Bikin ƙona haramtattun makamai da mai sayar da aswaki a hotunan Afirka

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Ƙayatattun hotunan Afirka da na ƴan nahiyar a wasu sassan duniya cikin makon da ya gabata

Wata mata a bakin teku tana diban ciyawa
Bayanan hoto, Nan wata mata ce ke dibar ciyawar teku a Zanzibar, da ke kasar Tanzania
Wasu matasa da tabarau a zaune
Bayanan hoto, Wasu matasa maza 'yankwalisa da suka halarci kallon gasar wasa da keke a garin Alabama na Afirka ta Kudu ranar Asabar
Wata mata na rawa
Bayanan hoto, A wannan rana ta Asabar ne dai a birnin Durban na kasar ta Afirka ta Kudu mawakiya MaWhoo ta yi wasa, a bikin ranar Matasa ta Duniya. An ware ranar 16 ga watan Yuni na kowace shekara a kasar domin tunawa da dalibai bakar fata da 'yansanda suka kashe lokacin zanga-zangar birnin Soweto a 1976, lamarin da ya haifar da gagarumin sauyi a gwagwarmayar yaki da mulkin wariyar launin fata.
Mata biyu na waka da rawa
Bayanan hoto, Shahararriyar mawakiyar kasar Benin Angelique Kidjo tare da mawakiyar Brazil Flavia Coelho a wani biki a kudancin Faransa ranar Lahadi.
Hoto
Bayanan hoto, Iska mai karfi ta rura tare da yada gobarar daji a birnin Cape Town, na Afirka ta Kudu, ranar Lahadi.
Wani mutum ya rufe kansa yayin da yake kwallo da gwamgwanin hayaki mai sa hawaye
Bayanan hoto, 'Yansanda sun rika harba hayaki mai sa hawaye a titunan babban birnin Kenya, Nairobi, lokacin zanga-zangar zarginsu da kashe wani mai yada bayanai ta intanet Albert Ojwang, mai shekara 31a lokacin da yake tsare a hannunsu.
Wani mutum sanye da tabarau yana waya
Bayanan hoto, Wani mai goyon bayan Al-Ahly, ta Masar, na yake bayan kungiyarsu ta sha kashi 2-0 a hannun Palmeiras ta Brazil, a gasar cin kofin duniya na Kungiyoyi, ranar Alhamis. Rashin kyawun yanayi ya sa aka dakatar da wasan tsawon miti 40, kafin a dawo a ci gaba.
Wani dan kowa a saman shingen karawa
Bayanan hoto, A ranar Juma'a ne a Legas, Richard Muzaan na Najeriya ya doke takwaransa na Burkina Faso Israël Mano, inda ya ci kambin damben MMC na marassa nawi na Afirka.
Wani mutum na kallon zane-zane
Bayanan hoto, Shahararren marubuci da kuma zane-zane na Moroko Tahar Ben Jelloun na kallon wasu daga cikin zane-zanensa a dakin adana kayan tarihi na Mohammed VI a Rabat ranar Talata.
Wani mutum a tsaye ya sa hannu a aljihu
Bayanan hoto, Mai zane-zane Gideon Appah, dan kasar Ghana ya tsaya a kusa da wasu daga cikin zanen da ya yi da aka yi holinsu a Faransa a ranar Litinin.
Wasu sojoji biyu sun juya yayin da ake kona makamai
Bayanan hoto, Jami'an tsaron Kenya na kallon yadda ake kone haramtattun makamai 7,000 da aka kwace daga bata-gari.
Fafaroma Pope Leo XIV, tare da wasu manyan limaman cocin
Bayanan hoto, Fafaroma Leo na 14, yana ganawa da babban limamin Katolika na Madagascar a fadar Vatican ranar Litinin.
Wata mata na nuna adonta
Bayanan hoto, Masu yawon bude idanu na China na ziyartar wajen kwaikwayon fitaccen birnin na na Moroko Chefchaouen, wanda aka yi a China.
Wata mai sayar da aswaki
Bayanan hoto, A ranar Juma'a ke nan wata mata na sayar da aswaki a babban birnin Togo, Lomé.