Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wakilan Tonali sun tuntuɓi Real Madrid, Liverpool da Man U na zawarcin Diomande
Ƙungiyar Everton na bibiyar halin da kwantiragin ɗan wasan tsakiya na Ingila John Stones yake ciki a Manchester City, bayan rahotanni sun nuna cewa ba a sa ran ba shi sabon yarjejeniya. Stones mai shekara 31 ya taɓa taka leda a Everton. (Talksport)
A wani bangare kuma, wakilan ɗan wasan tsakiya na Italiya Sandro Tonali sun tuntubi Real Madrid yayin da suke neman sabuwar ƙungiya ga ɗan wasan mai shekara 25. Haka kuma Manchester City na cikin ƙungiyoyin da ke sha'awar ɗan wasan na Newcastle United. (Teamtalk)
Ƙungiyar Barcelona ce ke kan gaba wajen neman ɗan wasan tsakiya na Portugal Bernardo Silva mai shekara 31 daga Manchester City kyauta a lokacin bazara. (The Sun)
Arsenal na bibiyar matashin ɗan wasan gaba na Bayer Leverkusen Christian Kofane mai shekara 19, inda ƙungiyar ta Jamus ke neman kusan fam miliyan 60 domin sayar da shi. (Florian Plettenberg)
Zaɓin sayen ɗan wasan gaba na Ingila Marcus Rashford da Barcelona ke da shi na fam miliyan 26 ya ƙare a watan Maris, wanda ke nufin dole ne yanzu su tattauna kai tsaye da Manchester United kan farashinsa. (Cadena SER)
Kungiyoyin Manchester City da Liverpool da Chelsea na sa ido kan ɗan bayan Faransa Jules Kounde mai shekara 27 wanda ke taka leda a Barcelona. (Mundo Deportivo)
An sanar da aniyar cefanar da ɗan bayan Netherlands Denzel Dumfries mai shekara 29 ga kungiyoyin gasar Premier League ciki har da Liverpool, Manchester City, Manchester United, Chelsea, Tottenham Hotspur da Newcastle United. (Teamtalk)
Manchester United na sha'awar ɗan bayan Sweden Samuel Dahl mai shekara 23 daga Benfica, inda kungiyar ta tura wakilanta suna kallon murza ledar dan wasan sau fiye da 10 a wannan kakar. (Record/SportWitness)
Celta Vigo na son ɗan wasan tsakiya na Spain Fer Lopez mai shekara 21 ya ci gaba da zama a ƙungiyar bayan karewar aro daga Wolverhampton Wanderers. (Faro de Vigo/SportWitness)
Mai horarwa Roberto De Zerbi na son sayo ɗan wasan tsakiya na Italiya Manuel Locatelli mai shekara 28 daga Juventus don taka leda a Tottenham Hotspur a lokacin bazara. (Calciomercato)
A ƙarshe, Manchester United da Liverpool na zawarcin ɗan wasan gefe na Ivory Coast Yan Diomande mai shekara 19 daga RB Leipzig. (Sportsboom)