Bikin sabuwar shekara da rantsar da shugaban Mozambique cikin hotunan Afrika

    • Marubuci, Natasha Booty
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Wasu daga cikin zaɓaɓɓun hotunan Afrika na wannan makon

A man smiles and lies on top of a huge mound of fluffy, picked cotton.
Bayanan hoto, Ranar Litinin, Ange Gnacadja mai sahekara 31 ya kwanta kan audugar da aka girbe a yankin Soclogbo na Jumhurriyar Benin
People in running gear and with numbers attached to their chests jog on a road. Hot-air balloons rise in the background.
Bayanan hoto, Ranar Asabar aka gudanar da gudun famfalaƙi na a birnin Luxor na ƙasar Masar
A man dressed in loose clothing shows off his moves while others watch seated.
Bayanan hoto, Ranar Lahadi, masu rawa sun fafata a gasar rawa ta Juste Debout ,a Birnin Tunis na ƙasarTunisia
A person dives from a springboard during a hot summer day at Sea Point swimming pool in Cape Town, South Africa, January 10, 2025.
Bayanan hoto, Wani mai ninƙaya ya shirya yin nitso a birnin Cape Town na ƙasara Afrika ta kudu ranar Asabar
A woman wearing a tasselled red, green and yellow headdress smiles.
Bayanan hoto, A ranar Litinin ne alummomin ƙabilar Amazigh guda 2975 da ke nahiyar Afrika suka yi bikin sabuwar shekara
Women play tambourines and sing.
Bayanan hoto, Bukukuwan da aka yi a birnin Rabat na ƙasar Morocco sun haɗa da baje kolin kayan sa wa da kuma wake-wake
A man rides a motorbike along a road that is scarred with huge cracks across it.
Bayanan hoto, Girgizar ƙasa ta lalata tituna a yankin arewacin Habasha, kuma hakan na kawo wa wannan mutumin cikas yayin da ya ke ƙokarin safarar kaya ranar Litinin
A women dressed in a trilby, shirt and chef's waistcoat smiles infront of luxurious wallpaper and lighting.
Bayanan hoto, An ɗauki hoton Shararariyar mai dafa abincin nan Georgiana Viou a Ranar Lahadi yayin da ta bar ƙasaitaccen wurin cin abincin da ta ke a Faransa ta buɗe wani sabon wuri da ake kira Restaurant L'Ami a Jumhurriyar Benin
People wearing matching clothing sing and dance in procession. Behind them is a pink wall which is painted with symbols in turquoise and black.
Bayanan hoto, Har ila yau dai a Benin, mabiya addinin Vodún sun nufi fadar sarki Kpodégbé Lanmanfan Toyi Djigla...
A person dances in circles wearing a huge swirling costume of long purple tassels,
Bayanan hoto, Rawar 'Zangbetos' na ɗaya daga cikin abubuwan da aka saba gani a lokacin bikin Vodún
A man dressed in white poses for a portrait in a darkened room.
Bayanan hoto, Wannan mabiyin na addinin Vodun ya tsaya a ɗauke shi hoto a ɗakin Ibadar Mami Wata da ke yankin Ouidah
A woman pickets the mine in Stilfontein with a sign that reads: '"Stilfontein is the next Marikana".
Bayanan hoto, Ƴan Afirka ta Kudu sun nuna bacin ransu da gwamnati inda suka ce alhakin kisa ya rataya a wauyarta bayan ta yi jinkiri na watanni kafi zakulo masu haƙar ma'adinai da suka maƙale a ƙarƙashin ƙasa tun watan Nuwamba. Wasu na kwatanta badaƙalar da kisan kiyashin da aka yi a hakar ma'adinai ta Marikana a shekarar 2012
A man in tattered clothing is stretchered away.
Bayanan hoto, Akasarin waɗanda suka tsira sun kwashe kwanaki babu abinci, lamarin da ya Sanya sai da ka ɗauke su a gidajen ɗaukar marasa lafiya domin basu da ƙarfin da za su iya tafiya ta ƙafafunsu.
People stand crowded into a darkened makeshift home. They have very few belongings. Many are children.
Bayanan hoto, Wannan yaron da Iyalai da dama da ke kewaye da shi na cikin sama da mutane 100,000 da suka tsere daga gidajensu a yankin Masassi a gabashin jumhurriyar Dimokradiyyar Kowngo, a cikin makon da ya gabata sakamakon rikici tsakanin ƙungiyar ƴan tawaye ta M23 da sojin ƙasar.
A general view of water bottles with stickers on of Mozambique President-elect Daniel Chapo.
Bayanan hoto, A bikin rantsar da sabon shugaban Mozambique Daniel Chapo an rarrabawa mutane abubuwan sha da aka buga hotunansa a kai.
A woman draped in the Mozambique flag squares up to a line of armed policemen and shouts slogans near the Independence Square during the inauguration of Mozambique's fifth president, Daniel Chapo, in Maputo.
Bayanan hoto, Kuma a wannan ranar masu zanga-zangar sukar sakamakon zaɓe, waɗanda basu amince da Chapo a matsayin shugaban da aka zaɓa ba sun yi wani gangamin nuna rashin amincewarsu
A woman looking at her mobile phone and the graphic BBC News Africa

Go to BBCAfrica.com for more news from the African continent.

Follow us on Twitter @BBCAfrica, on Facebook at BBC Africa or on Instagram at bbcafrica