A Tribe Called Judah: Fim ɗin da ya fi kawo kuɗi a tarihin Najeriya

A Tribe Called Judah
An wallafa

Wani fim ɗin masana'antar Nollywood ta kudancin Najeriya, ya kafa sabon tarihin zama fim ɗin Najeriya na farko da ya kawo kuɗi har naira biliyan ɗaya a sinimun cikin gida.

Fim ɗin mai taken 'A Tribe Called Judah' wanda gwari-gwari za a iya fassara shi da 'Wata Al'umma Da ake Kira Judah', ya cimma wannan abin tarihi ne a cikin mako uku kawai.

Wadda ta shirya fim ɗin - jarumar fina-finai, darakta a Najeriya kuma furodusa, Funke Akindele - ta gode wa magoya bayanta saboda wannan abin tarihi.

"Na gode Allah! Na gode muku 'yan Najeriya! Na gode muku mutanen Ghana!" ta wallafa a shafinta na Instagram, wanda ya janyo taya murna daga dubban mutane.

Bajintar ta sanya Funke Akindele 'yar shekara 46, zama daraktar da ta fi samun kuɗi a masana'antar Nollywood.

Fim ɗin ya kuma fito da taurari har da na arewacin Najeriya kamar Uzee Usman.

'A Tribe Called Judah' ya kama hanyar dakushe fitattun fina-finan Hollywood, ta fuskar yawan kuɗaɗen da suke kawowa a sinimun Najeriya ciki har da fim ɗin zaƙaƙuran gwaraza mai suna Black Panther: Wakanda Forever wanda a baya shi ne ke riƙe da wannan matsayi na fim ɗin da ya fi kawo kuɗi a ƙasar.

"Wannan bajinta ba kawai ta yawan kuɗin da aka samu ba ce; wata shaida ce ga ƙwarewar iya ba da labari da alfahari da al'adu da nagartar Nollywood ta rashin miƙa wuya ga abokan gogayya," wani kamfanin samar da fina-finai, FilmOne Entertainment, ya ce a dandalin Instagram.

Ya yaba wa fim ɗin a matsayin wani "abin al'ada mai daraja".

Kamfanin ya kuma jinjina wa Funke Akindele inda ya ce ƙwazonta na iya ba da labari ya "ƙyanƙyashe wani muhimmin babi a gagarumar masana'antar sinimun Najeriya".

A Tribe Called Judah ya samu bita daga masu sharhi da 'yan kallo kuma yana samun babban matsayi a dandali daban-daban na sharhin fina-finai.

Mahaifiyar Funke Akindele ce - wadda daraktar ta sadaukar da fim ɗin gare ta -ta yi mata ƙaimi wajen shirya fim ɗin - wanda ke nuna makircin wata uwar marayu na yin fashi a wani babban kanti, tare da 'ya'yanta biyar da ke cikin matsin rayuwa.