Inter Miami na zawarcin Vozinha, Arsenal na son Mora

Asalin hoton, Reuters
Arsenal ta mayar da hankali kan ɗan wasan Aston Villa da Ingila Morgan Rogers mai shekara 23, kuma tana son ta sayi ɗan wasan daga Aston Villa (The Athletic, external).
Liverpool ta yi tambaya kan yiwuwar ɗaukar matashi, ɗan wasan ƙasar Mexico, Gilberto Mora, mai shekara 17 daga ƙungiyar Tijuana. (El Universal, external).
Everton na son daukar ɗan wasan Ingila Djed Spence mai shekara 25, daga Tottenham (The Athletic, external).
Tottenham na shirin gabatar da tayin fam miliyan 85 domin ɗaukar ɗan wasan Faransa Junior Kroupi mai shekara 19, daga Bournemouth.(TalkSport, external).
Inter Miami na zawarcin mai tsaron ragar ƙasar Cape Verde Vozinha mai shekara 40, bayan da ƙungiyar Chaves da ke mataki na biyu a Portugal ta sallame shi. (Marca, external).
Chelsea na shirin bai wa ɗan wasan Ingila Jesse Derry mai shekara 18, sabon kwantiragi domin dakile sha'awar da Bayern Munich ke nuna masa.(Football Insider), external.
Ipswich Town, wadda ta koma babbar gasa, na son kammala ɗaukar ɗan wasan Brazil Emersonn mai shekara 21 daga Toulouse a kan kuɗin da zai zama mafi tsada a tarihin siyan 'yan wasa na ƙungiyar. (Give Me Sport), external.
Paris Saint-Germain ta fara tattaunawa domin ɗaukar ɗan wasan Faransa Maghnes Akliouche mai shekara 24, daga AS Monaco. (RMC Sport, external).














