Su wane ne ƙungiyoyin Premier da suka samu tikitin gasar Zakarun Turai ta baɗi?

Asalin hoton, Getty Images
Ana tashi daga wasannin da aka yi a filayen wasa 10 a ranar Lahadi, aka kawo karshen kakar Premier League ta bana mai cike da armashi da ƙalubale da kuma takaici.
Ƙungiyar Arsenal ce ta kammala kakar a matsayin wadda ta lashe kofin a karon farko cikin shekara 22, abin da ya dawo da farin ciki ga magoya bayanta bayan dogon lokaci.
A gefe guda, West Ham United da ta fuskanci koma baya a kakar, ta doke Leeds United da ci 3-0, amma hakan bai hana ta faɗuwa daga Premier League ba, inda za ta buga Championship a kakar mai zuwa ta 2026–27.
Haka kuma, ƙungiyoyi irin su Burnley da Wolverhampton Wanderers su ma za su bi West Ham zuwa mataki na komawa buga gasa mai darja ta biyu a Ingila, bayan kasa yin abin kirki.
Sai dai ba barin gasar Premier League ne ya fi ja hankali ba, neman tikitin shiga gasar zakarun Turai ta Champions League da Europa da kuma Conference League shi ma ya dauki hankula.
Karshen kakar bana ta zo da abubuwa masu ban mamaki—da suka haɗa da lashe kofin bana, bayan dogon zangon jira daga Gunners da gurbin Europa da kuma Conference League.
Su wane ne suka samu gurbin Champions League?

Asalin hoton, Getty Images
Kafin a fara wasanni 10 a ranar karshen ta gasar Premier League a ranar Lahadi, Arsenal wadda tun saura wasa guda ta lashe kofin a hukumance ta samu tikitin shiga gasar Champions League a baɗi tare da Manchester City da kuma Manchester United.
Haka kuma, Aston Villa ta samu tikitin Champions League bayan ta koma matsayi na huɗu ta haye kan Liverpool wadda ta kare gasar a matsayi na biyar.
Sai dai saboda nasarar da Villa ta samu a Europa League a ranar Laraba, hakan ya bai wa kungiyoyin Ingila damar samu gurabe biyar a kakar Champions Lig.
Daga ƙarshe, nasarar da Villa ta yi 2-1 kan Manchester City a ranar Lahadi ta kawo ƙarshen dukkan jita-jitar samun guraben shida, tare da tabbatar da cewa ƙungiyoyi biyu ne za su buga Europa League a kakar mai zuwa daga Ingila.
A karshe, Arne Slot na Liverpool ne ya samu tikitin karshe, kuma na biyar da zai kai su Champions League a shekara mai zuwa, yayin da Bournemouth za ta fafata a Europa League.
Su wane ne za su je Europa kaka mai zuwa?

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Bayan Aston Villa ta samu maki uku a kan City, an rage damar zuwa gurabe biyu na gasar Europa League, inda ƙungiyoyi hudu suka shiga takarar matsayi daya da ya rage.
Bournemouth ta riga ta samu tikitin gasar zakarun Turai a karon farko a tarihinta bayan kunnen doki da ta yi da Manchester City a wasan da suka yi na tsakiyar mako a lokacin. Sai dai canjaras din ranar karshe wato Lahadi da ta yi da Nottingham Forest ya sa ta kammala kakar a matsayi na shida.
Wannan ya sa fafatawar neman gurbin Europa daya da ya rage ta zama tsakanin Brighton & Hove Albion, Chelsea, Brentford da Sunderland.
Abin mamaki, shi ne Sunderland—wacce ba a yi mata zaton samun gurbin ba saboda nisan da ta yi da shi, sai kuma gashi ta samu tikitin cikin ruwan sanyi.
Sunderland ta samu wannan damar bayan doke Chelsea da ci 2-1, yayin da Brighton ta sha kashi a gida a hannun Manchester United, sannan Brentford ta yi kunnen doki a Anfield, wanda hakan ya sa Sunderland ta tashi daga matsayi na goma zuwa na bakwai a teburin Premier League.
Wannan nasara ta sa Sunderland ta zama daya daga cikin ƙungiyoyi 10 a tarihin Premier League da suka samu shiga gasar Zakarun Turai a kakarsu ta farko a gaar, bayan zuwa Premier daga Championship a shekarar farko.
Ƙungiyar da Regis Le Bris ke jan ragama ta shiga sahun ƙananan ƙungiyoyin da suka yi irin wannan bajinta a tarihi, tare da Wolverhampton Wanderers wadda ta yi hakan a kakar 2018–19.
A gefe guda, Crystal Palace za ta bi sahun Bournemouth da Sunderland a Europa League idan ta doke Rayo Vallecano a wasan karshe na gasar Conference League a ranar Laraba 27 ga Mayu.
Conference League fa?

Asalin hoton, Getty Images
Akwai gurbi guda ɗaya kacal a gasar UEFA Conference League a kakar 2026–27, kuma wanda ya ƙare gasar a matsayi na takwas ne a teburin Premier League, zai samu wannan dama mai muhimmanci.
Kamar yadda aka yi a fafatawar neman gurbin Europa League, ƙungiyoyi huɗu—Chelsea, Brighton & Hove Albion, Brentford da kuma Sunderland—duk suna da damar ƙarewa a matsayi na takwas kafin a buga wasan karshe ranar Lahadi.
Sai dai Chelsea ta yi rashin nasarar da ci 2-1 a hannun Sunderland, ya jefa ta zuwa matsayi na 10, wanda shi ne matsayi mafi muni a tarihinta na kasa ƙwazo tun kakar 2022–23.
A gefe guda, Brighton ce ta ci gajiyar wannan matakin na wakiltar Ingila a gasar Zakarun Turai a baɗi, duk da cewa koma baya ta samu, domin kafin wasan tana mataki na bakwai a teburin gasar.
Ko da yake Brighton ta sha kashi da ci 3-0 a hannun Manchester United, saboda haka rashin nasarar Chelsea a Sunderland da kuma Brentford da ta raba maki a Anfield ya ba Brighton damar tsallaka wa zuwa matsayi na takwas a teburin.
Wannan ya tabbatar wa Brighton tikitin shiga Conference League a karon farko a tarihinta.
Ƙungiyar da aka fi sani da "Seagulls" ta riga ta shiga gasar Zakarun Turai a 2023 bayan ta kare a matsayi na shida a Premier League, amma yanzu za ta fara buga Conference League a karon farko a kakar wasa mai zuwa.











