers, mai shekara 23, a kokarinsa na ci gaba da samun nasarar lashe gasar Premier, duk da cewa Paris St-Germain da ta lashe gasar zakarun Turai ita ma na zawarcinsa. (Mirror), external

    Manyan masu daukar ma'aikata a Real Madrid sun bukaci kungiyar ta nemi dan wasan Arsenal Declan Rice, sakamakon yadda dan wasan na Ingila mai shekaru 27 ya burge su kan jagoranci da kuma kwarewa.(Teamtalk), external

    Golan Liverpool Alisson, mai shekara 33, yana shirin fada wa sabon kocin kungiyar cewa yana son ya bar Anfield ya koma Juventus. (Gazzetta dello Sport - in Italian), external

    Manchester United na gab da kulla yarjejeniya da dan wasan Brazil Ederson, mai shekara 26, daga Atalanta kan kudi kusan fan miliyan 35. (Talksport), external

  14. Za a hana ƴan wasa zuwa wajen koci idan gola ya ji rauni a gasar kofin duniya, Gasar kofin duniya

    Za a hana ƴan wasa a gasar Kofin Duniya ta 2026 zuwa yankin masu horarwa, domin tattaunawa da koci a lokacin da mai tsaron raga ya ji rauni, kamar yadda shugaban alkalan FIFA, Pierluigi Collina, ya bayyana.

    Haka kuma, Hukumar Dokokin Kwallon Kafa ta Duniya (IFAB) ta amince da bukatar sauya tsarin VAR, domin a ba da damar duba kura-kuran da suka shafi ketar da aka yi wa ƴan wasa.

    Wannan tsarin da ake kira “goalkeeper tactical timeout” ya zama abin tattaunawa sosai a ƴan shekarun nan. Ana amfani da shi a wasu lokuta ne ta hanyar kociyoyi domin ba ƴan wasa sabbin umarni ko dabaru ko kuma rage karfin gwiwar abokan hamayya.

    A watan Nuwamba, kocin Leeds United, Daniel Farke, ya zargi mai tsaron ragar Manchester City, Gianluigi Donnarumma, da yin kamar ya ji rauni domin “karkatar da dokoki” da kuma dakatar da wasa na ɗan lokaci.

    A irin wannan yanayi, mai tsaron raga kan zauna a kasa ya nuna alamar neman a duba lafiyarsa, sauran ƴan wasa su tafi wajen koci domin samun sabon umarni, sannan da zarar an gama bayanin, mai tsaron ragar zai tashi ya ci gaba da wasa kamar yadda aka saba.

  15. Har yanzu Wiliiams na jin raɗaɗin da kasarsa ba za ta buga gasar kofin duniya ba, Gasar kofin duniya

    Neco Williams ya amince cewa rashin zuwa buga gasar cin Kofin Duniya ta bana har yanzu yana ci masa rai, domin ya yi imanin Wales za ta iya yin tasiri a gasar da za a yi a Amurka da Canada da kuma Mexico.

    Wales ta rasa damar zuwa gasar karo na biyu a jere bayan ta sha kashi a wasan neman cike gurbi a hannun Bosnia-Herzegovina.

    Wannan rashin nasara ta fi taɓa zuciyar ɗan wasan baya na Nottingham Forest, Neco Williams, musamman ganin cewa shi ne ya kasa cin fenariti mai muhimmanci a karawar.

    Sai dai duk da wannan ci gaba da takaici, ɗan wasan mai shekara 25 ɗin ya ce wasannin sada zumunta da Ghana da Romania a wannan mako su ne matakin farko na ci gaba da huce wannan raɗaɗi, yayin da tawagar ke mai da hankali kan gasar Euro 2028 da za a yi a gida.

    Wasan da za su buga da Ghana a Cardiff ranar Talata zai zama abin tunawa da abin da suka rasa, domin Ghana na shirin shiga rukunin gasar World Cup ɗin da Ingila za ta kasance a ciki.

  16. , Daga Jaridu

    Dan wasan Portugal Joao Palhinha, mai shekara 30, ba ya son aron da aka ba da shi daga Bayern Munich zuwa Tottenham ya koma na dindindin kuma zai yi kokarin ganin ya koma Sporting a maimakon haka. (A Bola - in Portuguese), external

    Manchester United da Chelsea da Arsenal da Tottenham da Liverpool da kuma Newcastle dukkaninsu na zawarcin dan wasan AC Milan da Portugal Rafael Leao inda dan wasan mai shekara 26 na son ya bar San Siro a wannan bazara . (Calciomercato - in Italian), external

    Paris St-Germain ta fasa daukar dan wasan Atletico Madrid Julian Alvarez, sai dai dan wasan Argentina mai shekara 26 na jan hankalin Arsenal da Barcelona. (Mundo Deportivo - in Spanish), external

    An yi wa Inter Milan tayin dan wasan Manchester United Harry Maguire sai dai kungiyar ta Italiya ba ta dauki daukar dan wasan Ingila mai shekara 33 a matsayin wani abu da za ta ba fifiko ba (Gazzetta dello Sport via Football Italia), external

  17. Watakila Palace ta ɗauki Sage a matakin sabon koci, Premier League

    Ana sa ran kocin Lens, Pierre Sage, zai tattaunawa da Crystal Palace a farkon wannan mako yayin da ƙungiyar Premier League ke neman wanda zai maye gurbin Oliver Glasner.

    Palace (wanda ake yi wa lakabi da Eagles) na fuskantar kalubale a kokarin ɗaukar Andoni Iraola, wanda ake sa ran zai fara tattaunawa a hukuma da Liverpool a kwanaki masu zuwa domin maye gurbin Arne Slot da aka kore a ranar Asabar.

    Palace wadda ta lashe Conference League ta gabatar da tayin aiki mai tsoka ga Iraola, amma da alama yana kan hanyar zuwa wani wuri, yanzu Crystal Palace na duba wasu zaɓuɓɓuka daban.

    Ƙungiyar ta kudancin London, ƙarƙashin jagorancin shugaba, Steve Parish, ba zai yi gaggawa wajen yanke hukunci ba kan sabon koci, domin suna nazarin wasu sunaye daban.

    Daga cikin waɗanda ake dubawa akwai Sage, wanda ya yi suna a matsayin ɗaya daga cikin masu horarwa masu hazaka a Turai.

    BBC Sport ce ta fara bayyana sha’awar Crystal Palace ga mai shekara 47 a ranar 8 ga Mayu, amma a lokacin shugabancin Palace ya fi mayar da hankali kan ƙoƙarin ɗauko Iraola daga Bournemouth.

    Rahotanni sun ce kocin Lens ɗin da yiwuwar komawa Palace, kuma ana sa ran zai gana da jami’an ƙungiyar a cikin kwanaki masu zuwa.

  18. , Daga Jaridu

    Dan wasan Portugal Bernardo Silva, mai shekara 31, yana sha'awar komawa Barcelona ya yin da kwantiraginsa a Manchester City na gab da karewa.(Mundo Deportivo - in Spanish), external

    Brighton za ta fuskanci hamayya daga Hoffenheim da Eintracht Frankfurt wajan sayen dan wasan Wolfsburg Patrick Wimmer mai shekaru 25 .(Florian Plettenberg), external

    Crystal Palace ta sake tattaunawa da kocin Lens Pierre Sage da ake ganin yana da kwarewa sosai .(Mail), external

    Kocin Como Cesc Fabregas na jin dadin aikinsa a kungiyar Italiya duk da cewa an alakanta da shi da wasu ayuikam horas dayan wasa a wasu wurare ciki harda Real Madrid (Sport - in Spanish)

  19. Slot ya ce ya bar Liverpool a gurbin da ta dace, Liverpool

    Arne Slot ya ce ya bar Liverpool “daidai inda ya kamata ta kasance: cikin manyan ƙungiyoyin Turai” bayan da aka kore shi daga aikin koci ranar Asabar.

    Ɗan kasar Netherlands mai shekara 47 ya lashe kofin Premier League a kakar sa ta farko, amma shugabancin ƙungiyar ya yanke shawarar korarsa, bayan da Liverpool ta kare a matsayi na biyar a gasar bana, inda ta kasance da tazarar maki 25 tsakaninta da Arsenal wadda ta lashe kofin a karon farko bayan shekara 22.

    Liverpool za ta fara tattaunawa a hukumance a wannan mako da tsohon kocin Bournemouth, Andoni Iraola, kan yiwuwar ya maye gurbin Slot a matsayin sabon koci.

    A cikin wata buɗaɗɗiyar wasika mai cike da tausayi da aka buga a Liverpool Echo, Slot ya ce magoya baya sun tarbe shi cikin murna tun farko kuma sun taimaka masa wajen gudanar da aikinsa. Ya ce “Wannan abu ne da ba zan manta da shi ba,” in ji shi.

    Ya kara da cewa: “Na bar ƙungiyar da cikakken tabbaci game da abin da ke gaba.”

    “’Ƴan wasan da yawa sun yi hidima sosai, sun kiyaye darajojinsa kuma suka samar da lokuta masu ban mamaki, sun gina tushe mai ƙarfi da zai dawwama.”

    Duk da cewa Liverpool ta sha kashi sau 20 a dukkan fafatawa a bana, Slot ya tabbatar da cewa Liverpool ta samu gurbin shiga Champions League na kakar gaba.

    “Samun gurbin Champions League wani muhimmin nauyi ne kuma ya tabbatar Liverpool za ta ci gaba da fafatawa a matakin koli a kakar gaba da ma bayan haka,” in ji shi.

    “Lokacin da na fara tsayawa a matakin kociyan Liverpool, na san abin da wannan ƙungiyar ke bukata. Na kuma san cewa ba mu daina kokari ba.”

    Slot ya maye gurbin Jürgen Klopp a Liverpool a shekarar 2024 bayan kocin Jamus ɗin ya sauka daga mukaminsa bayan shekaru tara.

    Ya fara aikinsa cikin nasara sosai, inda ya jagoranci Liverpool zuwa kofin Premier League na 20, har ma da tazarar maki huɗu kafin ƙarshen kakar wasa a gaban magoya baya a Anfield.

  20. Milner ya yi ritaya bayan shekara 24 yana taka leda, Premier League

    Tsohon ɗan wasan tawagar Ingila, James Milner, ya sanar da yin ritaya daga buga ƙwallon ƙafa bayan ya shafe shekara 24 yana taka leda a gasar Premier League.

    Milner mai shekara 40, wanda ke iya taka leda a wurare daban-daban a fili, ya zauna ba tare da kwantiragi ba bayan shekara uku da suka gabata a Brighton & Hove Albion.

    A tsawon rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa, Milner ya buga ƙungiyoyi shida wasa a gasar Premier League, kuma a watan Fabrairu ya kafa tarihin ɗan wasan da ya fi kowa yawan buga wasanni a gasar.

    Ya fara sana’arsa ne ta taka leda a Leeds United, sannan ya lashe kofin Premier League sau uku – guda biyu tare da Manchester City da kuma sau ɗaya tare da Liverpool. Haka kuma ya taimaka wa Liverpool ta ɗauki gasar UEFA Champions League a shekarar 2019.

    Milner ya fara buga wa Ingila wasa a shekarar 2009 lokacin yana tare da Aston Villa, ya yi wa tawagar kasar wasa 61.

    Milner ya fara bugawa Leeds United wasa yana ɗan shekara 16 a watan Nuwamban 2002. A lokacin, shi ne ɗan wasa na biyu mafi ƙarancin shekaru da ya taba buga Premier League.

    A wata mai zuwa kuma, ya zama mafi ƙarancin shekaru da ya ci ƙwallo a tarihin Premier League. A yanzu yana matsayi na uku bayan Max Dowman da James Vaughan.

    Rauni ya sa Milner ya rasa mafi yawan wasannin a kakar 2024-25, amma ya dawo ya buga karawa 22 a dukkan fafatawa a kakar 2025-26. Wasansa na ƙarshe a Premier League ya kasance na 658, wanda ya buga a ranar ƙarshe a kakar wasa da Brighton.

    Bayan shekara biyu a babbar ƙungiyar Leeds, an sayar da shi zuwa Newcastle United bayan Leeds ta faɗa gasar Championship a shekarar 2004.

    Daga nan ya koma Aston Villa a 2008, sannan Manchester City a 2010, inda ya taimaka musu wajen lashe kofunan Premier League na farko a shekarun 2012 da 2014.

    A shekarar 2015 ya koma Liverpool, inda ya shafe shekaru takwas a filin Anfield, ya zura ƙwallaye 26 a wasa 332.

    A shekarar 2020, ya taimaka wa Liverpool lashe kofin Premier League na farko tun 1990. Haka kuma ya lashe kofin FA Cup da League Cup tare da Liverpool da Manchester City.