Kotu ta yanke wa waɗanda suka sace ɗaliban Oyo hukunci

Asalin hoton, Attorney-General of di Federation (AGF)
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya yanke wa wasu mutane uku hukuncin ɗaurin rai da rai da aka kama bisa hannu a garkuwa da ɗaliban jihar Oyo da malamansu a karamar hukumar Oriire.
Alƙalin kotun Maishari'a Salim Ibrahim ya ce kotun ta yanke hukuncin ne bayan da suka amsa duka laifukan da ake tuhumarsu.
Kotu ta samu mutanen uku waɗanda dukansu ƴan asalin jihar Neja ne da laifukan ɓoye bayanan mutane masu alaƙa da ta'addanci, da yin garkuwa da mutane da kuma amfani da dandalin saƙonni wajen horas da ayyukan ta'addanci.
Maishari'a Salim Ibrahim ya ce mutanen uku ƴan ƙungiyar Darul Salam ne, mai biyayya ga ƙungiyar Ansaru.
A makon da ya gabata ne Babbar Kotun Tarayyar ta yanke wa wasu manyan kwamandojin ƙungiyar Ansaru da hukumar DSS ta kama hukunci.
Su wane ne mutanen?
Mutanen uku da aka yanke wa hukuncin sun haɗa da:
- Abu Khalifa/Abu Khalid
- Bin Musa
- Abu Itisar
Dukanzu mazauna ƙaramar hukumar Suleja ta Jihar Neja ne, kuma ana zarginsu da cewa sun haɗa baki da wasu mutum ukun daban a tsakanin watan Janairu da Mayu na shekarar 2026 domin yin garkuwa da ɗalibai da malamai a Jihar Oyo, wanda hukumomi suka ce ya saɓa wa Sashe na 26(1) na Dokar Hana da Takaita Ta'addanci ta shekarar 2022.
Haka kuma an zarge su da taimakawa wajen sace ɗaliban da malamai, sannan suka ɓoye bayanai game da waɗanda ake zargin su ne suka shirya harin duk da cewa suna da masaniya a kai. An ce hakan ya saɓa wa Sashe na 26(2) da Sashe na 16(1) na dokar.
Bugu da ƙari, ƙarar ta ce a ranar 2 ga Yuni, 2026, mutanen ukun sun bayyana kansu a matsayin mambobin Darul Salam, wata ƙungiya da ake zargin tana da alaƙa da Ansaru (Jama'atu Ansarul Musulmina Fi Biladis Sudan), wadda gwamnatin Najeriya ta haramta saboda ayyukan ta'addanci. Ana zargin hakan ya saɓa wa Sashe na 25(1) na Dokar Ta'addanci.
A wasu tuhume-tuhume na daban, an zargi ɗaya daga cikin su da horas da ƴanta'adda ta hanyar buɗe zauren WhatsApp mai suna "The Oneness of Allah is the Foundation of Peace", da kuma tunzura mambobinta su aikata ayyukan ta'addanci. An ce waɗannan laifuka sun saɓa wa Sashe na 15 da Sashe na 2(2)(g) na Dokar Ta'addanci ta 2022, da kuma Sashe na 18 na Dokar Laifukan Yanar Gizo (Cybercrime Act) ta shekarar 2015.
Tuhuma ta goma kuma ta zargi ɗaya daga ciki da haƙar zinari ba tare da izini ba a ramukan yankin Chaza da ke ƙaramar hukumar Suleja tsakanin shekarun 2024 da 2026.
DSS ba ta gamsu da hukuncin ba
A nata ɓangare hukumar tsaro ta DSS a Najeriya ta ce za ta ɗaukaka kara game da hukuncin da kotu ta yanke wa wasu mutum uku da aka samu d alaifin hannu a sace ɗaliban jihar Oyo.
Hukumar ta DSS, wadda ta gurfanar da mutanen ta ce hukuncin da kotun ta yanke musu ya yi kaɗan idan aka kwatanta da laifin da suka aikata.
Hukumar ta kafa hujja da kisan malaman makarantar biyu da masu garkuwar suka yi lokacin da suke hannunsu.
Yadda aka kuɓutar da ɗaliban
A baya-bayan nan ne rundunar sojin Najeriya ta ce ta ceto dukkan ɗalibai da malamai su 44 da aka sace kimanin wata biyu da suka gabata daga makarantu a jihar Oyo da ke, sannan ta ce an kama wasu daga cikin masu garkuwar.
Rundunar sojin ta kuma bayyana cewa wasu daga cikin sojojinta sun rasa rayukansu yayin gudanar da aikin ceton.
Sace ɗaliban na Oyo ya matuƙar ɗaukar hankali, inda har fitaccen mawaƙin Najeriya Davido ya isar da batun zuwa duniya bayan ya taka rawa a raƙashewar share fagen Gasar Kofin Duniya sanye da riga mai ɗauke da sunan ɗaliban.
Matakin nasa ne ya haifar da zazzafar muhawara tsakaninsa da fitaccen mawaƙin siyasa, Dauda Kahutu Rarara a kafofin sadarawa.
Yadda aka sace ɗaliban
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A ranar 15 ga Mayun 2026 ce wasu mahara masu ɗauke da makamai suka kai hari makarantu uku da ke ƙaramar hukumar Oriire a jihar Oyo, inda suka yi garkuwa da ɗalibai, malamai da ƙaramin yaro.
Maharan sun isa yankin ne a kan babura, inda suka kai hare-hare lokaci guda kan makarantu uku a Yawota da Ahoro-Esinele.
Makarantun da aka kai wa hari su ne
- Baptist Nursery and Primary School, Yawota;
- Community High School, Ahoro-Esinele;
- L.A. Primary School, Ahoro-Esinele
Sun isa makarantun ne ana tsaka da karatu, inda suka riƙa harbe-harbe kafin su kutsa cikin ajujuwa. Wani malami ya shaida wa BBC cewa yara sun riga sun zauna a cikin aji lokacin da harin ya fara, kuma maharan suka tafi da su ba tare da wata turjiya ba.
Masu garkuwar sun sace yara ƙanana har masu shekaru biyu, tare da malamai da kuma wani ƙaramin yaro wanda yake tare da ɗaya daga cikin malaman da aka sace.
A yayin harin, mutane biyu sun mutu: wani mutum da aka harbe bayan maharan sun yi zargin yana binsu, da kuma wani malami da aka kashe nan take a wurin harin.
Sace ɗalibai daga makarantu ya fara zama ruwan-dare a Najeriya ne tun bayan sace ƴan matan makarantar Chibok da ƙungiyar Boko Haram ta yi a shekarar 2014, inda aka sace ɗalibai mata kusan 276.
Lamarin ya faru ne ƙasa da shekara guda bayan wasu manyan hare-haren sace ɗalibai, ciki har da sace kusan yara 100 daga wata makarantar Katolika a jihar Neja a ƙarshen shekarar 2025, da kuma sace ƴan mata 25 daga makarantar mata ta Government Girls Comprehensive Secondary School a jihar Kebbi.












