Me ya sa ƙasashen Afirka ke rashin nasara a mintunan ƙarshe?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Ibrahim Yusuf Mohammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Journalist
- Aiko rahoto daga, Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Sau biyu, a Gasar Kofin Duniya ta 2026, magoya bayan tawagogin Afirka suka sha mamaki a mintunan ƙarshe na karawar da suka yi da abokan hamayya.
Mutane da dama ba za su manta yadda Senegal ta jefa magoya bayanta cikin takaici ba, bayan ta ɗanɗana musu zuma a baki, sannan a ƙarshe ta ba su kunya mintuna ƙalilan kafin a tashi wasa.
An kai minti 80 Senegal na gaba da ci 2, amma a ƙarshe ta sha kashi hannun Belgium da ci 2-3.
Kafin raunin da Senegal ta yi wa zukatan magoya bayanta ya warke, sai Masar ta ƙara zuba gishiri a gyambon.
Bayan ta girgiza duniyar ƙwallo ta hanyar jefa ƙwallo biyu a ragar mai riƙe da kofi Argentina, Masar ta watsa wa masu kallo ƙasa a ido, inda ta yi rashin nasara da ci 2-3.
To amma me ya haifar da hakan?
Wannan tuntuɓe da ƙasashen Afrika ke yi a mintunan ƙarshe na wasanni ya sa masana da masu sharhi suna ƙoƙarin fahimtar dalilan da ke haddasa hakan.
Dalilan da ya sa ƙasashen Afrika ke tuntuɓe a ƙarshen wasanni

Asalin hoton, Getty Images
Wannan lamari mai ban mamaki da rikitarwa ya haifar da muhawara mai zafi tsakanin masu bibiyar ƙwallon ƙafa. Lamarin da ya sa wasu masana suka zayyano wasu dalilai da ke haddasa wannan koma baya ga tawagpoogin ƙasashen Afrika, waɗanda suka haɗa da:
Rashin laƙantar dabarun wasa
Masana harkokin wasanni irin su Salisu Musa Jegus na ganin cewa tawagogin ƙasashen Afirka na fama da rashin fahimtar dabarun wasa da kuma yadda salon wasa ke iya sauyawa a kowane lokaci yayin da ake cikin buga wasan.
Ya yi la'akari da cewa kowanne daƙiƙa a wasan ƙwallon ƙafa na da irin salon wasan da ya kamata ƴan wasa su buga domin tabbatar da sun samu sakamakon da ake buƙata.
Ya ce ''Mallakar wasa da kuma mallakar yadda ake gudanar da wasa a kowanne minti abu ne da yake da muhimmanci a harkokin wasanni, kuma ba ƴan wasa kaɗai suke da alhakin aiwatar da irin waɗannan ba har da masu horaswa da mataimakansu a lokacin da ake gudanar da wasan.''
Masanin ya ƙara da cewa duk lokacin da ƙwallo ke tafiya akwai salon yadda ya kamata a tafiyar da ita kuma galibi ƙasashen Afirka ba su laƙanci dabarar sauya salon wasa da kuma lokacin da ya kamata salon ya sauya ba.
Rashin ingantattun gasannin cikin gida
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Salisu Musa Jegus ya bayyana cewa akwai bambanci tsakanin yadda ake gudanar da harkar ƙwallon ƙafa a Turai da kuma yadda ake yi a Afirka, haka kuma yana yin tasiri kan yadda ake tsarawa da kuma gudanar da gasannin cikin gida, wanda kuma ke tasiri kan irin salon wasan da tawagogin ke takawa.
Kasancewa ana samun gasannin ƙungiyoyi na cikin gida masu ƙarfi galibin ƴan wasan suna wasa ne a waɗannan gasannin kuma haka yana sanyawa su saba wasa tare kuma hakan zai yi mu su sauƙi idan an tashi zuwa gasar ƙasa da ƙasa.
''Turawan nan akwai lig-lig da suke bugawa kuma da dama daga cikinsu sukan buga lig ɗin ne a tare, baya ga wasannin sharar fage na gasar cin kofin duniya akwai kuma wasannin share fage na ƙasashen Turai da ake bugawa, wanda dukkaninsu a ɗan tazara kaɗan suke bugawa, saboda haka sun saba da junansu fiye da yadda namu na nahiyar Afrika suka saba da juna,'' in ji shi.
Masannin ya kara da cewa ƴan wasan tawagogin Afirka ba su cika ɗaukar lokaci suna wasa tare ba kuma hakan na tasiri kan yadda suke iya fahimtar wasan da kuma sauye-sauyen da ya kamata a yi domin a iya ci gaba da mallakar wasanni.
Rashin wayewa kan yadda wasa ke ci gaba a duniya
A cewar salisu Musa Jegus rashin wayewa da yanayin wasa da kuma matakin da wasa ya ke.
Ya ce; ''Matakin wasa na rukuni-rukuni ya saɓa wa matakin wasa na kifa-ɗa-ƙwala, saboda haka duk lokacin da ake wasa dole ne su san cewa irin yadda ake lissafa yanayin wasa a matakin rukuni ya sha bambam da yadda ake gudanar da shi a matakai na gaba.''
Ya nanata muhimmancin sanin yadda ya kamata ƴan wasa su kasance a ankare a koda yaushe musamman idan aka ce ba wasan rukuni ba ne domin duk yadda ƴan wasa suka bar wata kafa akwai yiwuwar abokan karawarsu za su yi amfani da wannan damar su samu galaba a kansu, kamar yadda aka gani a wasannin gasar cin kofin duniya ta bana.
''Za ka ga a ƙarshen wasa ne ake yi wa ƴan Afrika illa bayan suna kan gaba, saboda rashin mayar da hankali kan abubuwan da suka shafi yanayin yadda wasa ke sauyawa da kuma sabbin dabarun da ake bijirowa da su,'' in ji shi.
Masanin ya ƙara da cewa a irin waɗannan lokuta na ƙarshen wasa ne yake da matuƙar muhimmanci a mayar da hankali kan kiyaye wasu wurare masu haɗari da ake da su a filin wasa, kamar wadanda ke kusa da da'ira ta 18, kuma akasari ƙasashen Afirka da suka yi rashin nasara a ƙarshen wasanni ba su yi la'akari da wannan mataki mai muhimmanci ba.
Rawar da ƙasashen Afirka suka taka a Gasar 2026
Za a daɗe ana tuna irin rawar da nahiyar Afrika ta taka a gasar cin kofin duniya ta 2026 sakamakon irin wasanni masu ban mamaki da ƙasashen nahiyar suka buga a gasar.
Ba a taɓa samun ƙasashen Afirka da yawa da suka wuce matakin rukuni ba kamar wannan karo - inda Moroko da Senegal da Ghana da Algeria da Masar da Afirka ta Kudu da Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da Cabo Verde da Cote d'Ivoire - duk suka kai zagaye na biyu.
Wannan ya yi nuni da irin ƙarfin da nahiyar take da shi a fagen ƙwallon ƙafa.
Gasar wadda aka faɗaɗa zuwa tawagogi 48 ta samar da ƙarin damarmaki, amma ƙasashen Afirka sun tabbatar da matsayinsu ta yadda suka ƙalubalanci ƙasashe da aka san su da daɗaɗɗen tarihi a fagen wasan a duniya.











