Mece ce gaskiyar shekarun Mahmud Buba da aka fi sani da Abin Al'ajabi?

Abin Al'ajabin Zazzau
Bayanan hoto, A hirarsa da BBC Hausa, Mahmud Buba ya shaida wa kafar cewa shekarunsa sun wuce 25
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Mahmoud Sadis Buba, wanda aka ake yi wa laƙabi da abin 'Abin al'ajabi' wani matashi ne daga jihar Kaduna, wanda ya ja hankalin mutane da dama bayan an tace shi a matsayin mai neman tsayawa takarar ɗan majalisar wakilan tarayya ƙarƙashin jam'iyyar APC a babban zaɓen Najeriya na 2027.

Matashin ɗan siyasar ya ɗauki hankali mutane a shafikan sada zumunta sanadiyyar matakin da ya ɗauka na tsayawa takarar.

Ya ce hatta shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ƙarfafa masa gwiwar yin takara.

A hirar da matashin ya yi da BBC a makon da ya gabata, Mahmud Buba ya bayyana wa kafar cewa shekarunsa "sun fi 25" wanda hakan zai ba shi damar tsayawa takarar kujerar majalisar wakilai bisa doka.

Sai dai kuma bayan tattaunawar, muhawara ta kaure a kafafen sada zumunta kan asalin shekarun matashin, wanda fitowarsa takarar ɗan majalisar wakilan tarayyar Najeriya ta ɗauki hankali a faɗin ƙasar.

Wasu takardu sun riƙa yawo a shafukan sada zumunta da ke iƙirarin cewa shekarun matashin ba su kai yadda ya bayyana ba, inda wasu rahotannin ke bayyana cewa har yanzu yana karatu ne a matakin sakandare.

Yaushe aka haifi Mahmud Bello?

BBC ta nuna wa wani jam'in shigi da fici hoton fasfo ɗin da ake zargin na Mahmud ne da ke yawo a soshiyal midiya domin tantance gaskiyar al'amarin, inda bayan binciken da ya gudanar ya bayyana cewa "fasfo ɗin na gaskiya ne".

Bugu da ƙari, BBC ta tattauna da wani abokin mahaifin Mahmud Buba wanda ke zaune a garin na Zaria wanda ya ce "zan fi yarda da shekarun da ke takardun da ke yawo a soshiyal midiya ɗin."

"Ni abokin mahaifinsa ne kuma shekarunmu ma kusan ɗaya wato kamar 40 da kaɗan. Kuma ai a 2009 aka yi auren mahaifiyarsa," in ji abokin mahaifin Mahmud.

Wane mataki na karatu Mahmud yake?

A wani ɓangare na hirar da Mahmud Buba ya yi da BBC Hausa da ba ta saka ba akwai inda 'Abin al'ajabi' ke cewa "na yi rashin lafiya sai na daina zuwa makaranta amma kuma daga baya na koma."

To sai dai wani malamin makarantar 'Demonstration' da ke Zaria, ya ce Mahmud ɗalibinsu ne.

"E haƙika ɗalibinmu ne kuma yana SS1 amma dangane da shekarunsa ban sani ba saboda ba ni ne form master ɗinsa ba," in ji malamin.

Me Mahmud Buba zai ce?

Kalli abubuwan da ke faruwa
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo

BBC ta yi ta ƙoƙarin samun Mahmud domin jin martaninsa dangane da takardun da ake yaɗawa da ke musanta shekarunsa na haihuwa kamar yadda shi da kansa ya yi iƙirari sai dai abin ya ci tura kasancewar bai ɗauki kiraye-kirayen waya ko kuma saƙonnin da aka tura masa ba.

Wane ne Mahmoud Sadis Buba?

An haifi Mahmoud Sadis Buba ne a garin Zaria na jihar Kaduna, arewacin Najeriya.

A cikin wani faifan bidiyo da ke nuna lokacin da ake tantance, Mahmoud ya bayyana shekarunsa a 30, sai dai a tattaunawar da ya yi da BBC, ya ce "aƙalla ya wuce shekarun tsayawa takara, wato 25".

Ya fito ne daga gundumar Sabon Gari a jihar Kaduna, kuma shi ne ɗa na farko a wurin mahaifinsa.

Ya bayyana cewa ya gaji rashin tsawo ne daga wurin kakansa da kuma mahaifinsa.

A tattaunawarsa da BBC ya bayyana cewa yana tallafawa da kuma kula da mutane da dama, kuma shi ɗan kasuwa ne, wanda ya mallaki shaguna da kuma baburan haya.

Ya yanki takardar neman tsayawa takara domin wakiltar gundumar Sabon Garin jihar Kaduna a majalisar wakilan tarayya a zaɓen shekara ta 2027.