Mece ce hujjar Trump kan iƙirarin haɗa miyagun ƙwayoyi a cibiyoyin nukiliyar Iran?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi ikirarin a karon farko a wani jawabin yaƙin neman zaɓensa da ya gabatar a Durant, jihar Oklahoma, cewa cibiyoyin nukiliyar Iran da jiragen saman B-2 na Amurka suka kai wa hari ana amfani da su ma wajen haɗa miyagun ƙwayoyi. Sai dai bai gabatar da wata hujja da ke tabbatar da wannan ikirari ba.

Yayin da yake tuna harin da Amurka ta kai kan waɗannan cibiyoyi, Mista Trump ya ce bama-baman sun shiga cikin abin da ya kira "masana'antun miyagun ƙwayoyi", yana mai jaddada cewa wuraren "na nukiliya ne kuma na miyagun ƙwayoyi." Daga baya ya riƙa kiran su da suna "masana'antun miyagun ƙwayoyi/nukiliya".

Wannan ne karo na farko da Trump ya danganta hare-haren da Amurka ta kai wa cibiyoyin nukiliyar Iran da batun samar da miyagun ƙwayoyi.

Babu wani jami'in gwamnatin Amurka ko wata majiya mai zaman kanta da ake ganin abin dogaro ce da ta ce ana amfani da cibiyoyin nukiliyar Iran da aka kai wa hari wajen samar da miyagun ƙwayoyi.

Shugaban na Amurka ya kuma sake bayyana a Denton, jihar Texas, cewa Amurka "ba ta da wani zaɓi" illa ɗaukar mataki a kan Iran domin, a cewarsa, ƙasar na gab da mallakar makamin nukiliya.

Ya yi ikirarin cewa Iran saura makonni kaɗan ta samu irin wannan makami, ikirarin da ya yi sau da dama a baya.

'Iran na iya miƙa wuya a kowane lokaci'

Daga nan Trump ya tashi daga Texas zuwa Durant a Oklahoma, inda ya gudanar da gangamin goyon bayan 'yan takarar Jam'iyyar Republican.

Wannan ziyara wani ɓangare ne na yaƙin neman zaɓensa gabanin zaɓukan tsakiyar wa'adi na watan Nuwamba.

A wata hira dabam da gidan talabijin na News9 na Oklahoma, Trump ya ce Iran "na iya miƙa wuya a kowace rana", tare da sake jaddada cewa ba zai bari ƙasar ta mallaki makamin nukiliya ba. Ya kuma ce yana sa ran farashin mai zai ragu bayan yaƙin ya ƙare.

Tun bayan fara yaƙin, Trump ya sha bayyana cewa manufar farmakin da Amurka ta ƙaddamar ita ce lalata ƙarfin nukiliya da na sojan Iran.

Fadar White House ta bayyana aikin soja mai suna "Epic Fury" a matsayin martani ga ƙarfin makamai masu linzami da kuma barazanar soja daga Iran.

Sabbin kalaman Trump a Oklahoma sun zo ne kwana guda bayan mujallar Time ta wallafa wata doguwar hira da shi, inda ya ce tsawaita yaƙin da Iran ya samo asali ne daga shawarar da shi kansa ya yanke.

Trump ya ce zai iya dakatar da farmakin bayan jiragen B-2 sun kai hari kan cibiyoyin nukiliyar, amma ya zaɓi ci gaba da shi domin ba ya son Iran ta sake farfaɗo da ayyukanta a wurin ko kuma a wani wuri dabam.

Batun lalata nukiliyar Iran

A cikin wannan hirar, ya sake yin ikirarin cewa ya lalata ƙarfin nukiliyar Iran da rundunar ruwanta da rundunar sama da kuma tsarin radarta.

Ya kuma ce Iran na son cimma yarjejeniya, amma shi yana neman "yarjejeniya ta haƙiƙa".

Haka kuma, Trump bai janye daga barazanar da ya yi a baya ta "lalata Iran" a hirarsa da mujallar Time ba.

Lokacin da aka tambaye shi ko yana nufin gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ne ko kuma ƙasar Iran gaba ɗaya, bai bayar da amsa kai tsaye ba, sai dai ya koma magana kan yadda aka murƙushe zanga-zangar adawa a Iran.

Har ila yau, bai kawar da yiwuwar ƙara tsananta hare-haren bam a kan Iran bayan zaɓukan tsakiyar wa'adi na Amurka ba. Da aka tambaye shi game da hakan, ya ce: "Mai yiwuwa ne."

A baya ma shugaban Amurkar ya yi magana kan yiwuwar "rushe Jamhuriyar Musulunci ta Iran" a jawabinsa na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya, yana kwatanta hakan da yiwuwar cimma yarjejeniya da Tehran.