Bukukuwan Sallah da furanni cikin hotunan Afrika

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Wasu daga cikin ƙayatattun hotunan Afirka da na ƴan nahiyar a wasu sassan duniya.

Wata mata sanye da fafaren kaya na wucewa ta gefen hotunan shugabannin addini a Dakar babban birnin Senegal
Bayanan hoto, Wata mata sanye da fafaren kaya na wucewa ta gefen hotunan shugabannin addini a Dakar, babban birnin Senegal
Mabiya Addinin Islama da suka yi ado da fararen kaya na gudanar da a addu'o'i
Bayanan hoto, Mabiya Addinin Islama da suka yi ado da fararen kaya na gudanar da a addu'o'i ranar sallar idi a birnin na Dakar
Wani mutun akan doki lokacin hawan sallah a Dutse, ya yi kwalliya da kayan hawa tare da dokinsa
Bayanan hoto, Wani mutun akan doki lokacin hawan sallah a Dutse, ya yi kwalliya da kayan hawa tare da dokinsa
Wasu daga cikin fadawan gidan sarki sun ɗauki hoto a jikin katanga a ƙofar fadar Sarkin Dutse
Bayanan hoto, Wasu daga cikin fadawan gidan sarki sun ɗauki hoto a jikin katanga a ƙofar fadar Sarkin Dutse
Mutane na girka abinci cikin manyan tukwane kan murhun itace a Afrika ta Kudu
Bayanan hoto, Mutane na girka abinci cikin manyan tukwane kan murhun itace a Afrika ta Kudu
A Ivory Coast wata Musulma ta sanya jan kaya tana gyara hijabinta, gashin kanta a rufe ya yin shagulgulan bikin Salla
Bayanan hoto, A Ivory Coast wata Musulma ta sanya jan kaya tana gyara mayafinta yayin shagulgulan bikin Salla
Ɗaruruwan mutane sun saki balo sama bayan kammala sallar Idi a titin Sidi Bishr a birnin Alexandria dake ƙasar Masar
Bayanan hoto, Ɗaruruwan mutane sun saki balo sama bayan kammala sallar Idi a titin Sidi Bishr a birnin Alexandria da ke ƙasar Masar
Wani mutun da safar hannu riƙe da kwaɗon da girmansa ya kai na kyanwa
Bayanan hoto, Wani mutun da safar hannu riƙe da kwaɗon da girmansa ya kai na kyanwa
Tauraruwar fina-finai Alice Da Luz na fara'a ya yin da ta ke kallon wasan kwaikwayon mai tarihi
Bayanan hoto, Tauraruwar fina-finai Alice Da Luz na fara'a ya yin da ta ke kallon wasan kwaikwayon mai tarihi
Masu zanga-zanga ɗauke da kwalayen neman a yiwa Cwecwe adalci
Bayanan hoto, Masu zanga-zanga ɗauke da kwalayen neman a yi wa Cwecwe adalci
Kashegari masu goyon bayan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Al Hilal a Masar sun sanya kaya iri ɗaya kuma sun ɗaga hannaye tare don nuna goyon baya
Bayanan hoto, Kashegari masu goyon bayan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Al Hilal a Masar sun sanya kaya iri ɗaya kuma sun ɗaga hannaye tare don nuna goyon baya
Ranar Talata ƴan fafutuka da masu goyon baya sun yi dandazo a kan titi bayan sukar aniyar Tidjane Thiam ta tsayawa takarar shugabancin ƙasa a Ivory Coast
Bayanan hoto, Ranar Talata masu fafutika da masu goyon baya sun yi dandazo a kan titi bayan sukar aniyar Tidjane Thiam ta tsayawa takarar shugabancin ƙasa a Ivory Coast
Mata da Maza na motsa jiki cikin furanni a Delta Park a Afrika ta Kudu
Bayanan hoto, Mata da Maza na motsa jiki cikin furanni a Delta Park a Afrika ta Kudu