Ɓarnar da girgizar ƙasa ta yi a Morocco cikin hotuna

An wallafa

Mummunar girgizar ƙasar da ta faru a kudancin Morocco, wadda ta hallaka dubban mutane, kuma ta lalata wuraren tarihi da yawa a Marrakesh.

Yanayin ya tilastawa 'yan wayon buɗe ido da dama da mutanen gari kwana a filin Allah-Ta'ala, saboda tsoron kada girgizar ta ci gaba.

fg
Bayanan hoto, Wata mata na duba ɓarnar da girgizar ƙasar ta yi a Marrakesh a dare Juma'a.
fg
Bayanan hoto, Ɓurbishin wani gini mai tarihi da ya zubo kan wata mota, kuma abin ya rutsa da mutane masu yawa da lalata ababan hawa.
fg
Bayanan hoto, Ɓarnan da girgizar ƙasar ta yi wa gine-gine ba su bayyana ba sai da gari ya waye a ranar Asabar
fg
Bayanan hoto, Gine-gine da dama sun ruguje, abin da ya bar masu su cikin zullumi
fg
Bayanan hoto, Girgizar kasar wadda ta kai maki 6.8 ta yi ƙamari ne a yankin Atlas Mountain mai nisan ƙasa da mil 50 daga cikin birni.
fg
Bayanan hoto, Mutane a Marrakesh sun riƙa bayar da taimakon jini da ɗaruruwan jama'ar da musufar ta shafa
fg
Bayanan hoto, Da yawan mazauna birnin sun kwana ne a waje saboda fargabar abin da zai iya biyo bayan girgizar ƙasar
fg
Bayanan hoto, Gwamman mutane sun yi barci a kusa da wajen wanka da ke cikin totel a ɗaya daga cikin manyan otal ɗin yankin
Bayanan bidiyo, Yadda girgizar ƙasa ta lalata masallacin Kutubiyya