Atletico Madrid na zawarcin Tijjani, Silva ya fi son ya koma Barcelona

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan AC Milan da Portugal Rafael Leao, mai shekara 26, na cikin jerin 'yan wasan da Manchester United ke zawarcinsu kuma za a same shi kan farashi mai rahusa bayan kungiyar ta Italiya ta kasa tsallakewa zuwa gasar zakarun Turai.(Football Insider), external
Dan wasan Portugal Bernardo Silva, mai shekara 31,zai kasan ce ba shi da kwantaragi bayan ya bar Manchester City a wannan bazara kuma Atletico Madrid da Benfica sun yi masa tayi amma ya fi son ya koma Barcelona.(Times, subscription required), external
Dan wasan Eintracht Frankfurt Jean-Matteo Bahoya, mai shekara 21, na jan hankalin kungiyoyin kwallon kafa na firmiya da Turai yayin da kungiyoyin Saudi Pro League suma suna zawarcin dan wasan na Faransa na tawagar yan kasa da shekara 21.(Sky Sports, external)
Kocin Jamus Dino Toppmoller, wanda ya bar kungiyar Frankfurt ta Bundesliga a watan Janairu, yana daya daga cikin 'yan takarar da za su maye gurbin Oliver Glasner na Austriya, mai shekara 51, a Crystal Palace.(Sky Sport - in German, external)
Aston Villa na tattaunawa da dan wasan tsakiyar Netherlands Lamare Bogarde, mai shekara 22, kan sabon kwantaragi don ya ci gaba da taka leda a kungiyar.(Football Insider), external
Tsohon kocin Bournemouth Andoni Iraola na tattaunawa da Bayer Leverkusen ta Bundesliga kan zama kocinsu.(Times, subscription required), external
Barcelona da Bayern Munich na zawarcin dan wasan bayan Manchester City da Croatia Josko Gvardiol, mai shekara 24(Goal), external
Atletico Madrid na shirin neman dan wasan Manchester City da Netherlands Tijjani Reijnders, mai shekara 27, wanda ya koma kulob din na Ingila a bazarar da ta wuce.(Daily Mail)













